Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta tabbatar da cewa dan wasanta, Vinicius Junior zai yi jinyar mako shida sakamakon raunin da ya ji a kafarsa kuma likitoci suka yi masa tiyata.
Real Madrid ta tabbatar da cewar dan kwallon tawagar ta Brazil ya ji rauni a wasan Real Madrid din da kungiyar kwallon kafa ta da Celta Vigo ranar Juma’ar da ta gabata, wasan da Real Madrid ta samu nasara da ci 1-0 a gasar La Liga, kuma kungiyar ta lashe dukkan wasanni uku da ta fara kakar bana.
- Ana Zura Ido Kan Yadda Amurka Za Ta Ki Raba-gari Da Kasar Sin
- Yau Za’a Raba Jadwalin Kofin Zakarun Turai: Abinda Yakamata Ku SaniÂ
Dan wasan mai shekara 23 ba zai murmure ba kafin Champions League da za a fara a ranar 19 ga watan Satumba hakan yana nufin ba zai yi wa Real Madrid wasan La Liga da yawa ba, ciki har da na karawa da Real Sociedad da na hamayya da Atletico Madrid.
Rahoton da jaridun Sifaniya suka wallafa ya ce dan wasan zai yi jinyar tsakanin wata daya zuwa mako shida. Sannan ba zai buga karawa hudu ba a babbar gasar ta Sifaniya da kuma wasa daya a gasar cin kofin Zakarun Turai da za’a fara a watan gobe, kamar yadda hukumar kwallon kafa ta Nahiyar Turai ta tsara.