Kamar yadda bincike ya tabbatar, Nijeriya ce kan gaba wajen samar da Irin Karkashi, har ila yau a farkon shekarar 2018, Nijeriyar ce a kan gaba wajen fitar da Karkashin zuwa wasu kasashe na duniya.
Har wa yau, Nijeriya ce ta biyu a Afirka kuma ta bakwai a duniya wajen nomansa. Sa’annan, hada-hadar kasauwancinsa a kasuwar duniya na kara habaka, musamman a yankin Asiya da kuma Nahiyar Turai, inda kuma kasashen Japan da China suke shiga da Karkashin kasashen nasu daga Nijeriya.
- ‘Yan Bindiga Sanye Da Hijabi Sun Farmaki Ofishin ‘Yansanda A Katsina
- Nijeriya Na Fatan Samun Karin Masu Zuba Jari A Taron Kasuwanci Na Duniya
Bugu da kari, Kasashen Turkiyya, Indiya, Poland da kuma Netherlands, su ne a kan gaba wajen fitar da wannan Karkashi.
Wane Lokaci Ne Ya Fi Da Cewa A Shuka Karkashi:
Bincike ya nuna cewa, a yankin Kharif da ke Arewacin Kasar Indiya da kuma Kudancin Kasar, an fi yin noman Karkashi a lokacin rani, haka nan a nan Nijeriya an fi yin nomansa a wannan lokaci na rani.
Tsawon Lokacin Da Karkashi Ke Dauka Kafin Ya Girma:
Karkashi na kai wa tsawon kwana 100 zuwa 135 kafin ya gama girma baki-daya.
Ribar Nawa Ake Samu Daga Ganyensa Da Aka Sayar?
Ana iya samun akalla ribar Naira 60,036,06 a duk kadada daya da aka noma, sannan bayan an girbe shi za kuma a iya samun kudaden shiga akalla Naira 184,701,98, a kowace kadada daya, inda za a iya tara ribar da ta kimanin Naira 124,665,92.
Girbin Karkashi A Duk Kadada Guda Na Kaiwa Nawa?
Jumullar abin da ake samu bayan an yi girbi a kowace kadada na da yawan gaske, amma kuma ya danganta da ingantaccen Irin da aka yi amfani da shi wajen shuka.
Domin kuwa, zai iya yiwuwa a kowace kadada daya a samu daga kilo 200 zuwa 500.
Wane Takin Zamani Ya Fi Dacewa A Yi Amfani Da Shi?
An fi so a yi amfani da nau’in takin zamani na NPK, sannan an bayar da shawarar sanya takin NPK din buhu uku da kuma nau’in takin zamani na Urea.
A Ina Aka Fi Yin Noman Karkashi A Nijeriya?
An fi yin noman Karkashi a garuruwan Keffi, Lafiya, Doma da ke a Jihar Nassarawa, sai kuma a Jihohin Taraba da Makurdi da ke Biniwe.
Har ila yau, ana yin remon Irin Karkashi a jihohi kamar su Ebonyi da Delta da Jigawa da Bauchi da Nassarawa da Benuwe da Maiduguri da Katsina da Taraba da sauransu.
Wane Lokaci Ya Fi Dacewa A Shuka Karkashi?
Wannan ya danganta da irin yanayin da ake ciki na lokacin yin noman, amma ya fi kyau a lokacin da ma’aunin yanayi ya kai kimanin 70.
Matakan Fara Yin Nomansa:
Zabar Gonar Da Za A Shuka Shi: Ana son a zabo kasar noman da ta fi dacewa da shuka shi, sai dai wannan abu ne mai sauki a Nijeriya; domin kuwa tana da kasar noma mai kyan gaske da za a iya shuka shi ba tare da fuskantar wata matsala ba.
Zabo Ingantaccen Iri:
Ana bukatar a samu ingantaccen Iri wanda ya kamata a shuka, inda ake da nau’ikan Irin har kala biyu, mai ruwan kasa da kuma fari.
Gyaran Gonar Da Za A Shuka Shi:
Yana da kyau kafin a fara shuka shi a tabbatar da an gyara gonar, musamman wajen cire ciyawa ta yadda zai girma da wuri kuma cikin sauri.
Ana shuka Irinsa a kasar noman da aka yi wa haro, inda ake bukatar a shuka Irin daga kilogiram 4 zuwa 5, sannan kuma ya kamata a sani cewa; a duk Irin Karkashi a kadada daya, ana samun kimanin tan 1 zuwa 1.5 a duk shekara.
Lokacin Girbe Shi:
A nan ko shakka babu, ya na kai wa akalla wata biyar kafin ya gama girma baki-daya.