Gidan tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari da ke Daura a Jihar Katsina ya zama fadar ziyarar manyan ‘yan siyasar Nijeriya.
A wannan makon dai, tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa a karkashin tutar jam’iyyar PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar ya ziyarci Buhari a gidansa da ke Daura a Jihar Katsina, inda suka yi ganawar sirri tare da tsohon wamnan Jihar Sakkwato kuma sanata mai wakiltar Sakkwato ta kudu, Aminu Waziri Tambuwal.
- Kamfanin Kera Motoci Masu Amfani Da Lantarki Na Sin Ya Shiga Kasuwar Kenya
- Rasuwar Suruka: Gwamnoni Sun Kai Wa Shettima Ziyarar Ta’aziyya
Sai dai ba a samu cikakken bayani kan tattaunawar da fitattun ‘yan siyasar suka yi ba, amma wasu manazarta na ganin ziyarar a matsayin wata dabarar da Atiku ya dauka na tabbatar da samun nasara a zaben shugaban kasa a 2027.
Amma a wata sanarwa da ya fitar, mai bai wa Atiku shawara kan harkokin yada labarai, Mista Paul Ibe ya ce tsohon mataimakin shugaban kasar ya kai ziyarar jaje ne Jihar Katsina.
Sanarwar ta ce, “Tsohon mataimakin shugaban kasar Nijeriya kuma dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP a zaben shugaban a 2023, Atiku Abubakar ya jagoranci sauran masu ruwa da tsaki na jam’iyyar zuwa gidan tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Alhaji Lawan Kaita a Daura wajen kai gaisuwar ta’aziyyar mutuwa da aka yi wa iyalan.
“Ziyarar wacce ta samu kyakkyawar tarba ga Atiku a manyan garuruwan masarautar Daura, sannan tsohon mataimakin shugaban kasar ya kai irin wannan ziyarar ga Sarkin Daura, Alhaji Farouk Umar Farouk da tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari.
“Taron da Atiku Abubakar ya yi a Jihar Katsina, ci gaba ne da ziyarar ban girma da ya kai tun bayan kammala bukukuwan Sallah da kuma jajanta wa iyalan tsohon abokinsa, Malam Lawan Kaita,” in ji shi.
Sanarwarta kara da cewa Atiku ya kuma ziyarci Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumini Kabir Usman.
Kwanaki biyar kafin tafiyar tasa zuwa Daura, tsohon mataimakin shugaban kasa ya kai ziyara daban-daban ga tsaffin shugabannin sojoji, Ibrahim Badamasi Babangida da Abdulsalami Abubakar a gidajensu Minna a babban birnin Jihar Neja.
Wannan ita ce ziyara ta farko da Atiku ya yi wa Buhari tun bayan da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a zabukan 2019 da 2023 ya fice daga jam’iyyar APC.
An kuma bayyana ziyarar tsohon shugaban kasan a matsayin wani dabarar siyasa da Atiku ya dauka”, musamman a daidai lokacin da yake kokarin hadakar jam’iyyun adawa don kwace mulki a wurin jam’iyyar APC karkashin jagorancin Bola Ahmed Tinubu a 2027.
Yunkurin nasa ya kara daukar hankali a watan da ya gabata lokacin da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP a zaben bara, Peter Obi, ya kai masa ziyarar ban girma. Obi shi ne abokin takarar Atiku a zaben shugaban kasa na 2019 da suka fafata da Buhari. Bayan sa’o’i 24 da ziyarar da Atiku ya kai wa Buhari, shi ma tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasiru el-Rufai ya kai irin wannan ziyarar ga tsohon shugaban kasa a gidansa da ke Daura.
Kafin yanzu, gidajen tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo da tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Ibrahim Babangida da tsohon shugaban kasa, Abdulsalami Abubakar, ya kasance wurin da ‘yan siyasa ke tururun kai ziyara.
Sai dai gidan tsohon shugaban kasa Buhari da ke Daura na ci gaba da ganin shahararrun ‘yan siyasa, musamman daga yankin arewacin Nijeriya.
Haka kuma, shi ma tsohon gwamnan Jihar Borno, Sanata Ali Modu Sheriff yana daga cikin manyan ‘yan siyasan da suka kai wa tsohon shugaban kasa Buhari ziyara a gidansa da ke Daura.
Tsohon sanatan Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani, ya soki wannan ziyarar da ‘yan siyasar arewa suke kai wa tsohon shugaban kasa Buhari. Yana mai cewa wannan wani yunkuri ne da ‘yan siyasan arewa suke yi na shirin tunkude shugaban kasa, Bola Tinubu a 2027.