Zawiyyar Ahlul Faidhati Mai Diwani Group da ke Sabon Garin Tudun Wadan Kaduna ta shirya gagarumin Maulidin Manzon Allah (SAW) na ranar haihuwa bisa jagorancin Sheikh Isma’ila Umar Almaddah (Mai Diwani) inda ta shafe tsawon daren ranar Laraba 12 ga Rabi’ul Awwal na bana ana gudanarwa.
Maulidin wanda ya kunshi karatun Alukr’ani, rera kasidun yabon Annabi (SAW) da tarihinsa tun kafin daukar cikinsa (SAW) har zuwa bayan haihuwa, ya samu halartar dimbin al’ummar musulmi hard aga kasashe makota irin su Benin, Nijar da Ghana. Har ila yau, ya kunshi gabatar da takardun shahada da izini ga dalibai biyu da suka haddace Alkur’ani mai girma a bara suka kuma yi karantarwa ta tsawon shekara daya, Fatima Isma’ila da Khadija Isma’ila da kuma wani malami almajirin Sheikh Isma’ila, Malam Umar Futi.
- Hisbah Ta Yi Wa Mutum 4,000 Rajista Da Ke Son Gwamnatin Kano Ta Aurar Da Su
- Al’adun Kasar Sin Na Da Tushen Neman Zaman Lafiya Tun Lokacin Da
Da yake jawabi game da falalar maulidin, Sheikh Isma’ila Umar Almaddah, ya bayyana cewa akwai muhimman abubuwa da suka sa suke shirya maulidi duk shekara.
“Sakon da muke tafe da shi a wannan dare na ranar haihuwar fiyayyen halitta ga Musulmai da Al’ummar duniya baki daya shi ne, muna yin murna ga samun Annabi Muhammadu SAW, sabida abubuwa da yawa amma ga wasu gudu Uku ‘yan kadan daga ciki:
“Na Farko, Sabida kasancewarsa rahama ga halitta baki daya, Ubangiji ya fada a cikin Alkur’ani, “Ba mu aiko ka ba sai kai rahama ne ga halitta – Mutum da Aljani.” Ba rahama ne ga Musulmai ko Muminai ko Muhsinai kadai ba, a’a, rahama ne ga duk halitta (duk wani abu wanda ba Allah ba). Wannan haka Sahabbai da Malaman al’umma suka tafi a kai, cewa, Manzon Allah (SAW) rahama ne ga Kafiri wadanda ke yakarsa, don ba a halaka su ba kamar yadda aka halaka Kafiran sauran Annabawa. Ashe duk wanda ya zama sababin tsira a gare ka, ba zaka taba mantawa da shi ba.
“Kasancewar Manzon Allah SAW rahama ne ga halitta, wannan ya cancanci a yi murna da shi a kowanne lokaci balle ranar da aka haife shi (SAW). Idan muka koma cikin Alkur’ani sai mu ga wannan abu a sarari, Fatihar da muke karantawa a cikin Salloli biyar – biyu da Asuba, hudu da Azahar da La’asar da Isha’i sai Uku da Magriba, duka sun fara ne da “Alhamdu lillahi rabbil alamin” kana ji ka san wannan sako ne Ubangiji yake son isarwa ga bayinsa. Don haka, kowa yana da hanyar da zai bi ya yi murna da haihuwar Annabi (SAW), kuma babu wanda zai hana wani bin irin hanyar da yaza ba na murna da haihuwar Annabi.
“Na Biyu, Allah ya aiko Annabi (SAW) zuwa ga duk halitta baki daya – Afirka, Larabawa, Sinawa, Turawa,… an aike shi ya isar musu da sako, wani ya dauka ya kai zuwa wani yanki daga nan wani ya dauka ya kai wani yanki har ya karade duniya baki daya. Don haka, Larabawa ba su da iko su takaice sakon Annabi (SAW) a iya su kadai kawai. Don haka, za ka ga wani karatu wanda kai ba ka fahimta ba amma wani ya fahimta a Alkur’ani ko a Hadisi. Ko wane Annabi kauyensu aka aika shi cikin kabilarsa amma Annabi Muhammad (SAW) ga duk duniya baki daya. Sabida haka ne, Masoya kuma Malamai suka tafi cewa, Annabi (SAW) ya iya kowane yare. Da za ka yi Mafarki da shi, cikin yarenka za ka zanta da shi, sabida Allah ba ya aiko Annabi sai cikin yarensa, shi kuma Annabi (SAW) duk duniya ne aikensa, sai dai ya tsaya cikin Larabci amma ya umurci wasu daga cikin Sahabbansa, Zaidu bin Sabit yana ciki da su karanci Turanci (Yaren Rum) don su yi musu wa’azi. Don haka, ya dace, Musulmi su mai da hankalinsu, su fahimci cewa, Annabi (SAW) na duk ‘yan Adam ne. Don haka, duk wata jama’a da ta ke son takaita sakon Annabi SAW a iya daidai fahimtarta ko al’adarta, ta tauye abu mai fadi.
“Na Uku, Annabi (SAW) shi ne cikamakon Annabta da Manzanci, Annabtar da ta taso tun daga kan Annabi Adam (AS), da kuma Manzancin da ya taso tun daga kan Annabi Nuhu (AS). Kowanne Annabi (AS) yana zuwa ne da ci gaban rayuwa, in muka duba dan Adam a zamanin Annabi Adam, Dan’adam da dabba duk rayuwa iri daya suke yi sai dai shi Dan’adam a tsaye yake, yana tafiya da kafa biyu, daga kan Annabi Adam, Allah ya sanya wa Dan’adam hankalin da zai iya magana, zai iya banbance abubuwa kala-kala har ya mayar da muryarsa zai iya yin Yare da wannan hankalin da Allah ya sanya masa, daga nan dan Adam ya tashi daga suna ‘Basharu’ ya koma ‘Insanu’ daga nan ya zama Khalifan Allah. Annabi Nuhu ne ya fara zuwa da bin Salsalar iyaye.
