An Yaba wa Alhazan Jihar Zamfara

Daga Bello Hamza, Gusau

An yaba wa irin halayyar da alhazan bana ‘yan jihar Zamfara musamman wadanda su ka fito daga yankin karamar hukumar Anka da Mafara suka nuna a kasa mai tsarki a yayin gudanar da aikin hajjin bana, wannan yabo ya fito ne daga bakin Honarabul Hambali Shiitu Samaho mai ba gwamnan Jihar Zamfara shawara a fannin muradun karni (Special Adbiser on Sustainable Debelopment) a wata hira da ya yi da jaridar Leadership A Yau a garin Gusau.

Honorabul Hambali ya nuna farin cikinsa a kan yadda alhazan suka gudanar da ayyukan ibadunsu cikin natsuwa da bin doka da oda tun daga gida Nijeriya har zuwa kasa mai tsarki, har kuma gashi Allah Ya kaddara dawowarsu gida lafiya, “wannan abin alfahari ne ga daukacin jama’ar jiharmu” in ji shi.

Daga nan, sai ya jinjina wa Gwamnan jihar Alhaji AbdulAziz Yari da hukumar kula da aikin hajji ta jihar karkashi jagorancin Alhaji Abubakar Sarkin Pawa Dambo bisa jajircewarsu da aiki tukuru da suka yi wajen ganin an samu wannan nasara a aikin hajin bana, ya kuma bukace su da su kara kaimi wajen ganin an samu irin wannan nasarar ko ma fiye da haka a shekaru masu zuwa.

Daga karshe, Honarabul Hambali ya yi addu’ar Allah Ya karbi ayyuka da addu’o’i da alhazanmu suka gabatar a kasa mai tsarki, ya kuma yi addu’ar Allah ya ba mu alherinsa a cikin wanna sabuwar shekarar.

 

Exit mobile version