Mahdi M Muhammad" />

Yadda Biri Ya Far Wa Wata Karamar Yarinya

Jama’a na ta cece-kuce a kafafen sada zumunta akan yadda wani goggon-biri da ya tsere daga cibiyar kula da dabbobi ya far wa wata yarinyar da ba ta ji ba ba ta gani ba akan hanyarta ta zuwa makaranta.

Amma Dakta Flora Ilonzo, wacce ta kafa cibiyar kula da dabbobi da bada da magunguna (CPHA), a Jihar Anambra, ta musanta zargin na cewa, goggon-birin da ya tsere daga cibiyarta ne ya far wa wata yarinya ‘yar makaranta.

Ilonzo ta fadi hakan ne a cikin wata sanarwa da aka bayar ga Kamfanin dillancin labaran Nijeriya (NAN), ta hannun mai taimaka ma ta ta fuskar yada labarai, Mista Okechukwu Onugbue, a ranar Juma’a, a Awka da ke jihar Anambara.

Ta karyata zargin, tana mai cewa, karamin birin da ya tsere lokacin da ake tsabtace kejinsa ne a safiyar Laraba ya far wa dalibar.

Ta ce, tun daga wancan lokacin aka sake wa birin sabon keji mai tsoro sosai biri.

Ya ci gaba da cewa, “Muna cikin share kejin birin a safiyar ranar Laraba, abin takaici sai kawai birin ya gudu ya ciji wata yarinya da ke kan hanyar zuwa makaranta. Mahaifinta ya zo harabar gidana don ya tambaye ni sunan allurar da za a yi amfani da ita don kula da ’yarsa. An kuma kai ta asibitin Assumpta, kuma likitan ya nemi ya zo wurina domin in fada masa sunan allurar da za a yi amfani da ita.”

“Na je wancan asibitin kai tsaye na nuna musu allurar riga-kafin cutar cizon birin, domin na je da kaina don neman allurar, amma ban samu ba a Awka. Na yi odar allurar ne daga Onitsha, kan kudi Naira 18,500, kuma na je asibitin domin ganin wacce abin ya shafa da kuma likita da ke kula da ita, don tambayar su ko sun samu allurar, amma likitan ya ce basu samu ba kuma har yanzu suna bukatar ta. Na bukace su da su kwantar da hankalinsu cewa na yi shiri don a kawo allurar cikin gaggawa. Lokacin da allurar da na umarta ta iso, na ba su kuma an yi wa yarinyar allurar, kuma sun ce zasu sallame ta da yammar ranar. An kuma sallami yarinyar daga asibiti. Duk abin da nake yi shi ne don yarinyar ta warke,” in ji ta.

NAN ta ruwaito cewa, wani likita a asibitin Assumpta, wanda baya son a ambaci sunansa, ya tabbatar da faruwar lamarin, sannan kuma ya ce an sallami yarinyar daga asibiti.

A cikin martanin gaggawa, Mista Haruna Muhammed, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda na Anambra (PPRO), a cikin wata sanarwa, ya tabbatar da labarin da aka yada a kafafen yada labarai cewa, goggon-biri ya tsere daga CPHA kuma ta ji wa wata yarinya ‘yar makaran rauni.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, rundunar tana hada kai da hukumomin gwamnati da abin ya shafa domin tabbatar da cewa an kiyaye dabbobin da ke cibiyar don kiyaye sake afkuwar irin wannan lamarin.

Exit mobile version