Wani rahoto da kafar yada labarai ta PRNigeria ta fitar ya nuna cewa hare-haren da ake kai wa al’ummar Chonoko a jihar Kebbi, da kuma al’ummar Kagara a jihar Neja sun taimaka matuka gaya wajen raguwar kwararrun likitocin kiwon lafiya, da ayyukan ilimi, da sauran ayyukan jin kai a jihohin.
Baya ga kalubalen rashin tsaro da ake fama da shi, rahoton ya yi nuni da cewa, rayuwa a sansanonin ‘yan gudun hijirar ta zama abu mai wahala, ganin yadda jama’a ke matukar bukatar manyan ababen more rayuwa na dan Adam kamar abinci, ruwa, matsuguni da dai sauransu. .
- Sojoji Sun Cafke ‘Yan Bindiga 7, Sun Kubutar Da Wasu Mutane
- Amurka Ce Ke Yi Wa Zaman Lafiya A Zirin Taiwan Barazana
Sai dai kafar yada labaran ta zargi masu ruwa da tsaki a jihar da yin sama da fadi da kayan agajin da Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) ta bayar ga al’ummomin da ba su da karfi.
Wakilin PRNigeria, Mukhtar Madobi ne, ya bayyana hakan a yayin wani taron bita na yini biyu a Abuja mai taken: ‘Yan Jarida na Jin kai don Ci gaban Tattalin Arziki’ a lokacin da yake gabatar da wani bincike kan halin jin kai da kuma halin da ‘yan gudun hijira ke ciki a jihohin Kebbi da Neja.
Ya yi nuni da cewa ilimi wani bangare ne mai matukar muhimmanci wanda shi ma yake fama da matsalar rashin tsaro.
Sakamakon binciken ya nuna cewa an rufe akasarin makarantu a kauyukan saboda fargabar hare-haren ‘yan bindiga.
“Manoma a wasu kauyukan da ke kusa da su sun koma biyan haraji ga ‘yan bindiga domin samun damar shiga gonakinsu da gudanar da ayyukan noma. Duk da haka, ayyukan noma sun ragu sosai ta yadda hakan ya haifar da karuwar matsalar karancin abinci.
“Yawancin makarantun kauyukan a rufe suke saboda fargabar hare-haren ‘yan bindiga, wanda hakan ya shafi fannin ilimi a yankin.”
Rahoton ya kara da cewa, “Yanzu haka harkar kiwon lafiya an mata kisan mummuke, saboda Babban Asibitin garin ba ya aiki yadda ya kamata saboda fargabar ‘yan bindiga.”
A halin da ake ciki, wasu asibitocin da ke cikin garuruwan an mayar da su sansanonin ‘yan gudun hijira inda ake kula da wadanda abin ya shafa.
Ya koka da yadda lamarin ya sa dalibai da dama daina zuwa makarantu, wanda hakan ya kara yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a yankin da ma kasar baki daya.