Mai taimakawa shugaban Hukumar NAHCON a kafafen yada labarai, Ahmad Muazu, ya ce akwai wani lokaci da yin shiru ba ya amfanar da al’umma wanda hakan yana faruwa ne idan aka riƙa maimaita ƙarya har ta ga ana buƙatar neman gaskiyar lamari.
Kowace ma’aikata na da nata ƙalubale, wanda ita ma Hukumar Aikin Hajji ta ƙasa (NAHCON), na fuskantar nata rikicin a ɓangaren shugabanci, duk da cewa abu ne da aka saba gani. Bayan kammala aikin Hajjin 2025, an buɗe wani sabon inda daga bisani kamar yadda aka saba, kanun labarai suka fara fitowa kan rahotannin zarge-zarge a salo daban-daban.
Abin da aka sanar da jama’a a watannin da suka gabata ba wai ilimantar ko ankararwa irin na aikin jarida ba kan gaskiya, illa labaran soki burutsu da ƙanzon kurege daga wasu ‘yan jarida da aka ɗauki hayarsu domin lalata amincewar da ke tsakanin jama’a, da shugabancin Hukumar Hajji ta Ƙasa (NAHCON), musamman babban shugabanta Farfesa Abdullahi Saleh Usman. An ƙirƙiro tare da tsara labaran ne a salon da ya ɗauki hankali ba bisa tsarin aikin jarida na gaskiya ba sai domin ɓata suna da matsin lamar ganin an sauya shugabanci ta hanyar amfani da farfagandar aikin jarida.
Ina rubuta wannan ne ba a matsayin mai kallo daga nesa ba, illa a matsayin wanda ke aiki a cikin hukumar tate da ganin yadda ake tafiyar da al’amura, kuma na fahimci nauyin aikin da aka ɗora mata tare da girmama hukuma da muhimmancin nauyin da take ɗauke da shi ga miliyoyin Alhazan Nijeriya.
Idan aka duba da kyau, tsarin ya bayyana sarai duba da yadda rahotannin suka dogaro da “majiyoyi” marasa tushe da ba su taɓa fitowa fili ba inda ake ambaton manyan jami’ai da ba za a iya tantance su ba tare da faɗo “masana” da ba su da cikakkiyar fahimta game da tsarin aiki da doka da kuma hulɗar diflomasiyya da ke tattare da gudanar da shiriya Hajji. Kowane labari yana fitowa ne a gaggauce amma babu wanda zai iya tsayawa idan an yi masa tambayoyin asali ya bayar da cikakkiyar amsa. Labarin ɗaya ne kullum, sai dai kalmomi ne kawai ake sauyawa ganin yadda a yau zai fito da taken “na musamman” ne, gobe kuma “binciken ƙwakwag”, washegari “tantance gaskiya” da dai sauransu wanda laƙabi kawai ake sauyawa, amma abun iri ɗaya ne.
A aikin jarida na gaskiya, tantance bayanai na zuwa kafin wallafawa, domin wannan shi ne ginshiƙin sahihanci, kasancewar ba a ɗaukar ɓangaren da ake zargi a matsayin abin dogaro ba tare da jin ɗayan ɓangaren ba. Amma da yawa daga cikin waɗannan labaran suna dogaro da jimla ɗaya kacal da ke cewa “an yi ƙoƙarin jin ta bakin hukumar amma bai yiwu ba”, domin rufe gazawar neman ɗayan ɓangaren labari wanda hakan ba ƙwazo ba ne, illa son kai da aka shirya domin cimma wata manufa ta kashin kai.
Abin lura shi ne, manyan kafafen watsa labarai masu daraja da suna suna guje wa waɗannan zarge-zarge, inda editoci ke neman hujjoji da takardu da gaskiyar lamarin, wanda wannan kaɗai ya isa ya faɗakar da jama’a. Zarge-zargen da ba za su iya tsallake gwajin tantancewa ba, sukan koma dandamali marasa tsari da ƙa’ida domin wasa da hankali.
Ya dace a tambaya: wace manufa waɗannan labaran ke da su? Idan gyara ake nema, da an fara da hujjoji tabbatattu da nazarin manufofi ba tare da son rai ba, da shawarwari a bayyane. Amma abin da muke gani shi ne hayaniya ba tare da shaida ba da kuma gaggawa ba tare da tushe ba. Irin wannan aikin ba gyara ba ne sai dai wani yunƙurin nufin matsa lamba ko neman wata dama wanda idan hakan ta ci tura, sai a ƙara ɓullo da wata dabara.
Wannan dabara ba sabuwa ba ce, sai dai sari da ake zargi kafin a fara tattaunawa, sannan a yi amfani da ita kan muradin jama’a, na buƙatar sanin gaskiya amma waɗanda suka ƙirƙiro labaran sun yi ne kawai domin buƙatar kan su da abinda za su samu da zaran sun wallafa kuma ba sai an kawo hujja ba saboda hayaniya ce manufar.
Yayin da ake fara shirye-shiryen Hajjin 2026, tun kafin a fara sarrafa biza ko kammala kasafi, an riga an fara kitsa irin waɗannan labarai wanda wannan ba wai hasashe ba ne, tsantsar shiri ne da suka fara tun tuni.
Abin da waɗannan masu kitsa labaran ba su fahimta ba shi ne NAHCON ba hukuma ce mai rauni da ke rayuwa da jin-ƙai ko kanun labarai ba. Hukuma ce ta doka, wadda Dokar NAHCON ta 2006 ta kafa, tare da bayyanannen nauyi na yi wa Musulman Nijeriya hidima a tafiyar Hajji, wadda ita ce mafi girman ibada a rayuwarsu. Tana da manufa a fili: samar da ingantattun ayyuka ga Alhazai. Hukumar ta fuskanci matsin lamba a baya kuma ta yi nasara akan guguwar da ta fi wannan ƙarfi.
Jama’a sun cancanci tsabtatavven bayani ba mai rikitarwa ba, tare sanin bambanci tsakanin aikin jarida na sa ido kan gaskiya da kuma matsin lamba da aka ɓoye da sunan nuna damuwa. Bugu da ƙari hujja da tsari da kuma manufa ta gari su na da muhimmanci.
Ga jama’a, roƙona a bayyane yake kancewa a lura da tsari tare da nuna shakka kan labaran da suke cike da zargi amma babu hujja. Sa’an nan jama’a su kwatanta aikin gudanar da Hajji mai natsuwa da tsari, da hayaniyar kanun labarai masu tayar da hankali.
Game da waɗanda ke cin riba ta hanyar yayata labaran da suka karkatar daga gaskiya, mun fahimci dabarunsu kuma irin waɗannan dabaru ba su daɗewa, hasali ma gaskiya ba ta buƙatar hayaniya domin ta yi halinta.
Hukumar NAHCON, za ta ci gaba da aikinta kuma Shugaban Hukumar zai ci gaba da sauke nauyin da aka ɗora masa, tare da cikakken goyon bayan kwamishinoni da kwamitin gudanarwa, ba don basa karɓar suka ba, sai don ayyukansu suna kan tsarin doka kuma suna da manufa da nufin hidima ga al’umma.














