Nijeriya kasa ce mai Harsuna da suka zarce 250 kafin ta kasance kasa daya shi sashen Arewaci da Kudancinta na zaman kan shi har sai lokacin da Turawan Mulkin mallaka suka hade sassan biyu a shekarar 1914, tun daga wancan lokacin ne take zaman dunkulalliyar kasa shekara fiye da shekara 100 ke nan.
Daga shekarar 1960 lokacin da aka samu mulkin kai har zuwa shekarar 1967 bayan shekara 53 da kasancewa tare, babu wani abin da ya yi kama da jiha, Jihohin da ake da su ba an kirkiro su ba ne a rana daya ba, an fara ne da sassa uku da suka hada da sashen Arewa, sashen Yamma, da kuma sashen Gabas, daga baya ne aka samu kirkiro da sabon sashen Yammaci da ake kira da suna Mid Western States.
- Xi Ya Karfafawa ‘Ya‘yan Wadanda Suka Sadaukar Da Rayuwarsu Da Su Zama Amintattu Masu Kare JKS Da Al’umma
- Yadda Alakar Sin Da Afirka Ke Kara Bunkasa Kasashen Nahiyar Afirka
A shekarar 1967 lokacin da Shugaban kasa na mulkin soja Ritaya Janar Yakubu Gowon ya kirkiro da jihohi 12 da suka hada da Jihar Arewa maso yamma, Kaduna, Kano, jihar Arewa maso gabas, Kwara, Jihar Benuwe da Filato, Jihar Yamma, Jihar Gabas ta tsakiya, Kuros Riba, Legas, da Ribas. Ranar 3 ga Fabrairu 1976 Janar Murtala Ramat Muhammed ya kirkiro sabbin jihohi 7 da suka hada da Bauchi, Benuwe, Borno, Imo, Neja, Ogun,da Ondo. Haka ya sa suka kai 19 ,bayan shekara 40.
Shekara goma sha daya a shekarar 1987 jihohi suka koma 21 bayan da Janar Babangida Shugaban kasa na mulkin soja a lokacin ya kirkiro da Jihohi biyu Akwa Ibom da Katsina, bugu da kari a ranar 27 ga Agusta shekarar 1991 Babangida ya sake kirkiro Jihohi 9 da suka hada da Abia, Inugu, Delta, Jigawa, Kebbi, Osun, Taraba da Yobe inda hakan yasa suka kai 30.
Janar Sani Abacha ya kirkiro karin sabbin jihohi shida ranar 1 ga Oktoba 1996 da suka hada da Ebonyi, Bayelsa, Nasarawa, Zamfara, da Ekiti shi ya sa take da Jihohi 36.