Yadda Aka Yi Taron Tunawa Da Sam Nda-Isiah Karo Na Farko

Ta’aziyar Rasuwar Sam Nda Isaiah

 

Daga Bello Hamza, Abuja

 

A ranar Talata 14 ga Disamba 2021 ne aka gudanar da taron tunawa da cika shekara daya da mutuwar Sam Nda-Isaiah, shugaban rukunin kamfanin LEADERSHIP Group Ltd wanda ya rasu ranar 12 ga watan Disamba 2020. An da gudanar da taron ne a dakin taro na ‘Interational Coference Center Abuja’,  taron ya samu halartar dinbin al’umma daga bangarorin rayuwa daban-daban, abokansa aikinsa a harkar jarida ‘yansiyasa da kuma ‘yan uwa da abokan arziki. Sakataren Gwamnatin Tarayya, Mista Boss Mutapha ya jagoranci taron shi ne kuma ya jagoranci tawagar gwmanatin tarayya wadanda suka hada da Ministan Yada Labarai da Al’adu, Mista Lai Mohammed, Ministan Albarkatun Ruwa Injiniya….. da Ministan Matasa da wasanni, Sunday Dare da kuma Uwar Gidan Shugaban Kasa, Aisha Buhari.

An dai kasa taron ne kashi uku, da farko an gabatar da addu’o’i na musamman da wake-wake kamar yadda addinin Kirista ya koyar a karkashin jagorancin Bishop Edwin Musa Jarumai. Bangare na biyu na taron kuma ya kunshi tattaunawa a kan al’umurran da suka shafi siyasar Nijeriya, a jawabinsa, Ministan Yada Labarai da Al’adu, Alhaji Lai Mohammed ya nemi masu gidajen jarida a kasar nan su yi koyi da halayen kishin kasa na Marigayi Sam Nda-Isiah don shi bai taba cire rai da cewa Nijeriya za ta gawurta tare da zama kasar da kowa zai yi alfahari da ita ba.

“Ina son sauran jaridu su yi koyi da yadda jaridar LEADERSHIP ke guanar da harkokinta, musamman abin da ya shafi sanya bukatar kasa a gaba fiye da komai, don da wuya ka ga wasu labarai masu tayar da hankali da za su iya wargaza kasa a cikn jaridar,” inji shi.

Ya ce, babbar burin Marigayi Nda-Isaiah shi ne samar da hadadiyar kasa mai cike da zaman lafiya.

“Shi dan kishin kasa ne wanda yake burinsa a dukkan lokutta shi ne na ya taimaka wa harkokin tabbatar da kasar nan dunkullaiyar, fatansa shi ne samar da Nijetiya mai cikakken zaman lafiya. Marigayin zai yi murnar ganin abokansa na tunawa dashi a daidai irin wanana lokacin”.

Ministan Al’adun ya kuma ce, Sam ya yi amfani da jaridarsa wajen gabatar da suka mai ma’ana ga gwamnatin Nijeriya ya kuma ba gwamnatin dukkan goyon bayan da ta ke bukata na samun nasarar tafiyar da mulki.

A nata jawabin, Uwar Gidan Shugaban Kasa, Aisha Buhari, ta bayyana cewa, za a cigaba da tunawa da Marigayi Sam Nda-Isaiah a Nijeriya saboda harkokin da ya gudanar da kishin kasa da jinkan al’umma, musamma a kan yadda ya jagoranci taimakawa al’umma da dama daga dukkan bangarorin kasarnan.

Ta ce, za a cigaba da tunawa da Nda-Isaiah ta fannoni da dama, wasu na tuna shi a matsayin mai fashin baki a akan harkokin siyasa, dan siyasa, mai ilimin hada magunguna, dan jarida kuma wanda ya kirkiro rukunin jaridar nan ta LEADERSHIP, ga iyalansa kuma za su cigaba da tuna da shi a matsayin miji na gari, uba na gari, dan uwa na gari, mutane da yawa na kiransa Shugaba saboda tasirin da ya yi a rayuwarsu.

“Mun taru a nan ne yau don tunawa da Sam kamar yadda muke tunawa da shi a kullum za kuma mu cigaba da tunawa da shi har karshen rayuwar mu.

A shekarun da ya yi a duniyar na, Sam ya shiga harkoki da dama wanda kuma dukkan su harkoki ne da shuka shafi bukasa kasa, tabbas shi ne wanda za a iya cewa cikakken dan kasa mai neman cigaban ta,” in ji ta.

