Assalamu alaikum masu karatu, barkanmu da sake haduwa daku a wannan makon a cikin shirin na mu mai farin jini da albarka na Girki Adon Mata
A yau shafin na mu zai koya mana yadda ake Chicken Teriyaki Rice:
Chicken Teriyaki Rice abin ci ne na zamani da ya shahara a kasashen Asiya. Ana hada shinkafa da kaza tare da miya mai dandanon teriyaki, wanda ke sa abin cin kamshi da dandano na musamman.
Abubuwan da ake bukata:
Shinkafa, Naman kaza, Albasa, Tafarnuwa, Karas,
Koren tattasai, Koren wake, Mai, Gishiri, Black pepper, Danyar citta,
Teriyaki sauce, Dan zuma, Dan ruwan lemun tsami.
Yadda ake hadawa:
Da farko, a wanke shinkafa sannan a dafa ta da dan gishiri har ta yi laushi, a tace ta a ajiye.
Sai a yanka naman kaza kanana, a zuba masa gishiri da black pepper. A dora kwanon suya a wuta, a zuba dan mai sannan a soya kazar har ta soyu kuma ta yi dan ruwan kasa.
Bayan haka, a kara yankakken albasa, tafarnuwa da danyar citta a soya su na ‘yan mintuna. Sai a zuba karas da koren tattasai, a motsa su a hankali.
Daga nan sai a zuba teriyaki sauce da dan zuma da ruwan lemun tsami. A bar su su dahu na ‘yan mintuna har miya ta yi dan kauri.
A karshe, a zuba shinkafar da aka dafa tare da kazar teriyaki. A kawata da yankakken albasa.
Ana iya kara kayan lambu daban-daban kamar broccoli ko koren wake domin kara wa abin cin armashi da kayatarwa. Aci dadi lafiya.














