Yadda Kanawa Suka Sha Tattaki Yayin Yajin Aikin ‘Yan Adaidaita Sahu

Daga Mustapha Ibrahim Kano

 

Bayan yajin aikin matuka babura mai kafa uku wanda aka fi sani adaidaita sahu a Kano, LEADERSHIP HAUSA ta shiga lungu da sako don jin ta bakin masu ruwa tsaki a yajin aikin, inda suka bayyana ra’a’yoyinsu ko fahimtarsu a kan lamari duk da wasu da yawa sun hana a bayyana sunansu a wannan rahoto na musamman.

Wasu direbobin tasi sun ce, sun farfado daga kanshin mutuwa ko suma da suka yi da sanadiyyar yawan matuka adaidaita sahu a Kano, domin haka wannan yajin aikin na ‘yan adaidaita sahu ya sa sun farfado da aikinsu.

Wani direban tasi mai suna Malam Abdullahi ya ce wannan yajin aikin abin takaici ne kuma Allah ya sauwake ya kawo mafita.

Su kuma direbobin bas sun ce, “Yajin aikin nan ya sa mun dawo da aiki cikin gari dan taimaka wa jama’ar Kano. Dama kwazzabar ma’aikatan kan hanya na kudin tikiti da karban na goro ne ya hana mu aiki a cikin birni muke fita kayuka, amma yanzu mun dawo kuma mun kara yawan ma’aikata maimakon mu wuni mu biyu muna aiki, yanzu mutum hudu ne ke aiki a Bas guda, biyu da safe biyu da yamma.

Shi kuwa Direktan Tsare-tsare da Kididdiga na Hukumar Sufuri   na Kano (Kano Line), Abdullahi Babangida ya shaida wa manema labarai a madadin shugaban Hukumar, Hon. M.D Bashir Nasiru Aliko Koki cewa motoci 60 suka fito da su kan titi shida na Kano a rana ta biyu da yajin aikin, domin aikin cikin gari wanda aka fi sani da Jakara Kasuwa da ke daukar mutane Dawanau zuwa Bata, Na’ibawa zuwa Bata, Zoo Road zuwa Bata, Hotoro zuwa Bata, ‘Yan Kaba zuwa Bata, Birigade zuwa Bata, kuma kudin sufurin baya wuce naira 50 zuwa 100 a dogon zango.

Ya kara da cewa za su kara yawansu indai yajin aikin ba a janye ba, kuma yanzu haka Gwamnatin Kano na da shirin samar da hukumar sufurin cikin birni zalla. Sai dai kuma ya ce suna bukatar karin motoci a Kano Line daga Gwamnatin Kano.

A ra’ayoyin mutane na ganin cewa motocin sun yi kadan.

Wakilin mu ya ruwaito mana cewa, Kano Line na fuskantar karancin motoci mallakarta kamar yadda wata majiya ta tsegunta mana.

Wasu matuka adaidaita sahu sun ce suna nan kan bakansu na yajin aiki. Sun ce za su iya wata guda suna yajin aiki, domin haka suna nan ba gudu ba ja da baya har sai an janye kudin da aka dora mana.

Wani dan kasuwa a Kano mai suna Alhaji Bawa ya ce rashin ‘yan adaidaita sahu an zalunce su, domin ya yajin aikin ya mana tasgaro a kasuwancisu na yau da kullum, inda ya bukaci a sasanta wannan rigimar wajen kawo karshen yajin aikin nan.

Masu mashinan Lifan da Bespa da wasu masu motocin kansu da ba na haya ba sun rika daukar mutane musamman matafiya a kasa kyauta kama daga ‘yan makaranta, ‘yan kasuwa, ma’aikata da ma sauran baki matafiya da suka rasa abin hawa. Sun dai taimaka gaya wajen daukar mutane kyauta ba tare da ko kwabo ba da zaran sun gamsu da kamalarka da kuma bukatarka.

‘Yan acaba a Kano sun dawo da bara bana ta hanyar yin haya da mashin mai kafa biyu da gwamnati ta haramta yin hakan, amma saboda matsalar rashin abin hawa ya sa ‘yan acaba sun caba a Kano a wannan lokaci, inda suka tsauwala farashin daukar mutane dan kai su wuraren aiki ko kasuwanni. Wurin da ake biyan naira 50 ya koma 150 kamar yadda Malam Uzairu wani ma’aikacin kamfani ya koka da haka.

 

Shugaban hukumar kula da ababen hawa na Kano, Dakta Baffa Babba Dan Agundi ya ce wannan mataki na matuka adaidaita sahu ba zai amfane su ba za kuma su yi dana sani a kan yajin aiki, domin hukumarsa za ta dau mataki na inganta harkar sufuri wajen tabbatar da walwala da jin dadin al’umma bisa doka da oda.

Ya ce Gwamnatn Kano na shirin samar da sabuwar hanyar sufuri daidai da zamani a hirarasa da manema labarai.

Rahotanni dai sun tabbatar da cewa rundunar ‘yan sandan Kano ta kama wasu matasa 40 kan yunkurin kawo cikas ga wasu motoci da suka yi yunkurin taimaka wa jama’a a ranar farko, kamar yadda kakakin rundunar DSP. Abdullahi Haruna Kyawa ya bayya wa manema labarai a Kano.

Exit mobile version