Ta kuma kara da cewa, samun imutum irin Sam a Nijeriya abu ne mai matukar wahala, wannan jajircewar ce ta sanya ya samu nasarorin da ya samu a harkokin da ya fuskanta a rayuwarsa.

“Tabbas Zainab, kin kasance gwarzuwa tun rasuwar Sam, muna kuma horan da ki kasance yadda kike, iyalanki da harkokin kasuwancinsa da mu gaba daya na matukar bukatar ki a wannan lokacin.

“Muna matukar alhinin rabuwa da kai Sam, amma irin rayuwar da ka gudanar sune suke karfafa mu a halin yanzu, muna kuma yin addu’ar Allah ya cigaba da gafarta maka.

Sakataren Gwamnatin Tarayyar, Boss Mustapha

A nasa jawabin Sakataren Gwamnatin Tarayyar, Mista Boss Mustapha, wanda kuma shi ne ya jagoranci taron, yace, Sam Nda-Isaiah bai yi mutuwar banza ba don ya taba rayuwar al’umma masu yawa a fadin tarayyar kasarnan wadanda suna gudanar da ingantacciyar rayuwar saboda gudumawarsa.

Sakataren gwamnatin ya kuma ce, mutuwar Nda-Isaiah babbar rashi ne ba kawai ga iyalai da makusantasa kawai ba, babbar rashi ne ga al’ummar Nijeriya gaba daya, musamman ganin ya gudanar da rayuwa mai cike da kishin kasa.

“Rayuwar Sam cike take da sakonni masu yawa, sun kuma hada da bukatar aiki tukuru, son juna tare da soyayya ga Nijeriya, rauwarsa ya zama darasi abin koyi ga matasa masu tasowa a kan yadda yakamata su fuskanci rayuwa’’ in ji Boss Mustapha.

Boss Mustapha ya kuma ce, mutuwar Sam ba wai rashi ne kawai ga kamfann LEADERSHIP ba amma rashi ne ga daukacin harkar jarida a Nijeriya gaba daya, ya kuma ce, babbar kalubalen dake gaba makusantan Sam a wannan lokacin shi ne na su cigaba da ayyukan da ya fara na bunkasa rayuwar al’umma ba tare da nuna banbanci ba, ya kuma nuna jindadinsa akan yadda aka shirya wannan taron, musamman yadda ya ga abokai da makusantan Sam sun samu halarta, ya ce, tabbass wannan an kawo hanyar samar da wani abu da zai kasance wani damdamali na tumawa da Sam har abada.

Wadanda suka gabatar da jawabi a wajen taron su kuma hada da Shugaban Hukumar AMCON, Ahmed Kuru, inda ya yi magana a kan yadda marigayin ya rike amanar zumunci a tsakanin dukkan abokansa, ya ce, Sam mutum ne da baya nuna banbanci a stakanin Musulmi ko Kirsita, yana rike alkawarin dake a tsakanin abokai. Ya kuma tabbatar da haka a tsawon shekarun da ya yi a duniya, ya kan tsayu don ganin ya taimaka wa abokan huldarsa ko da kuwa sun cuce shi a baya. Ya kuma kara da cewa, da wannan kishin ne Sam ya shiga siyasa, yana mai fatan samun damar bauta wa kasa tare da kawo canjin da ya kamata a rayuwar al’ummar kasar nan.

Ita kuwa Halima Remawa-Fufore, wadda suruka ce ga iyalan Nda-Isiah ta bayyana yadda marigayin ya taimaka mata tare da wasu mutane da dama ta hannun ta, ta kuma ce, irin wanna taimakon da Sam yake yi sune sirrin nasarorin da ya samu a rayuwa.

‘’Kofarsa a bude take ga kowa da kowa don bayar da shawara da taimako, ya kuma tsayu wajen kare iyalansa, tabbas ya yi rayuwa kamar yadda taken jaridarsa take na “Don Allah Da Kishin Kasa “.

Haka kuma Kingsley Chukwu, Dakta Tunde Owoyele, dukkan su sun bayyana irin jarumtar Sam a fagen taimakon al’umma da sauransu.

A nasa bangaren, Babban Editan jaridar Thisday kuma shugaban gidan talabijin na Arise News Channel, Nduka Obaigbena, ya yi amfani da damar da ya samu na jawabi a wurin taron tunawa da rasuwar Sam, inda ya yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya sanya hannun a kan daftarin dokar zabe na 2021 don ta fara aiki, musamman ganin zaben 2023 na tafe.

Prince Obaigbena ya kuma tuna da yadda marigayin ya kaddamar da takararsa na neman shugabancin kasar nan a shekarar 2014 da shirin na nasa na ‘The Big Ideas’ wannan shiri ne da yake kunshe da tsare tsare da aka shirya za su ceto kasar nan daga dukkan matsaloli.

“Muna bukatar tsari zaben da zai tabbatar da dukkan kuri’ar da aka kada sun yin tasiri. Saboda haka ina kira ga Ministan Al’adu Alhaji Lai Mohammed, ya taimaka waje kira ga shugaban kasa don ya gaggauta sanya hannun a kan daftarin dokar don amfanin al’ummar kasar nan na yanzu da masu zuwa a na gaba.”

Ya kuma bayar da shawarar gwamnati ta fara karbar haraji ga al’umma kasar nan don tallafa wa jami’an tsaronmu don fuskanta matsalar tsaron da ke fuskanta a kasar nan.

Daga nan ya kuma yi ta’aziyyar wasu manyan yan Nijeriya da suka mutu a ‘yan tsakanin nan sun kuma hada da Samaila Isah Funtua, Wada Maida da tsohon shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Abba Kyari.

A nata jawabin, shugabar kamfanin LEADERSHIP Group Ltd, Zainab Nda-Isaiah, kuma matar marigayin Nda-Isaiah ta bayyana cewa, Sam mutum ne wanda ya san mutumcin iyalansa, ya kuma tarbiyartan da iyalansa a kan yadda suma za su fuskanci rayuwa ba tare da tasro ba.

“A ranar da ya rasu, na yi tunanin al’amurran rayuwar mu za su taya gaba daya amma lallai Allah ya tausaya mani tarr da iyalai na. A ranar da muka hadu da miji na ya gabatar da kansa, ya na mai cewa, suna na Sam, sai kawai ya kuma kara da cewa, ‘ina son auren ki.’ Shike nan sai muka zama miji da mata.

“Mutum ne mai magana daya, bai yarda da munafunci ba, bai yarda da bata lokaci ba, ya kan ce, lokaci mafi kyau na yin wani abu shi ne jiya ba yau ba.

“Ya fuskanci kalubalen rayuwa, kuma yana bukatar muma iyalansa mu bi sahunsa akan haka, koda ya samu koma-baya baya karaya, ya kan sake tasowa ya fuskanci abin dake gabansa.

“Mun yi rayuwar aure mai cike da soyayya, bana kiran sunan sa sai dai in kira shi da ‘Sweetie’ wanna ma yasa ‘yar autanmu bata ma san sunansa ba, don wata rana mun dawo coci sai wani ya tambaye ta sunan mahaifinta sai tace musa, ‘Sweetie’.

Ta kuma cigaba da bayyana cewa, “Ina mika godiya ga Allah a kan taimakonsa. A rayuwarsa, miji ne mai tsananin tausayi da nuna soyayya haka a mutuwarsa ya tanadar mana dukkan abin da zamu bukata don kada mu sha wahala.”

Daga karshe ta mika godiya ga dukkan wadanda suka samu halarar taron ta kuma yi addu’ar Allah ya saka musu da alhairi.

Wasu fittatun mata da suka yi jawabi a wurin taron sun hada da Elder Martina Kobe, Mary Owoyele, Lydia Ageni, da kuma Elizabeth Dul.

A nasa jawabin, Bishop Edwin Musa Jarumai, na cocin Diocese of the Praise Church, Abuja, ya bayyana cewa, Nda-Isaiah nada kyakyawar alaka da ubangijinsa kafin ya koma zuwa ga Allah. Ya kara da cewa, Sam ya gudanar da rayuwa gamsasshiya tsakaninsa da Allah ya kuma karfafi iyalansa dasu zama mutanen kirki masu bautar Allah.

“’Yanuwa maza da mata, ku sani cewa, akwai rayuwa bayan mutuwa, kuma Allah zai yi mana hisabi a ranar sakamako, saboda haka yakamata mu gudanar da rayuwa ta yadda Allah za yi alfahari da mu in mun riskesa.” In ji shi.

 

Exit mobile version