Connect with us

Ka San Jikinka

Yadda Jikin Mutum Ke Aiki (4)

Published

on

‘Yan uwa masu karatu Assalamu alaikum. Barkanmu da wannan lokaci, barkan mu da sake saduwa a wannan shafi mai ilmintarwa, da ke zayyano muku bayanai game da duniyar jikin dan adam, domin ku faidantu kuma ku ilmintu; ku san yadda jikinku ke aiki.

A makon da ya gabata, na kawo muhimman misalai game da ‘Kundin Tsarin AikinJiki’
Misalan da na kawo sun hadar da yadda dumamar jiki ke aiki, da yadda numfashi yake; da yadda yawan jini da ake bukata a jiki yake; da yadda harbawar zuciya take,da karfin gudun jini acikin hanyoyinsa; da yadda yawan sikarin dake cikin jini yake;da yanayin yadda ruwan jiki yake. A kusan kowanne misali, na fada cewa sauka daga ‘daidaitacen ma’aunin’ da Sarkin halittta ya samarwa wadannan abubuwa kan iya kawo tazgaro a yanayin aikin jikin dan adam
Yanzu zan dora akan ragowar misalan da ban kawo ba.
Sinadaran “hormones” wadanda na dan kawo bayaninsu a rubutun makonnin da su ka gabata su kanyi yawa a jikin dan adam ko kuma akasin hakan: wato su yi kadan. Kowanne daga cikin wadannan yanayi kan iya haifar da illa a jikin mutum. Misali akwai halitta da muke kira “thyroid gland”, wadda take zaune a wuyan mutum. Aikin wannan halitta shi ne samarwa tare da tsarto da sinadarin da ake kira “thyroid hormone”. Idan wannan halitta ta tsarto wannan sinari da yawa cikin jini, fiye da yadda jiki ke bukata, akwai abinda a ke kira da “Makoko” zai ya fitowa mutum.
Akwai kuma wani sinadarin da ake kira”growth hormone”, wato wanda ke kula da girma da bunkasar jikin dan adam. Idan aka zubo shi da yawa a jiki, sai yaro ko yarinya suyi girman da ba a so, abinda muke kira da “gigantism”. Idan kuma ba a zubo isasshen ruwan sinadarin ba a lokacin shekarun girma, yaro zai iya gamuwa da ‘wadantaka’ ko kuma “dwarfism” a turance.
Sinadaran da ke cikin ruwan jiki irinsu gishiri, tama, karfe, alminiyom, da kalsiyom, da sauransu, su ma a aune suke. Kowanne akwai gwargwadon kimarsa a cikin ruwan jiki, kuma ba a so ya ketare ko kuma ya gaza wannan gwargwado. Duk wani sauyi da zai takali wannan gwargwado na wani saindari ko kuma wasu sinadarai dake cikin ruwan jiki, kuma a dauki tsawon lokaci ba tare da an shawo kan matsalar ba; wato mayar da wannan sindari kan matsayinsa, to hakika hakan kan taba lafiyar jiki.
Wadannan misalai da na kawo kadan ne daga cikin abubuwan da Sarkin Halitta ya tsara musu kima daidaitacciya a jikin dan adam. Wannan ya na kara tabbatar da gaskiyar ayar da Sarkin ya ke cewa: “Lallai mun halicci dan adam a sura mafi kyawun tsayuwa.”
Sauka daga wannan daidaitaccen geji da Rabbul izzati yayi wa wadannan halittu ko kuma sassa shi ne ke sanya dan adam rashin lafiya. Idan kuma sauyin da aka samu yayi tsanani ko kuma ya dauki tsawon lokaci ba tare da an gyara shi ba, mutum zai iya cewa : “ga garinku nan”.
Babban aikin likita shi ne yin iya kokarinta/kokarinsa na ganin cewa an mayar da duk wani sinadari, ko wata gaba, ko wani sashe izuwa asalin tsari da kima da Ubangijin halitta Ya samar masa; kuma jikina da naka, aikin da su ke yi kenan kulla yaumin ba dare ba rana, ba tare da mun sani ba. Idan sauyin da aka samu ya kasa gyaruwa ta hanyar cibiyoyin da kula tsare-tsare da gudanawar jikin dan adam, to akwai bukatar a bashi ko a bata magani domin shawo kan matsalar.
