A yau canjin yanayin wannan zamanin ya zo wa da mata wani sabon salo da yadda suke daukan ‘yara domin taya su aiki a gida.
Wasu su kan sakar wa mai aiki ragamar aikin gida, har ya kai ga basu koya wa ‘ya’yansu mata girki domin wasu ana yin aurensu basu iya girki ba. Ko me za ku ce akan hakan? Shafin Taskira shafi ne da ya saba zakolo muku batutuwa daban-daban wadanda suka shafi al’umma. Tsokacimmu na yau zai yi doba ne game da yadda ake samu, ana auran yara mata basu iya Girki ba:
Usman Sani
Gaskiya wannan batu yana da muhimmanci sosai. Yanzu zamanin ya canza, kuma yawancin iyaye suna daukar ma’aikata don su taimaka a ayyukan gida. Wannan ba matsala bace idan dai iyayen suna koyar da ’ya’yansu abubuwan da suka kamata, musamman girki.
Amma idan aka bar wa mai’aikata duk aikin gida, kuma iyaye ba su ba wa ’ya’yan nasu lokaci don koya musu girki ba, lamarin zai iya zama matsala. A lokacin aure, wasu matan za su fuskanci kalubale saboda ba su da gogewa.
Ina ganin wajibi ne iyaye su rika koya wa ’ya’yansu mata abubuwan da suka dace, ko da kuwa akwai ma’aikata a gida. Wannan zai taimaka musu su zama masu cikakkiyar basira da iya kula da gida a gaba. Wannan kuma ba zai hana daukar ma’aikata ba, amma ba dole a jingina komai a kansu ba.
Khadija Abdullahi
To gaskiya rashin iya girki ga mace ba karamar matsala bace, saboda bai kamata ace tunda aka haifeki har kika taso koka girma ace baki iya girki ba wannan gaskiya abun kunya ne.
Ya kamata ace iyaye su dage, suyi iya kokarinsu danganin sun koyawa yaransu girki, tun yarinya na karama yakamata afara koyamata ahankali ahankali hatta girma, kafin yarinya ta girma sai ki ga ta iya aikinta. Amma da zarar annuna wa yarinya so an bar ta ba a koya mata komai ba haka za ta girma ba ta iya komai ba, kuma ta zo ta wahala daga baya tun da dole sai ta yi, ba za a tattaba ta yi aure ba, sannan ba ka san wanda za ta aura ba ya yanayin halinsa yake, wani komai halinsa ba ya son mai aiki ya fi son matarsa ta yi masa girki da kanta.
Shawara ga iyaye mata mu cire son ‘ya’yanmu, mu koya musu girki kala-kala, duk inda za su shiga ba za su ji kunya ba saboda sun san sun iya komai, amma idan basu iya ba sai ki ga su kansu suna jin kunyar shiga mutane. Ki koya wa ‘ya’yanki aiki wannan shi ne gata. Allah ya sa mu dace.
Fa’iza Musa
To ni a ganina gaskiya ka koyawa ‘ya’yanka mata aikin gida shi ne gata, ba wai ka bar su sakaka ba komai a ce mai aiki ce za ta yi gaskiya wannan ba daidai ba ne, ba kuma so bane, ni ina ganin ma cutarsu kake. Ya kamata iyaye su koyawa ‘ya’yansu aikin gida ba wai girki kadai ba komai na gida yadda kyau yarinya mace ta iya kome na gida.
Sakarwa mai aiki ragamar gida ba kya koyawa ‘ya’yanki aiki ba wannan gaskiya ba karamin cutar kai bane.
Wai sai ki ga sai za a yi auren yarinya sannan ne za a kai ta wajen koyon girki a biya kudi mai yawa, wai a wannan lokacin ne za ta koyi duk wani girki, ai wannan lokacin ya yi kankanta, sannan kuma ko ta ko ya iyakarta ta yi na doki, ba za ta iya dorewa ba daga baya ta watsar tun da ba ta saba ba, ba lallai ne ta iya dorewa ba, a zo kuma a shiga wani yanayi. Allah ya ganar da mu.