Amurka ta sake hana Palasdinawa cimma burinsu na kafa kasarsu mai ’yancin kai.
A ranar 18 ga wata, a yayin da kwamitin sulhun MDD ke kada kuri’u a kan wani daftarin shiri game da bukatar Palasdinu ta zama mamba a MDD, kasar Amurka ta sake hawan kujerar na ki, kuma ita ce kasa kadai da ta kada kuri’ar nuna rashin amincewa. Idan ba a manta ba, tuni a yau shekaru 13 da suka wuce, Palasdinu ta mika rokon zama mamba a MDD, amma sakamakon yadda ita Amurka ta hana, ba a kai ga mika shi ga babban taron MDD ba.
- Kusan 90% Na Masu Amsa Tambayoyin Duniya Sun Yaba Da Gudummawar Da Sin Ke Bayarwa Ga Bunkasuwar Duniya Irin Na Kiyaye Muhalli, A Cewar Binciken Jin Ra’ayin Jama’a Na CGTN
- Yankin Kudancin Tekun Pasifik Ba Zai Zamo Dandalin Hamayyar Kasashe Masu Karfi Ba, In Ji Ministan Wajen Sin
Sai dai ko shugaban kasar Amurka ko sauran manyan jami’an kasar, sau tari ne suka bayyana goyon bayansu ga shirin samar da kasashe biyu a matsayin hanya daya tilo mai dorewa ta zaman lafiya ta tsakanin Palasdinu da Isra’ila. To, amma idan ba ta amince da kafa kasar Palasdinu mai ’yancin kanta ba, ina ne za a yi zancen “samar da kasashe biyu”.
Lallai amsa ita ce, zakin baki ba wani abu ba ne, amma kome shawara da za a yanke, dole ne ta amfana wa muradun kasar Amurka. Sanin kowa ne Amurka na da alaka ta kut da kut da Isra’ila ta fannoni daban daban, musamman ma a lokacin da Amurka ke dab da fara babban zaben kasar, ba za ta iya raba kai da Isra’ila ba. Idan Palasdinu ta kai ga zama mamba a MDD, za ta samu damar kara fito da muryarta a duniya tare da samun karin goyon baya, matakin da ka iya matsa wa Isra’ila, baya ga lalata muradun Amurka a yankin gabas ta tsakiya.
Rikici na ci gaba a tsakanin Palasdinu da Isra’ila, wanda yake ta haifar da mummunan tasiri ga sauran kasashen yankin. A cikin irin wannan hali, duk kasar da ke da niyyar tabbatar da ganin an tabbatar da zaman lafiya a yankin, za ta nuna goyon baya ga“samar da kasashe biyu” da kuma mayar da Palasdinu a matsayin mamba a MDD. Amma ga abin da ‘yan siyasar Amurka suka yi, a zahiri dai, abin da ke jawo hankalinsu bai taba zama zaman lafiyar yankin gabas ta tsakiya ba, a maimakon hakan, abin da suke mai da hankali a kai shi ne kare muradunsu.
Amma abin farin ciniki shi ne, daukacin kasashen duniya na goyon bayan zaman lafiya da adalci. Don haka ma, muna da imanin cewa, ko ba dade ko ba jima, Palasdinu za ta samu kujerarta a MDD kamar yadda sauran mambobin MDD suke, kuma kasancewarsu kasashe biyu, Palasdinu da Isra’ila za su zauna lafiya da juna a tsakanin makwabciyar juna. (Mai zane: Mustapha Bulama)