A kullum madatsa ‘Hackers’ suna bin hanyoyi daban-daban wajen ganin sun yi kutse a mutane. Kutsen kuwa ya hada da shafukan sada zumunta kuma har da asusun ajiya na Banki.
Wata hikimar da suke yi wajen yin datsa (Hacking) wadda ta yi kaurin suna a wannan lokacin da ake kira smishing ta sanya mutane da dama a halin ha’ula’i, duba da yadda ake yaudararsu don cutar da su.
Smishing wata dabarar kutse ce da ‘yan madatsa, wadanda aka fi sani da hackers su ke amfani da ita wajen yaudarar mutane. Suna amfani da wannan dabarar ne wajen yaudarar mutane ta hanyar tura musu sakonni ana tambayarsu game da wadansu bayanansu na sirri.
Irin wannan kutsen yana daga cikin ire-iren kutsen Social Engineering da ya addabi mutane. Don haka mutane da dama suna yawan korafe-korafe a kan yadda ake musu kutse ta hanyar shiga asusansu ba tare da saninsu ba.
Sai dai duk da haka, abin da ba a sani ba shi ne, mutanen ne da kansu ke bayar da bayanansu da hanunsu.
Hanya mafi sauki da madatsan kan bi wajen rudar mutane ita ce tura musu sakonni, musamman zuwa asusun sakonninsu (inbod) na waya da ke nuna kamar sakon yana da inganci, misali; sako daga 500, ko 424 ko makamancin haka. Wato dai wani code, wanda ke nuna cewa ba daga lambar waya bane, don kar a gane su.
Irin wadannan sakonnin suna tunzura mutum ya bayar da bayanansa na sirri, musamman idan aka dubi lambobin da aka yi amfani da su wajen tura sakonnin. Ta wannan hanyar mutum zai yi tunanin daga wani kamfani ne ake neman bayanansa.
Akwai wasu kalmomi da suke kamanceceniya da smishing, wadanda duk suka kasance ire-iren dabarar kutse Social Engineering kamar haka:
- Smishing — Tura sakonni zuwa asusun sakonnin waya don rudar da mutane tura bayanansu na sirri zuwa ga madațsa.
-  Phishing — Tura wa mutane likau, manhajoji ko sakonnin email don karbar wasu muhimman bayanansu na sirri.
- Bishing — Kiran mutane a waya ta hanyar bi da lallami da kalaman yaudara don damfararsu, musamman don samu bayanansu na sirri.
Ta Yaya Mutum Zai Kare Kansa?
- Kada a danna likau ko shafin yanar gizon da ba a yarda da su ba.
- Kada a mayar da martani ga sakon imel kin da ba a yarda da shi kuma ba a san wanda ya turo shi ba.
- Kada a kula da kiraye-kirayen wayoyin da ba a san su ba.
- A rinka kula da shafukan da ake ziyarta da tabbatar da sahihancinsu.
- Kada a sanya manhajar da ba a tabbatar da sahihancinta cikin na’ura ba.
- A kula da sakonni a cikin waya kuma kada a mayar da martani gare su.
Tabbas ya zama wajibi a kula da wadannan shawarwari don kada a yi nadama nan gaba, domin yanzu kutse ya zama ruwan dare a wannan zamanin.
Bugu da kari, a rinka kula da sakonnin da ake samu daga banki hakika ba kowane sako ba ne daga asusun banki, sau tari ana iya amfani da wasu dabaru don kutse cikin na’urori don tura wa mutane sakonnin bogi.