Wata mata mai juna biyu, Mista Mary Barka ta rasa ranta lokacin da masu garkuwa da mutane rike da bindigogi suka yi wa kauyen Pelachiroma da ke karamar hukumar Hawul a Jihar Borno kawanya.
Tuni dai shugaban kungiyar sa-kai, Mohammed Shawulu Yohanna ya samu nasarar damke wadanda ake zargi kuma ya hannanta su ga DPO na Hawul, Habila Lemaka.
Da yake ji wa manema labarai karin haske, Yohanna ya bayyana cewa an kai rahoton lamarin ofishin ‘yansanda a kwanin bayana lokacin da maharan suka yi yunkurin yin garkuwa da mutane a kauyen, amma ba su sami nasara ba.
Ya ce matan mai juna biyu, Mary Barka ta rasa ranta ne lokacin da maharan ke yunkurin yin garkuwa da maigidanta.
“Kauyen Pelachiroma yana cikin karamar hukumar Hawul ne wanda ‘yan bindiga suka addaba da farmaki a ko da yaushe. Lokacin da muka samu lafarin faruwar lamarin, nan take jami’aina suka dira kauyen tare da yin nasarar damke mutum huda da ake zargin sun yi yunkurin yin garkuwa da Mista Barka Paul Sawa, saboda ya ba su dabbobinsa su yi masa kiwo. Abun takaici dai shi ne, wadanda ake zargin sun yi nasarar halaka matar Sawa, Misis Mary Barka Paul Sawa da ke dauke da juna biyu.
“Wadanda ake zargin duka su hudun sun amsa laifinsu lokacin da muka mika su ga DPO na Hawul, Habila Lemaka. Ana sa ran za a mika su ga rundunar ‘yansandar Jihar Borno domin gudanar da cikakken bincike tare da gurfanar da su a gaban kuliya,” in ji Yohanna.