Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
ADVERTISEMENT
Home AL'ADU

Yadda Al’adun Aure Ke Gudana A Kasar Nijar

by Sulaiman Ibrahim
April 9, 2021
in AL'ADU
4 min read
Yadda Al’adun Aure Ke Gudana A Kasar Nijar
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Daga Auwal Mu’azu.

Assalamu Alaikum Warahmatullahi Wabarkatuhu.
Mun tattaro muku bayanan wannan makala ne daga shirin Mutum da Al’adunsa, wanda Nana Aicha Hamissou ke gabatarwa a Zauren Marubuta da ke Taskar Bakandamiya. Shiri ne da ke kawo bayanai mai zurfi game da al’adun mutane daban-daban a kasar Hausa da ma sauran kasashe da al’ummomi na duniya.
Barkanmu da warhaka barkanmu da saduwa da ku a cikin wannan shiri na Mutum da Al’adunsa, shiri da zai ke kawo muku bayanai na al’adun Hausa da sauran kabilu. A yau cikin shirin zan fara kawo muku al’adun aure a kasar Nijar.
Kafin mu tsunduma cikin shirin zan kawo maku sunayen garuruwan Nijar da kuma wasu yarensu, sannan kowanne gari da irin yarensu.
Nijar kasa ce da take da garuruwa guda takwas da gunduma kimanin araba’in, ga su kamar haka: Niamey (Capital ta Nijar), Maradi, Zinder, Tahoua, Agadez, Diffa, Tillabery da Dosso.
A cikin wadannan garuruwan kowanne yana da yarensu, kamar misali Maradi gari ne wanda ya hada katsinawa da gobirawa, duk wanda yake dan asalin garin Maradi to Bakatsine ne ko kuma Bagobiri. Sai dai akwai sauran yaruka kamar Tagamawa, Adarawa, Arawa, Zabarmawa, Fulani da Buzaye, da sauransu. Kuma kowanne kabila idan suka tashi aure da irin al’adar da suke gudanarwa, zan kawo su daki-daki in sha Allah.
Haka kuma Zinder gari ne na Damagarawa su ma da yadda suke al’adarsu.
Niamey garin zabarmawa ne, amma gaban Niamey akwai wani gari mai suna Torodi can fulani ne, su ma da yadda suke al’adarsu ta aure.
Dosso ma zabarmawa ne cikin garin amma dai suna da arawa cikin garin Dogon Dutci.
Tillabery ma zabarmawa ne sai dai suna da fulanin Zabarmawa.
Agadez garin Buzaye ne su ma da al’adarsu ta aure.
Tahoua garin Adarawa ne suna da buzaye su ma.
Diffa garin barebari ne su ma da al’adarsu ta aure.
Sai dai gabadaya waɗannan garuruwan guda takwas na Nijar babu inda babu Hausawa a ciki sai kamar gari uku (Niamey, Dosso da Tillabery) su ne Hausawa suka yi karanci a can, dan wasu ma babu abin da suka iya a Yaren Hausa, sannan kuma duk yarensu daya ne wato zabarmanci.
Wasu Hausawan in suka tashi aure suna daukar al’adar garin da suke ko da ba tasu ba ce, wasu kuma suna amfani da al’adarsu ta Hausawa domin gudanar da shagalin aurarrakinsu.
Bari mu fara da Maradi kai tsaye.
Maradi
Maradi gari ne wanda ya hada Katsinawa da gobirawa, da sauran wasu kabilu kamar: tagamawa, adarawa, fulani, buzaye, arawa, shuwa arab, zabarmawa, da barebari, gwarawa da sauransu.
Wanda duk ya kasance ɗan asalin Maradi ne to zai tabbatar maka da bakatsine ne ko kuma Bagobiri. Katsinawa suna da sarkinsu wato Alhaji Ali Zaki wanda ake kiransa da sarkin katsinar Maradi wanda gidansa yake cikin garin Maradi.
Haka suma Sarkin Gobirawa yana a cikin garin Tibiri-gobir wanda yake kilo meta uku (3) daga Maradi a hanya mai zuwa Yamai gaban asibiti wanda ake kira uwa da danta mai garinsu sunansa mai martaba Alhaji Abdu Bala Marafa.
