ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, December 21, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yadda Ake Cin Gajiyar ‘Google Drive’ Wajen Amfani Da Kwanfuta

by Ibrahim Sabo
3 years ago
Google

Menene Google Drive?

Google Drive wata ma’ajiya ce da kamfanin google suka tanadarwa duk wanda ya mallaki account din ‘Gmail’ kuma kyauta ne. G-dribe ya kan ba da damar ajiya na kimanin wurin ajiya (storage space) 15GB kuma ya tsare maka shi, wato ya ba da tsaro (security) ingantacce. Ya kan iya adana bayanai iri-iri, kama daga rubutu (document), murya (audio), hotuna (pictures) da kuma bidiyo (bideo).

Yaya Google Drive Yake?

ADVERTISEMENT

Mafi yawancin wayar hannu kirar (smartphones) tana zuwa da shi kuma kyauta yake a cikinta. Idan aka duba wayar da kyau cikin natsuwa za a ga application din me suna dribe kamar yadda yake a hoto.

Idan ba a samu ba, sai a sauke shi, wato a yi download daga google playstore, zai sauke shi cikin a wayarka. Sai a bude shi, za a ga wadannan abubuwa;

LABARAI MASU NASABA

Auren Da Ya Fi Auren Gidan Daula Dadi Ga Mace

Tinubu Ya Nuna Kwarewa Da Gogewa A Sha’anin Mulkin Nijeriya – Bishir Dauda

Sune kamar haka:

1) Folder

2) Upload

3) Scan

4) Google Docs

4) Google Sheets

5) Google Slides

 

Yaya Ake Ajiya A Google Dribe?

Yadda ake ajiya a google dribe shi ne, da farko za ka bude upload, nan take zai bude maka local storage, wato abubuwan dake cikin wayarka (memory). Da zarar ya bude, sai a zabi abin da ake so a ajiye din. Shafi wanda yake dauke da abubuwan da aka ajiye a cikinsa zai bayyana.

Shikenan an yi ajiya a cikin google drive din, duk lokacin da ake bukata sai a yi amfani da shi. Wani lokacin idan an ajiya (upload) sai ya nuna waiting for WiFi. To hakan yana faruwa ne musamman idan wannan ne lokaci na farko da mutum ya fara amfani da google dribe din.

A wasu lokutan kuma idan ana da matsalar network (data) ana fuskantar hakan. Idan aka yi upload, sai a ga yana nuna waiting for WiFi, to ga yadda za a yi masa.

A saman wayarka akwai wasu layuka guda 3 a kwance daga gefen hagu (option) kusa da Search in Drive, za a ga wani feji zai bude sai a danna Settings. Zai kara bude wa, to daga can kasa an rubuta ‘Data Usage’ a gefen rubutun akwai wani digo shudi (blue) sai a danna.

Shikenan wannan matsalar an yi maganinta.

Akwai abubuwa masu yawa wadanda google dribe kan iya taimaka wa wajen yin amfani dasu. Google Drive yana ba da damar ajiyar kowane irin file kamar yadda na muka ambata a baya. Za a iya adana file komai girmansa idan bai wuce nauyin 15GB ba. Kadan daga cikin mahimman amfaninsa shi ne:

1) Upload: Yadda za a dora abu a kan google dribe, kamar yadda na kawo misali a baya.

2) Scan: Google drive ya kan ba da damar yin scanning na takardu masu mahimmanci, kamar na karatu kuma a adana shi a cikin dribe, kuma ya kan ba da damar yin amfani da su a duk lokacin da ake da bukatarsu. Kamar a wajen rijista ta yanar gizo, lokuta da dama a kan bukaci takardun kammala karatu ta hanyar tura wa a website na neman aiki ko scholarship da sauransu. Scan yana taimaka wa sosai wajen kiyayewa hadarin gobara, ruwa da abubuwa makamantansu da kan iya kawo lalacewar takardu ko batansu. Idan kana da google dribe babu kai ba yawo da takardu a hannu.

3) Folder: Folder tana taimaka wa wajen rarrabe files da aka adana.

4) Ana iya kara girman memory storage space daga 15GB zuwa 100GB, 150GB, 200GB zuwa sama da hakan amma wannan siya ake yi, wato (Drive Upgrade).

Za mu yi bayaninsa a nan gaba.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Auren Da Ya Fi Auren Gidan Daula Dadi Ga Mace
Rahotonni

Auren Da Ya Fi Auren Gidan Daula Dadi Ga Mace

December 20, 2025
Tinubu Ya Nuna Kwarewa Da Gogewa A Sha’anin Mulkin Nijeriya – Bishir Dauda
Rahotonni

Tinubu Ya Nuna Kwarewa Da Gogewa A Sha’anin Mulkin Nijeriya – Bishir Dauda

December 19, 2025
Tunawa Da Sam Nda-Isaiah Bayan Shekara Biyar
Rahotonni

Tunawa Da Sam Nda-Isaiah Bayan Shekara Biyar

December 19, 2025
Next Post
Da Dumi-Dumi: Buhari Ya Tsige Shugaban NIRSAL, Aliyu Abdulhameed Kan Zargin Almundahanar Kudade

Da Dumi-Dumi: Buhari Ya Tsige Shugaban NIRSAL, Aliyu Abdulhameed Kan Zargin Almundahanar Kudade

LABARAI MASU NASABA

Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

December 21, 2025
Yadda Itacen Dorawa Ke Warkar Da Cututtuka Daban-daban

Yadda Itacen Dorawa Ke Warkar Da Cututtuka Daban-daban

December 21, 2025
‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta

An Cafke Wani Mutum Da Ya Lakada Wa Dansa Duka Har Lahira A Edo

December 21, 2025
Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

December 21, 2025
Kotu Ta Fara Sauraren Korafe-korafen Dalibai A Kan Jami’ar MAAUN

Kotu Ta Fara Sauraren Korafe-korafen Dalibai A Kan Jami’ar MAAUN

December 21, 2025
Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi

Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi

December 20, 2025
Wajibi Ne Tawagar MONUSCO Ta Wanzar Da Cin Gashin Kai In Ji Wakilin Kasar Sin

Wajibi Ne Tawagar MONUSCO Ta Wanzar Da Cin Gashin Kai In Ji Wakilin Kasar Sin

December 20, 2025
Matasa Miliyan 80 Ne Ba Su Da Aikin Yi A Nijeriya

Matasa Miliyan 80 Ne Ba Su Da Aikin Yi A Nijeriya

December 20, 2025
An Nuna Jigo Da Tambarin Shagalin Murnar Bikin Bazara Na Shekarar 2026 A Moscow

An Nuna Jigo Da Tambarin Shagalin Murnar Bikin Bazara Na Shekarar 2026 A Moscow

December 20, 2025
Auren Da Ya Fi Auren Gidan Daula Dadi Ga Mace

Auren Da Ya Fi Auren Gidan Daula Dadi Ga Mace

December 20, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.