A daidai lokacin da Abuja ke shirye-shirye yin bankwana da Shugaban kasa Muhammad Buhjari a yayin da wa’adin mulkinsa da ya shafe shekara 8 yana jagorantar Nijeriya ke cika, su kuwa al’umma Jiharsa ta Katsina musamman garin haihuwarsa ta Daura sun dukufa cikin shirin ganin sun yi wa dan nasu gaggrumar tarba tare da shirya gangami na al’ummar jihar don nuna godiyarsu ga Allah da ya bashi ikon kammala wa’adin mulkinsa lafiya.
A cewar, wani jigo a yankin, wannan wata baiwa ce da ya kamata su gode wa Allah, suna kuma godiya ga al’ummar Nijeriya a bisa goyon baya da suka ba dan nasu har ya samu wannan nasarar.
- Da Dumi-Dumi: Wanda Ya Assasa Bankin FCMB, Subomi Ya Rasu Ya Na Da Shekara 89
- EFCC Na Binciken Gwamnan Zamfara Kan Almundahanar Biliyan 70
Tun a kwanan baya, mai martaba Sarkin Daura, Alhaji Umar Faruk Umar ya sanar da cewa, masarautar za ta shirya wa Shugaba Buhari gagarumin hawan daba domin yi masa lale marhabin da dawowa gida.
Alhaji Muhammad Saleh, shi ne shugaban kungiyar “Concern People Forum” da ke masarautar Daura wadanda suke jagorantar shirye-shiryen gangamin tarbar shugaban kasa Muhammad Buhari a ranar 29 da watan Mayu na wannan shekara da wa’adin mulkinsa ke karewa.
Ya tattauna da LEADERSHIP Hausa game da shirye-shiryen da suke yi wanda ya ce suna sa ran manyan mutane za su shiga cikin lamarin domin karrama Shugaba Buhari a mahaifarsa kamar yadda ya kamata.
A cewar Muhammad Saleh, yanzu haka sun fara samun gudunmawa daga mai martaba Sarkin Daura, Alhaji Umar Faruk Umar domin ci gaba da shriye-shirye, haka kuma shi ma shugaban jam’iyyar APC na Jihar Katsina ya ba da tasa gudunmawar, kuma suna sa ran cewa wasu ma na kan hanya.
Ga yadda hirar ta kasance:
Ya ake ciki dangane da batun shirye-shiryen da kuke yi na tarbar Shugaban Kasa Muhammad Buhari da ke kammala wa’adin mulkinsa a ranar 29 ga watan Mayu?
Gaskiya muna nan muna ci gaba da shirye-shiryen tarbar mai girma shugaban Kasa idan Allah ya kaimu wa’adin mulkinsa ya kare a ranar 29 ga watan Mayu na wannan shekara ta 2023 a nan garin Daura idan Allah ya yarda.
Kamar dame-dame kuka shirya domin tarbarsa?
Muna son dai, mu tarbe shi, a ga jama’a sun tarbe shi ya dawo gida cikin farin ciki da walwala, shi ne muke shirya cewa za mu yi riguna da huluna wadanda za mu ba matasa su sanya, sannan za mu yi manyan alluna na sawa a kan titi na nuna murnar shugaban kasa ya dawo gida lafiya, ya gama aikinsa na shekara takwas, haka kuma za mu yi amfani da motoci wajen wannan tarba, za mu sanya mawaka da makada da za su kawata wannan tarba.
Kamar mutum nawa kuke sa ran za ku gayyata domin wannan biki na tarbar shugaban kasa?
Muna sa ran kowace karamar hukumar da ke cikin masarautar Daura za mu gayyaci akalla motoci goma da za su dauko jama’a zuwa tarbar shugaban kasa, kuma muna tsammanin kowace mota za ta dauko mutum 10.
Ya batun sanya manyan mutane cikin wannan hidima ta tarbar shugaban kasa?
Gaskiya, mun sanya manyan mutane daga masarautar Daura musamman wadanda ke son su ga an yi wannan hidima, yanzu haka akwai wasu dattawa da suke tattaunawa a kan wannan muhimmin batu na tarbar shugaban, kuma ni ma zan hadu da su domin tattaunawa ta yadda za a kara kawata wannan hidima a samu nasara, kamar uban kasa mai martaba Sarkin Daura ya shigo cikin wannan lamari, sai kuma ita kungiyarmu ta “Concern People Forum” ta shiga sosai, mai martaba Sarkin mun sanar da shi, kuma ya goyi bayan mu, har ya ba mu gudunmawa ta naira miliyan daya, ya ce mu je mu ci gaba da shirye-shirye shi ma yana da nashi shirin na yin Daba.
Kamar me ya bambamta wannan tsari naku da kuma na ita masarautar Daura tun da ita ma za ta shirya tarba ga shugaban kasa Muhammad Buhari?
Abin da ya bambamnta namu da kuma na masarauta shi ne, masarauta za ta shirya hawan Daba inda za a hau dawakai da hakimai da sauransu, mu kuma za mu tarbo shi ne da motoci a ya yin da wasu kuma a kasa za su rika takawa.
Ka yi maganar Sarkin Daura ya ba ku gudunmawa ta Naira miliyan daya, ga shi wannan taro yana bukatar kudi, yaya kuka tsara yadda za ku samu kudaden da za ku gudanar da wannan tarba cikin nasara?
Yanzu dai maganar da ake yi shi ne, mai martaba ya fara ba da gudunmawa, sai kuma shugaban jam’iyyar APC na jihar Katsina, Alhaji Sani Aliyu (JB) shi ma ya ba mu gudunmawa, ya zuwa yanzu wadannan gudunmawa guda biyu kadai suka shigo hannunmu, duk da cewa mun raba takardun neman gudunmawa muna kuma jiran amsa daga wadanda muka tura wa, daidai abin da muka samu da shi ne zamu yi amfani, idan mun samu kudi da yawa taro zai kawatar, idan kuma kadan aka samu za mu yi abin da ya sauwaka.
Shin me kuke fatan nunawa ga duniya ta hanyar wannan tarba da za ku shirya wa shugaban kasa ta dawo gida bayan kammala wa’adin mulkinsa?
Muna son duniya ta san cewa har yanzu dai mutanen kasar Daura suna son dansu, dansu ya je ya yi aiki, ya dawo sun tarbe shi, daman abin da ya kamata kenan, idan mutum ya bar gida zai dawo, to al’ummarsa su fito kwansu da kwarkwata su nuna jin dadi da dawowarsa, su nuna murna tun da ya yi wannan aiki ya gama lafiya.