Jama’a barkammu da sake haduwa da ku a cikin wani sabon shirin namu mai farin jini na Girki Adon Mace, wanda a yau za mu yi bayani kan yadda a ke yin miyar Zogala
Ga abubuwan da ake bukatar uwargida ta tanada kamar haka;
Zogale busasshe, Nama, Maggi, Albasa, Attarugu, Gyada (daidai misali), Citta, Tafarnuwa idan tana bukata.
Da farko za ki wanke namanki ki sa albasa da maggi ki dora a wuta ki tafasa, sai ki gyara zogalanki ki ajiye a gefe ki jajjaga Attarugu da Albasa da Tafarnuwa da citta ki a jiye a gefe.
Sai ki duba namanki idan ya yi sai ki zuba jajageggen attarugun ki kara ruwa ki sa Maggi da Gishiri dan kadan sai ki rufe ya yi kamar minti biyar.
Idan ya yi sai ki zuba zogalen ki rufe ya yi minti biyar shima sai ki zuba gyadarki ki rufe.
Idan ya nuna za ki ji yana kamshi, sai ki sauke, shi kenan miyar ta hadu. Ana iya cin miyar zogale da tuwo kowane iri.