A duk lokacin da mutum ya ci abinci, to jininsa ko jininta zai hauhawa kadan. Kamar yadda na fada, akwai tsare-tsare a kasa wadanda za su tabbatar da cewa jinin ya dawo izuwa daidaitaccen ma’auninsa bayan lokaci takaitacce. Hauhawar jini (na dan wani lokaci) kan faru a lokutan da mutum ya ji tsoro, ko ya razana, ko ya fusata, ko yake yin wani aikin karfi, ko lokacin motsa jiki, ko lokacin jima’i. Amma bayan takaitacce lokaci, karfin gudun jinin zai koma daidai, biyo bayan aikin wadancan tsare-tsare da ke aiki ko yaushe.
Abin fahimta a dunkule a nan shi ne, muhimman sauye-sauyen da jikin dan adam ke samu sun kasu kaso biyu ne: Na farko shi ne sauyi mai kawo RAGUWAR wani abu, ko wani aiki, ko wani sinadari, DA kuma sauyi mai kawo DAdUWAR wani abu, ko wani aiki, ko wani sinadari.
Amma akwai wani sauyin wanda ke faruwa saboda gurbacewar wani aiki ko wata gaba ko wani sinadari. Ko kuma sauyawar wata halitta daga zubinta na asali izuwa wani zubin.
Wadancan tsare-tsare da Sarkin halitta ya tanada domin su kula da duk wani sauyi da aka samu, su na bin sigogin aiki guda biyu:
1. Akwai mai amincewa da zarcewar da sauyin da aka samu;
2. Akwai mai dakile cigaban sauyin da aka samu.
Na fada cewa jikin dan adam ya fi bin sigar dakile ko dankwafe sauyin da aka samu; abinda muke kira da “negatibe feedback mechanism”. Sai dai kuma a wasu daidaikun lokuta, jikin mutum ya na bin sigar amincewa ko yarda da zarcewar sauyin da aka samu “positibe feedback mechanism” a lokutan da jiki ke bukatar daukar matakin gaggawa wato “emergency” domin ceto rayuwa daga garari.
Tun da a baya na dauki lokaci wajen bayyana misalan abubuwan da ke faruwa a jiki, kafin jiki ya tantance wane tsari ne yafi dacewa da wannan sauyi, yanzu lokaci yayi da zan fadada bayani akan wadannan tsare-tsare guda biyu da kuma misalan yanayin da suke faruwa.
Zan fara ne da sigar aiki da ke dakile cigaban sauyin da aka samu wato “negatibe feedback”.
1. Daidaituwar dumamar Jiki.
Shin ko kunsan cewa jikin dan adam kamar wani ‘inji’ ne wanda ke motsawa, a ke yi masa sabis, garanbawul, da juye kamar yadda a ke yi wa abin hawa irinsu babur da Mota? Idan kukayi nazari, za ku gasgata batu na. Idan kun lura da kyau, duk wani inji da yake aiki, ya kan dauki zafi bayan ya dauki wani lokaci ya na aiki. To, tun da jikin dan adam kullum cikin aiki yake, matukar ya na da rai, ashe ba za a raba shi da yin zafi ba. To amma wannan zafin ya na da daidaitaccen ma’auni kamar yadda na fada, wanda ya tsaya a 37 a ma’aunin Celsius ko kum 98.6 a ma’aunin Fahrenheit.
Bisa tsarin wannan siga, duk lokacin da dumin jiki yayi kasa da 37, to za a daga darajar dumin jikin har sai ta koma 37 din. Haka kuma idan sama yayi da 37,to za a dinga rage dumin jiki har sai ya dawo kan daidaitaccen ma’auninsa na 37.
Zafi ko dumin jikin dan adam kan yi kasa da 37 a lokacin da mutum ya tsinci kansa a muhallin da yake da sanyi.
Da zarar yayi kasa da 37 to sai cibiyar dake daidaita dumamar jiki da ke zaune a wata halitta da ake kira “hypothalamus” ta shirya gabbai masu kula da dumama jiki da kuma taskance zafinsa. Wannan cibiya mai daidaita dumin jiki wato “hypothalamus”, a cikin kwakwalwatake. Bayan daidaita dumin jiki, ta na kula da cin abinci, shan ruwa, da sha’awar jima’i.
A gefe guda kuwa, gabban da ke kula da dumamar jikin su ne fata, tsokar nama, da kuma jijiyoyin jini wato “blood bessels”
Idan da akwai wani topic da kike/kake so nayi rubutu a kai, to ku tura sakon kar-ta-kwana da sunan maudu’in zuwa lambar wayar da aka bayar.
‘Yan uwa, ku tara a mako mai zuwa da Yardar Sarkin halitta, domin ci gaba da kawo muku bayani akan yadda jikin dan adam ke aiki. Kafin nan nake cewa, ku huta lafiya.
Advertisement

labarai