Gurjiya (Bambara Nut), tana saurin girma yayin da aka shuka ta; sannan kuma ta fi bukatar yanayi mai dumi, kazalika ba ta bukatar yanayi mai sanyi a lokacin da take girma.
Haka zalika, ana safarar buhunhunanta daga kasuwar Alkaleri da ke Jihar Bauchi, zuwa wasu kasuwanni da ke fadin wannan kasa, domin hada-hadar kasuwancinta.
Akasari, an fi yin nomanta a Arewacin Nijeriya; sannan an fi shuka ta a lokacin damina, Irin da ake amfani da shi wajen shuka ta, yana rubewa a kasa ne; bayan kwana tara da shuka shi.
Har ila yau, ana kuma iya shuka ta ita kadai ko kuma a hada ta da sauran wasu amfanin gonan, amma ta fi son a shuka ta ita kadai; mai makon tare da wasu amfanin gonar, domin kuwa za su iya jawowa a kasa samun amfanin da ake bukata a lokacin girbinta, sannan ita ko kadan ba ta iya jurewa fari.
- Gwamna Yusuf Zai Ayyana Dokar Ta-É“aci A Fannin Ilimi A Kano
- 13 Ga Wata Za A Yanke Hukuncin Hurumin Shari’ar Sarkin Kano
Ana fara shuka Irinta ne, bayan an tabbatar ruwan sama ya daidaita, inda kafin fara yin shukar; ake fara gyaran gona da kuma yin haro, haka nan kokadan nomanta ba shi da wuya; sannan kuma ba a kashe kudi da yawa, kazalika; ba a bukatar zuba mata takin zamani ko maganin feshi kamar yadda ake zuba wa sauran amfanin gona.
Har wa yau, Abin da kawai ke da wuya a nomanta shi ne; lokacin girbinta, domin akwai wuya sosai ganin cewa; daya bayan daya ake cire ta daga kunyar da aka shuka ta, kana kuma ana samun amfaninta da dama bayan an girbe ta, wakazika ana bukatar wanda ya shuka ta ya kasance mai matukar hakuri; sakamakon lokacin da ake batawa wajen girbe ta.
Bugu da kari, tana kuma kai wa kimanin wata biyar zuwa shida kafin ta kammala nuna, ana kuma girbe ta a tsakanin watan Okutoba zuwa watan Nuwamba, sannan ganyenta na komawa Ja bayan Irin nomanta ya kammala nuna .
Haka nan kuma, akwai hanyoyi da dama da ake girbe Irin nomanta, domin kuwa za ka iya tuge ta tun daga Jijiyarta ko kuma ka bar ta ta bushe, sai ka yi amfani da Fatanya wajen cire ta.
Har ila yau, za ka iya samun kimanin buhu 20 a cikin kowacce kadada daya, amma ya danganta da ingancin kasar noman da aka shuka ta.
Ana Bukatar A Adana Ta Yadda Ya Kamata Bayan An Girbe Ta:
Bayan an girbe Gurjiya, da akwai kwarin da suke iya yi mata illa, saboda haka, ana bukatar wanda ya noma ta; ya tabbatar ya adana ta a wurin da babu abin da zai same ta.
Kwanakin Da Amfanin Gurjiya Ke Dauka Kafin Ya Kammala Girma:
A cikin kwanaki 150 Gurjiya ke kammala girma, idan kuma aka shuka ta a kasar noma mai kyau ko wadda ta dace, manominta zai samu saukin kashe kudin da dauko hayar masu aiki tare da kara samun amfani mai yawan gaske da ka iya kai wa kimanin kashi 28.8 cikin dari tare kuma da samun riba mai dimbin yawa.
Nawa Farashinta Yake A Nijeriya?
Farashin kowane kilo daya na Gurjiya a Nijeriya, ana sayar da shi kan kudi Naira 86,300.00.
Jihohin Da Ake Noman Gurjiya A Nijeriya:
A binciken da Alhassan da Egbe suka gudanar a shekarar 2013 ya nuna cewa, kashi 65.8 cikin dari; an fi noma ta a Jihohin Biniwe da kuma Kogi.
Yaya Ake Noman Gurjiya:
Ta fi saurin yin girma a yanayin noma mai kyau, sannan kuma tana bukatar ta rika samun hasken rana, kazalika kuma yawan samun ruwan sama yana taimaka mata wajen saurin girma da wuri.
Gurjiya Na Kara Wa Dan’adam Lafiyar Jiki:
Har ila yau, Gurjiya na dauke da sinadarin ‘carbohydrates, protein, fatty acids, potassium, magnesiumiron da kuma zinc’, wadanda dukkaninsu suna da matukar amfani a jiki Dan’adam, ta hanyar kara masa lafiya da kuma kuzari.