Yadda Aka Tsinci Jaririya Sabuwar Haihuwa A Kebbi

Daga Umar Faruk, Birnin-kebbi

Rahotanin da ke fitowa daga ƙaramar hukumar mulki ta Yawuri a yammacin jiya sun bayyana cewa, an tsinci wata jaririya sabuwar haihuwa a garin Yawuri  a Jihar Kebbi.

Jaririyar dai an same ta ne yashe a unguwar bayan ofishin NEPA a garin Yawuri

Domin jin ta bakin ƙaramar hukumar mulki ta Yawuri , LEADERSHIP A YAU ta samu zantawa da  jami’in da ke kula da irin wannan matsala  a ƙaramar hukumar Yawuri, wato Alhaji Aminu Musa Yawuri ta waya inda  ya bayyana cewa, “Da misalin ƙarfe  biyu na yammacin jiya aka bugo mini waya  cewa ga  wata jaririya sabuwar haihuwa an yarda ita  a bayan gidan marigayi tsohon gwamnan soja a Jihar Ekiti, Kanar  Inuwa Bawa (mai ritaya) a gidansa da ke bayan ofishin NEPA a cikin garin Yawuri”.

“Da ma idan  aka samu irin wannan matsalar  yakan kai rahoto ga  ‘yan sanda domin da jami’an ƙaramar hukumar da kuma jami’an ‘yan sanda muke  zuwa domin mu ɗauko yaran da aka jefar da su a ko’ina  a faɗin ƙaramar hukumar, wanda hakan muka yi ga  wannan ita jaririyar da aka tsinta a yanzu”, in ji jami’in.

Kazalika, ya ci gaba da cewa sun je  unguwar NEPA ofis  domin  tabbatar da gaskiyar wannan lamari, inda suka samu tabbacin aukuwar hakan. Daga nan ya ce, “Mun ɗauko jaririyar kuma a halin  yanzu tana ƙarƙashin kulawata  a matsayina na jami’in kula da irin wannan matsaloli idan suka samu a  yankin ƙaramar hukumar Yawuri”.

Haka nan ya ce,  “Kawo yanzu babu matar da ta ɗauki  alhakin yada  jaririyar, amma ƙaramar hukumar Yawuri ta kafa kwamitin bincike domin gano duk wani da ke da hannu a sha’anin jefar da wannan jaririya, haka kuma  ‘yan sanda garin Yawuri su ma  suna kan binciken”.

A ƙarshe ya ce, “Ƙaramar hukumar Yawuri za ta  kai jaririyar  gidan marayu  mallakar gwamnatin Jihar Kebbi da ke Birnin-Kebbi domin ci gaba da kula da ita”.

 

Exit mobile version