Kungiyar dattawan Arewa (NEF) ta nuna rashin jin dadinta akan yadda ‘yan ta’adda suke samun damar shiga makarantun da suka hada dana Sakandare da kuma manyan makarantu wadanda ‘yan ta’adda da sauran masu aikata laifuka da suka hada da har da garkuwa da mutane.
Wata sanarwar da aka rabawa amnema labarai a Abuja da ke dauke da sa hannun Shugaban kungiyar Farfesa. Dokta D.D. Sheni,ya bayyana an kusa shekara goma tun lokacin da aka dauki ‘yan makarantar mata ta Chibok masu yawa ta Jihar Borno, sannu a hankali sai al’amarin garkiwa da ‘yan makaranta yake daukae wani sabon salo.
- Shawarar Kasar Sin Ta Gina Al’ummar Duniya Mai Mokamar Bai Daya
- Gwamna Dauda Lawal Ya Yi Wa Matar Da ‘Yan Bindiga Suka Raba Da Muhallinta Shatara Ta Arziki
“ Yayin da ake ci gaba da fuskantar al’amarin na garkuwa da ‘yanmakaranta wanda kuma hakan ya nuna gazawa ta gwamnati wajen ceto yawancin ‘yan matan na Chibok daga wurin wadanda suka yi garkuwa da su, ana cikin hakan ne kuma sai ga maganar na ‘yan makarantar Dapchi wani abin ban takaici bayan an dauke sum ranar da za a maido dasu su ‘yan ta’addar ne suka maido su makaranta aka ce kada a yi masu wani abu. Hakan abin ya ci gaba da faruwa dar ya kai Kankara, Kagara,Kaduna da Kangebe, zuwa Yawurin Kebbi daga nan sai can sai dai fatar Allah ya kara kiyaye mu gaba daya.
Maganar awon gaba na’yanmata 46 da suke karatu a jami’ar tarayya ta Gusau wadanda ‘yan ta’adda suka dauka wannan ba shi bane lokaci na farko, kusan wannan zuwan ‘yan ta’addar na uku ne a jami’ar gwamnatin tarayyar.
“Irin yadda aka ci mutunci wajen kai farmaki wurin kwanan dalibai mata yadda aka shiga wurin kwanan na su haka aka shiga wurin kwanan dalibai na makarantar Dapchi,wanda shi an samu rasa rayuka da raunuka masu muni wajen daukar ‘yan makaranta da basu ji basu gani ba,yawancinsu matasa ne masu shekara goma sha”.
Dattawan na Arewa sun ce abin akwai ban takaici na yadda ake yawan daukar dalibai ‘yan makaranta ana garkuwa dasu,wannan aikata laifin ‘yanta’adda ne suke yin hakan saboda an samu rashin halin ko in kula na wasu jami’an tsaro da suke nunawa kan aikin nasu, irin hakan ne su ‘yan ta’addar suka yi amfani da damar da suka samu.
Sun ci gaba da bayanin “Abin yana daure mana kai,mu yadda da cewa lokacin da gwamnati take bugun kirjinta tana maganar ta sawo sabbi kayan fada har ma da jirage masu saukar angulu,wadanda aka samar masu da isassu,sai dai kash! rashin kishin kasa sai ga ‘yan ta’addar suna ta shige da fici suna abinda suka dama a Arewa babu mai ce masu ko uffan.
“’Yan Nijeriya baki daya da al’ummar Arewa shekarubn da suka gabata rayuwarsu da harkokin kasuwancinsu na yau da kullun al’amarin tabarbarewar tsaro da ya shafi amfani da tsattauran ra’ayin addini, ta’addanci, matsala tsakanin manoma da makiyaya,ga kuma garkuwa da al’umma kamar yadda kungiyar ta bayyana.
Kungiyar ta yi kira da gwamnatocin tarayya, Jihohi, kananan hukumomi da su hada kai wajen daukar dukkan matakin daya dace wajen tabbatar da samarwan al’ummarsu tsaro ta hanyar samar da wadanda za su sa ido kan al’amarin daya shafi tsaon al’umma a duk inda suke domin kulawa dasa ido kan al’amarin tsaron lafiya da dukiyar al’umma.