A ranar 4 ga watan Maris na shekarar 2023 ne, aka bude taron majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin wato CPPCC a takaice sai kuma taron majalisar wakilan jama’a ta kasar Sin NPC da aka bude a ranar 5 ga watan Maris a nan birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin, inda majalisun suka tattauna batutuwan da suka shafi makomar kasar Sin baki daya har zuwa ranar 13 ga watan Maris na shekarar 2023.
Yayin da yake halartar taron tattaunawa da tawagar wakilan lardin Jiangsu, a taron farko na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin (NPC) karo na 14, wato majalisar kafa dokokin kasar, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya jaddada cewa, samun bunkasuwa mai inganci shi ne aiki na farko kuma mafi girma wajen gina kasa mai tsarin gurguzu ta zamani daga dukkan fannoni.
Xi ya ce, wajibi ne kasar Sin ta zurfafa yin gyare-gyare, da bude kofa, da sauya tsarin raya kasa, don hanzarta kafa cibiyoyi masu dorewa, da hanyoyin s**amun bunkasuwa mai inganci. Yana mai cewa, kara kaimi wajen samun dogaro da kai, da karfin gwiwa a fannin kimiyya da fasaha, ita ce hanyar da ya kamata kasar Sin ta bi wajen samun ci gaba mai inganci.
Xi ya jaddada cewa, kara karfin aikin noma, shi ne ginshikin babbar kasa mai bin tsarin gurguzu ta zamani, kuma inganta zamanantar da aikin gona, muhimmin abu ne wajen samun ci gaba mai inganci.
Shugaba Xi ya kuma bayyana cewa, farin ciki da jin dadin jama’a, shi ne babban burin sa kaimi ga samun ci gaba mai inganci. Yana kara da cewa, matakin farko na tabbatar da shugabanci da jin dadin jama’a, na da matukar muhimmanci ga muradun jama’a, kuma suna da muhimmanci wajen ciyar da wadata da gina rayuwa mai inganci.
Majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa (CPPCC), majalisa ce da ta kunshi mambobi daga sassa daban-daban na kasar da suka hada da jam’iyyun siyasa, kungiyoyi da wakilai masu zaman kansu da sauransu.
Ita kuma majalisar wakilan jama’a wato NPC a takaice, majalisa ce da ake zaben wakilanta daga mazabun gundumomin kasar, yankuna masu cin gashin kansu, manyan biranen dake karkashin kulawar gwamnatin tsakiya, rundunar sojojin kasar da sauransu. Masana na bayyana cewa, kamar yadda aka saba, a tarukan na bana ma, an tattauna muhimman batutuwa kamar shirin raya kasa na shekarar 2023 na bunkasa tattalin arziki, da matakan inganta rayuwar al’umma da, manufofin diflomasiyar kasar Sin, da sauran muhimman batutuwa da suka shafi kasar Sin har ma da matakan samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya baki.
Tsarin majalisar wakilan jama’ar kasa, babban tsarin siyasa ne na kasar Sin. Majalisar wakilan jama’ar kasa, ita ce hukumar koli ta kasa, kuma ita ce take da ikon kafa dokoki da tsai da kuduri kan manyan batutuwan da suka shafi harkokin siyasar kasa. Babban ikon majalisar wakilan jama’ar kasa, shi ne gyara tsarin mulki da duba aikin aiwatar da tsarin mulki da kafa da gyara dokoki na harkokin jama’a da hukumomin kasa, da dubawa da zartas da shirin bunkasa tattalin arzikin kasa da zaman al’umma, da yadda aka aiwatar da su da ba da rahoto kan kasafin kudi na kasa, da yadda aka aiwatar da shi, da amincewa da tsarin larduna da jihohi masu ikon tafiyar da harkokin kansu da birane da tsai da tsarin jihohin musamman na tabbatar da zaman lafiya da zabar shugabannin hukumar ikon koli na kasa, wato zabar mambobin zaunannen kwamiti na majalisar wakilan jama’ar kasa da zabar shugaban kasa da mataimakinsa da nada firaminista na majalisar gudanarwa da sauran mambobi.
Sauran sun hada da zabar shugaban kwamitin koli na soja da sauran mambobi, zabar shugaban babban kotun al’umma da shugaban ofishin binciken shari’a, kuma majalisar wakilan jama’a ce take da ikon tube wadannan mutane daga kan mukamansu.
Majalisar wakilan jama’a tana da wa’adi ne na shekaru 5, kuma ta kan yi taro a kowace shekara. A lokacin da majalisar wakilan jama’a take a rufe, zaunannen kwamiti shi ne zai aiwatar da ikon koli. Zaunannen kwamiti na majalisar wakilan jama’ar kasa, ya kunshi shugaban zaunannen kwamiti da mataimakinsa da babban sakatare da mambobinsa.
Dokokin kasar Sin sun kunshi dokokin da majalisar wakilan kasa da zaunannen kwamitinta suka kafa, da dokokin da majalisar gudanarwa da ma’aikatunta suka kafa, da dokoki na wuri wuri da na jihohi masu ikon kai na kananan kabilu da dokoki na jihohin musamman na tattalin arziki da jihohin musamman.
Ita kuma majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama’ar kasar Sin, muhimmiyar hukuma ce ta yin shawarwarin siyasa da ke karkashin shugabancin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, kana muhimmiyar hanya ta yada tsarin gurguzu a cikin harkokin siyasa na kasar Sin. Hadin kai da demokuradiya, su ne manyan batutuwa biyu na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa.
Majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama’ar kasar Sin, tana kunshe da ‘yan jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin da wadanda ba ‘yan jam’iyya ba, da wakilan rukunonin jama’a da kananan kabilu da na da’irori daban daban, da wakilai na ‘yan uwan mazauna yankin musamman ta Hong Kong da Macao da Taiwan da Sinawa ’yan kaka gida da mutane na musamman da aka gayyace su, tsawon wa’adin wakilan wannan majalisa shi ne shekaru 5.
Babban aikin kwamitin kasa da sassan majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta al’ummar kasar Sin, shi ne yin shawarwari kan harkokin siyasa.
Abin da ake nufi da shawarwarin siyasa, shi ne tattaunawa kafin kasa da sassan kasar Sin su tsai da manufa kan muhimman batutuwan siyasa da tattalin arziki da al’adu da zaman tarayya. Kwamitin kasa da na wurare na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama’ar kasar Sin, za su iya shirya taruruka don yin shawarwari bisa shawarar jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin da zaunannen kwamiti na majalisar wakilan jama’a da gwamnatin jama’a da jam’iyyu da kungiyoyin jama’a, kuma za su iya ba da shawara ga wadannan hukumomi da su gabatar da muhimman batutuwa don a tattauna a kai.
Nazartar tsarin demokuradiya, shi ne duba yadda ake aiwatar da tsarin mulki da dokoki da muhimman manufofi da ka’idoji da aikin ma’aikatun gwamnati da ma’aikatansu, za ta iya duba su ta hanyar ba da shawara da nufin yin gyara.
Shiga harkokin siyasa shi ne binciken muhimman batutuwan da ke cikin siyasa da tattalin arziki, da al’adu da zaman al’umma da batutuwan da ke jawo hankulan jama’a, don bayyana ra’ayoyin jama’a da yin shawarwari. Suna kuma gabatar da ra’ayoyi da shawarwarinsu ga jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin da ma’aikatun gwamnati ta hanyar ba da rahoton bincike da ba da shawara da shirye-shirye.
A watan Satumba na shekara ta 1949, cikakken zama na farko na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama’ar kasar Sin ta wakilci iko na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin, da burin jama’ar kasa, da sanar da kafuwar jamhuriyar jama’ar kasar Sin, ta kuma yi tasiri a tarihi. Bayan da aka kira zaman majalisar wakilan jama’ar kasa na farko a shekara ta 1954, majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama’a, ta daina wakiltar ikon majalisar wakilan jama’a, amma ta ci gaba da zama wata babbar kungiyar kasar Sin ta kishin kasa da hada kai, kuma ta yi ayyuka masu dimbin yawa a cikin harkokin kasa da zaman al’umma da harkokin sada zumunta da kasashen waje, ta kuma ba da muhimmin taimako.
Idan ba a manta ba, a yayin zaman majalisar na baya ne, aka yiwa tsarin zaben yankin musamman na Hong Kong gyaran fuska, ta yadda a wannan karo, aka zartar da hukunci cewa, ’yan kishi kasa ne kadai za su gudanar da harkokin zaben yankin, a cewarsu, ta haka ne yankin da mazaunansa za su samu zaman lafiya da ci gaba da ma kyakkyawar makoma, baya ga tabbatar da dorewar manufar nan ta “kasa daya, amma tsarin mulki iri biyu” da ake bi a yankin.
Yanzu haka, zaman majalisar wakilan ya amince da kaddamar da shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar na 14 a kasar Sin a bana, inda aka fara kokarin gina wata kasa ta zamani mai bin tsarin siyasa na gurguzu. A wannan lokaci na musamman, tarukan majalisun dokokin kasar dake gudana sun janyo hankalin al’ummar duniya. A yayin tarukan, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci zama da wasu tawagogin wakilan jama’a, da ’yan majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa, don tattauna manufar raya kasa, musamman ma yadda za a tabbatar da ci gaban tattalin arziki mai inganci don amfanin jama’a.
Wadannan muhimman taruka, tamkar alkibla ce dake haska manufofin kasar Sin dake jawo hankalin kasa da kasa, kana muhimmiyar dama ce ga kasashen duniya, don su kalli yadda kasar take aiwatar da tsarin demokuradiyya. A yayin tarukan biyu na bana, wakilan jama’ar kasar Sin da yawansu ya tasam ma dubu 3 gami da mambobin majalisar CPPCC sama da dubu 2 da suka hallara a Beijing, fadar mulkin kasar Sin, sun tattauna kan wasu muhimman daftarori gami da shirye-shiryen da suka shafi ci gaban tattalin arziki da rayuwar al’ummar kasar Sin nan da shekaru 5 ko fiye dake tafe, al’amarin da ya sake bayyana tsarin demokuradiyya mai inganci na kasar.
Duk mai bibiyar wadannan taruka zai fahinci cewa, siyasar demokuradiyya irin ta gurguzu kuma mai salon musamman na kasar Sin, tana taka rawa sosai wajen zamanantar da tsarin tafiyar da harkokin mulki a kasar.
Wakilai gami da mambobin da suka wakilci miliyoyin al’ummun kasar Sinawa, sun hada da jami’an gwamnati, da shugabannin kamfanoni, da mutane daga bangarorin kimiyya da fasaha da ilimi, da kuma ma’aikata da manoma daga kananan hukumomi, al’amarin da ya tabbatar da cewa, abubuwan da jama’a daga matakai daban-daban suka mai da hankali a kai, za a iya kai su wurin da ake tattaunawa wato wajen tarukan biyu, ta yadda zai yi tasiri gami da taimakawa tsara manufofin kasar.
Duniya na mamakin yadda kasar Sin ta iya yin wasu abubuwan al’ajabi masu muhimmanci, kamar kawar da talauci a cikin kasar, da saurin ci gaban tattalin arziki gami da zaman lafiya mai dorewa, tsarin demokiradiya da ya shafi al’umma baki daya ta gurguzu mai salon musamman ta kasar Sin, ta amsa tambayoyin da jama’a suka dade suna yi, kan abubuwan dake faruwa a kasar Sin mai yawan al’umma biliyan 1 da miliyan 400. (Ibrahim Yaya)