“Haka, za ka ga kowanne Annabi, in ka duba karatunsa a cikin Alkur’ani za ka ga ya zo da wani ci gaban Dan’adam, kamar Annabi Salihu, mutanensa sun zo da kwarewar gini a tudu da kwari. A zamanin Annabi Shu’aibu, shi kuma har an iya noma da Awo har aka zo kan Annabi Ibrahim, shi kuma ya gyara Ibada, aka daina yanka Dan’adam da sunan Bauta aka fara yanka dabba. A zamanin Annabi Musa kuma aka daina auren ‘yar uwa – yaya da kannuwarta a lokaci guda, in ka duba tarihin Annabi Yakub sai ka ga ya auri yaya da kannuwa duk a lokaci guda.
“Daga kan Annabi Musa Annabta da Ilimi suka bunkasa, sai dai Mutanen suna da tsaurin kai, in Ubangiji ya hana su abu ba sa kamewa, sai ya fara kafa musu diyya kuma aka haramta musu abubuwa masu yawa, da Allah ya aiko Annabi Isa, shi kuma sai ya zo don saukaka wasu daga cikin abubuwan da Allah ya haramta musu. Annabi Isa ya bayyana a wata nasiharsa mai ban mamaki, inda yake cewa, an ce muku kaza ni kuma na canza zuwa kaza, sai wani ya tashi ya ce, wato kana so ka canza Shari’ar Annabi Musa ko? Sai ya ce masa, tun farko ba haka take ba, tsaurin Idonku ya sa aka maida ita haka amma Shari’ar Annabi Musa mai sauki ce, Annabi Muhammadu (SAW) yana nan zuwa, shi kuma zai sauke duk wannan nauyin da aka kakaba muku.
“Don haka, da Annabi Muhammad (SAW) ya zo, ya saukake komai. Allah ya cika Annbata. Manzanci kuwa, shi ne aike – Allah ne ya ce ungo wannan isar musu. Don haka, da isarwar da Ilimin, Manzon Allah (SAW) ya cika su, sai dai bayansa, Ilimi zai ta bunkasa har za a zo ranar da Dan’adam zai ga ya isa komai.
“Allah ya ba wa Annabi (SAW) gagararriyar Mu’ujiza, ita ce Alkur’ani, rayayye ne da yake tafiya da kowane zamani, yadda aka fassara shi a zamanin Annabi (SAW) daban da yadda za a fassara shi a wannan zamani. Zahirin Alkur’ani, Shari’a ne – Alfurkan; cikin Alkur’ani, Ilimi ne mai yawa – Alkur’anu (ya yi maganar abun da ke cikin Lauhul mahfuzi da kuma bayan abun ya faru), don haka, a cikin Alkur’ani, babu zancen “Halal ko Haram” sai dai ka ce “Gaskiya ne ko Karya ne”, Misali, yau mun zauna muna murnar zagayowar ranar haihuwar Annabi (SAW), a nan babu zancen “Haram ko Halal” don ba shari’a ba ce, sai dai ka ce “Gaskiya ne ko Karya ne” a kan tarihin da muka fada. A tarihi babu “Halal ko Haram” sai dai “Gaskiya ne ko Karya ne”.
“Kur’ani ya yi bayanin Hikima – kyawawan dabi’u, idan Kur’ani abu 100 ne, 80 kyawawan dabi’u ne, don haka, ba komai ba ne musulunci sai kyawawan dabi’u. sabida haka, Karanta tarihin Annabi babu abin da yake koyawa sai kyawawan dabi’u. Duk yawan ibada, in babu kyawawan dabi’u, shiru ce. Ashe Dan’adam ba komai ba ne sai kyawawan dabi’u, kuma wannan shi ne maksudin zuwan Annabi (SAW) da fadinsa “An turo ni don in cika kyawawan dabi’u”.
Akwai Zikru – Alkur’ani, Allah ya ce, shi ya saukar da shi kuma shi zai kare shi, tun ana da kira’a bakwai yanzu ana da kira’a 10 har yanzun an kai 20, duka Mu’ujiza ce ta Annabi Muhammad (SAW).
(Wannan duk yana nuna mana, mu zama al’umma mai ci gaba, wayayya. Manzon Allah (SAW) ya lura Makkah kauye ce, garin wasu mutane ce da ba za su taba amsar wata rayuwa ba sai tasu, amma Malamai sun ce, Makkah kadai aka amince wa ta zama haka don ta rike Dakin Allah, amma duk garin da ya ce zai yi haka, ba zai ci gaba ba. Don haka Annabi (SAW) ya bar ta ya tafi Yasriba daga baya ya sauya mata suna zuwa Madina kuma ya fara kafa kundun tsarin Mulki na farko a duniya, duk wanda yake Madina dan kasa ne, duk abin da ya shafi Madina ya shafe shi.” Ya bayyana
Sheikh Isma’ila Mai Diwani ya yi kira ga Musulmi da su gyara dabi’unsu inda ya ce, wannan shi ne babban Muradin wannan zamani, ya kuma sake kira ga gwamnati da ta raya kasa da ‘yan kasa ba ta rusa su ba, su kuma su amsa kiran gwamnati ga abin da zai raya kasar.
Zawiyyar za ta kuma gudanar da irin wannan maulidi a daren Laraba mai zuwa a matsayin Maulidin Suna na Annabi (SAW).