Assalamu alaikum masu karatu, barkanmu da sake haduwa da ku a wannan makon a cikin shirin na mu mai farin jini da albarka na Girki Adon Mata.
A yau shafin na mu zai koya muku yadda ake Alalle
- 2027: ‘Yan Siyasa Sun Yi Watsi Da Gargadin INEC, Sun Ci Gaba Da Yakin Neman Zabe
- Zaben Cike Gurbi: Tinubu Ya Lalata Tsarin Zaben Nijeriya — ADC
Abubuwan da ake bukata:
Wake, Tattasai, Attarugu, Albasa, Kwai, Karafish, Manja, Kori da Tayim, Magi
Da farko za ki wanke kwanki ki saka a tukunya, sai ki dora shi a kan wuta ya tafaso, bayan kin saka sai ki kawo waken ki sai ki zuba shi ki wanke ki cire bayansa.
Sai ki kawo kayan Attarugu da Tattasai da Albasa su ma ki wanke su ki gyara ki hada guri daya, sai ki kai markade amma idan kina da blender za ki iya yi a gida. Bayan nan za ki kawo manjanki da karafish, tayim da kori ki da magi ki zuba su cikin markaden sai ki motsa har sai ko ina ya samu.
Sai ki kawo kwanki da ya nuna ki bare shi sannan ki yanka shi dai dai yadda ya yi miki.
Sannan ki fara zubawa a leda za ki zuba markadadden waken da kika hada ciki sai ki dauki yankakken kwan ki saka a ciki, haka za ki yi ta yi har ki gama.
Bayan kin gama sai ki jera shi cikin tukuya ki saka masa ruwa yadda zai sha kanta sai ki rufe ki dora a wuta ki barshi har sai ya nuna, ya yi kamar awa daya haka, duk inda ya yi awa daya indai wuta tanaci to ya nuna. Ana iya cin da Jajjageggiyar miya ko kuma soyayyen manja da yaji. A ci lafiya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp