Assalamu alaikum masu karatu, barkanmu da sake haduwa da ku a wannan makon a cikin shirin na mu mai farin jini da albaka na Girki Adon Mata.
A yau shafin namu zai koya muku yadda ake Tuwan Amala da miyar Ewedu:
- Yadda Tashar Jirgen Ruwan Apapa-Moniya Za Ta Taimaka Wa Masu Safarar Fitar Da Kaya
- Sin Za Ta Kara Harajin Fito Kan Hajojin Amurka Da Ake Shigarwa Kasar Zuwa 125%
Amala da miyar Ewedu abinci ne da ake matukar so musamman a yankin Yarabawa na Nijeriya.
Ga dai abubuwan da ake bukata wajen hadawa:
Garin Alabo (garin danyen doya da aka busar)
Ga kuma yadda ake sarrafawa:
Da farko, a zuba ruwa a tukunya a sa a wuta domin ya tafasa.
A rage wuta kadan, sannan a zuba garin alabo a hankali cikin ruwan da ke tafasa, ana juyawa da muciya ko cokali ko leda mai kauri don kada ya yi kolalla.
A ci gaba da juyawa har sai ya hade sosai kuma ya zama mai laushi.
Idan yana da kauri sosai, sai a kara dan ruwan zafi kadan wanda dama kin rage, kuma a ci gaba da juyawa har sai ya yi laushi.
A rufe shi na ‘yan mintuna kafin a sauke.
Sai kuma yadda ake miyar Uwedu:
Iata ma ga abubuwan da ake bukata domin hada ta:
Ganyen Ewedu (fresh leabes)
Kanwa ko potash (dan kadan),Gishiri, Magi, yaji
Sai kuma yadda ake hadawa:
A gyara ganyen Ewedu, a wanke su da kyau.
Sannan a zuba ruwa kadan a tukunya, a sa kanwa ko potash, a sa a tafasa.
Idan ruwan ya tafasa, sai a zuba ganyen uwedu, a dafa na kimanin minti 5–7. A sauke, sannan a daka a cikin turmi ko a murza da blender idan ana so ya zama ya yi laushi. Sai a mayar da shi tukunya, a sa gishiri da maggi da yaji idan ana so, a dafa na minti kadan sai a sauke.
A ci dadi lafiya.
Za’a dan iya zuba miyar ja ko nama ko ganda ko kifi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp