Attajirin da ya fi kowa kudi a Afirka, Alhaji Aliko Dangote, ya kaddamar da rabon abinci kyauta ga al’ummar Musulmi akalla 10,000 a Jihar Kano, jiharsa ta asali, ta hannun Gidauniyar Aliko Dangote.
Har ila yau, gidauniyar ta fadada karamcin ta hanyar raba buhunan shinkafa miliyan daya da kudinsu ya haura Naira biliyan 13 a fadin jihohi 36 na tarayya da Babban Birnin Tarayya Abuja domin rage yunwa a kasar nan.
Manufar wannan tallafi ita ce a sassauta wa miliyoyin ‘yan Nijeriya matsin da suke sha sakamakon kalubalen tattalin arziki da kasar ke fama da shi.
Wannan duka kari ne a kan rabon burodi 20,000 a kullum ga mazauna Kano da kuma wasu 15,000 ga mazauna Legas, inda tsarin ciyarwar da aka fara kuma ya dore tun daga 2020 a lokacin annobar COVID-19.
Abincin da ake dafawa na buda-bakin Ramadan kyauta ya hada da shinkafa dafa-duka, farar shinkafa da miya, taliya dafa-duka, doya, wake da naman kaza da na saniya, kana da ruwan sha na gora ga kowane mutum.
Ana raba kunshin abincin ne a masallatan Juma’a da tituna da gidajen yari da gidajen marayu da gidajen riman (na tsare mutane) da sauran wurare a cikin birnin Kano da kewaye.
Wani da ya ci gajiyar abincin mai suna Musa Maikatako, mazaunin Tarauni ya nuna jin dadinsa da wannan karimcin wanda ya ce ya taimaka masa wajen yin buda baki cikin sauki.
Maikatako, wanda a bayyane fuskarsa na cike da farin ciki, ya ce abinci na kyauta ya kawar da wahalhalun da jama’a da dama za su iya fusktan wajen yin buda baki da ruwa kawai, ba tare da abinci ba, bisa la’akari da halin kuncin da ‘yan Nijeriya ke ciki.
“Ba zan iya bayyana irin farin cikin da nake ciki ba, wannan abincin zai taimaka matuka wajen taimaka wa talakawa kamar ni mu samu abin da za mu yi buda baki da abinci mai nauyi.
“Na san mutane da yawa a jihar nan wadanda za su iya yin buda baki da ruwa kawai. Don haka wannan abincin ya kawo sauki kwarai da gaske,” in ji shi.
Da yake nuna farin cikinsa, Maikatako ya nuna godiya ga Gidauniyar Dangote bisa wannan karamcin, inda ya yi addu’ar Allah ya kara masa arziki, ya kuma ci gaba da sanya albarka a kasuwancinsa.
Har ila yau, wata da ta ci gajiyar tallafin, Hajiya Inna Tukur, ta bayyana jin dadin ta da rabon abincin, wanda a cewarta Gidauniyar Aliko Dangote ta kawo mata dauki.
A cewar Inna, ta yi farin ciki da irin wannan abinci mai dadi da ake ba ta kyauta a halin matsin da ake ciki.
“A cikin wahalhalun da ake fama wanda yana da kamar wuya mu iya cin abinci ko da sau biyu a rana, amma sai ga shi cikin ludufi, an samu wani yana taimaka mana da abinci mai lagwada, gaskiya wannan ba karamin abu ba ne.
“Ba abin da zan ce sai dai in yi godiya ga ku da Aliko Dangote, ina rokon Allah ya kara muku albarka.”
Baya ga rabon burodi da aka kwashi tsawon shekara 4 ana yi kyauta, Gidauniyar Dangote ta shafe sama da shekaru 30 tana ciyar da mabukata a Kano. Ana yin hakan ne daga gidan mahaifiyarsa da ke Koki da kuma wasu wuraren dafa abinci daban-daban. Wannan shiri na ciyarwa yana ciyar da mazauna Kano 10,000 a kullum tun daga karin kumallo, abincin rana, da kuma abincin dare tsawon shekara 30 ba fashi.