Gaba daya Tibiri gaskiya gobirawa ne ba kamar Maradi ba da ake samun sauran kabilu sai dai haka wadanda aiki ya kawo nan garin.
A Al’adar auren wadannan mutanen wadanda suke ƴan sarki akwai yadda suke gudanar da shagalin bikinsu na gargajiya, wasu sun bari wasu kuma suna kan bakansu har gobe suna yi.
Za mu fara gabatar da al’adar aure ga wadanda ba ƴan gidan sarauta ba kamar na sauran wasu yare da suke Maraɗi wato mu kenan.
A wannan zamanin da muke ciki yawanci samari idan sun ga budurwar da ta yi masu, wasu kafin su tunkareta da suna sonta sai sun fara yin bincike a kanta sannan su fara zuwa neman izinin zance a wajen iyayenta, wasu kuma kawai fara zuwa suke yi har sai sun daidata sannan su turo iyayensu a nema masu auren budurwa. Kowanne dai da yadda yake yi. Wasu kuma in har ba su tashi aure ba kuma suna son budurwa to sai su aika da kudin tambaya gudun kar wani ya riga su. Idan har saurayi yana son budurwa to kafin auren duk lokacin sallah karama farkon azumi sai ya kai sikari(sugar) da kudin kayan sallah gidansu budurwa har zuwa lokacin da za a yi aurensu.
Yadda ake kai kudin aure
A nan Maradi in za a kai kudin ana kai wa gidan yayan uba, ko kuma gidan su amarya din. Wasu da dare suke kai kudin auren wasu kuma da yamma.
Idan za a kawo kudin aure a gidansu amarya ana dafawa dangin ango abinci mai rai da lafiya kamar kaji da lemo haka. Idan ma akwai hali irin sosai ɗin nan wasu har rago suke yankawa. Ya dangata dai daga halin gidan su amaryar. Ko kafin dangin ango su iso an gyara masu abincinsu an zuba cikin manyan kuloli an jere masu kuma an tanadar masu lemo.
In dangin ango sun iso kamar iyayensa maza da mata da abokansa kuma duk suke zuwa cikin motoci.
Za su zo da goro da kudi (kuma masu yawa fa tunda yawanci masu karamin karfi ne ma suke kai jikka dari biyar wanda ya kai kudin Nijeriya nera dari uku da wani abu, wasu kuma suna kai millions ya danganta dai daga halin miji), da kuma akwati. Wasu kuma suna kawo lefe cikin akwatina, wasu kuma suna kawo akwatina babu komai sai su ba wa amarya kudi ta siyi kayan da take so da kanta ta zuba ciki.
Idan sun gama ba da kudi da komai sai a ba su abincin da aka dafa masu da kuma lemo su tafi da shi gida haɗe kuma da kuɗi wanda kamar tukwici ne haka.
Yawanci wadanda suke kawo kudi da dare to gidan amarya ba su wannan dafa abincin sai dai kuma su bayar da kuɗi tukwici ga wadanda suka kawo, amma dai wasu suna dafawa.

SendShareTweetShare
Previous Post

An Kaddamar Da Manyan Ayyukan Da Aka Zubawa Jarin Yuan Biliyan 72 A Xinjiang

Next Post

Za Mu Iya Samun Nasara A Wasa Na Biyu – Mbappe

RelatedPosts

Barebari

Barebari Da Al’adunsu Na Aure

by Sulaiman Ibrahim
3 months ago
0

Gabatarwa: Kanuri suna ne na wata ƙabila daga cikin manyan...

Al’adun Auren Zawarawa A Kasar Hausa   

Al’adun Auren Zawarawa A Kasar Hausa  

by Muhammad
6 months ago
0

Ma'anar Al'ada Kalmar Al'ada ta sami ma'anoni daga masana daban-daban....

Mawaka Da Kidan Gargajiyar Hausa

Mawaka Da Kidan Gargajiyar Hausa

by Sulaiman Ibrahim
8 months ago
0

Wannan wani guzuri ne da na ci karo da shi...

Next Post
Mbappe

Za Mu Iya Samun Nasara A Wasa Na Biyu - Mbappe

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version