Yanzu haka rahotanni sun nuna irin yadda mata wani lokaci har da maza da ke ta shige da fice tsakanin Nijar da Nijeriya, wanda ake ganin kasashe guda biyu dangantaka ta yi tsami a tsakaninsu, domin neman magani a asibitoci mallakar gwamnatocin Nijeriya.
A wata ziyara ta gani da ido da wakilan kafafen yada labarai da suka kai a garin Magama da ke cikin karamar hukumar Jibia, sun ganewa idanunsu yadda mata ke tuturuwa zuwa asibiti domin neman lafiya
- Abuubuwan Da Suka Fi Daukar Hankalin ‘Yan Nijeriya A 2024
- Kamfanin ‘Promasidor Nigeria’ Ya Kaddamar Da Sabuwar Garabasar ‘Onga Taste The Millions Promo’
Mafiyawan wadanda ake kawowa yara ne kanana da kuma mata masu juna biyu domin yin awo, wani lokaci kuma har haihuwa ana karba a wannan asibiti na Mgama da ke Jibia.
Rabi Sani da Hauwa Haruna da kuma Hassan Lawalli duk sun zo ne daga wasu kauyuka da ke cikin Nijar, amma suna makwabtaka da Nijeriya saboda haka suka ce zuwa asibitin Magama Jibia ya fi masu dauki da kuma kwanciyar hankali.
Hauwa ta shaida wa manema labarai cewa ta kawo danta da yake fama da kuraje da zazzabi, wanda kuma aka ba da magunguna da madara domin kula da yaronta.
Kazalika, Rabi da ta zo daga kauyen Mai Rage cikin Nijar ta bayyana irin yadda jami’an kiwon lafiya ke haba-haba da su idan sun zo neman lafiya.
Ta kara da cewa babban abin da ya sa suke zuwa Nijeriya maimakon su tsaya Nijar shi ne, yadda ba a nuna masu bambanci kuma ana wayar masu kai kan yadda za su kula da yaronsu idan sun koma gida.
Ita kuwa Hasana Lawalli cewa ta yi har mai ciki ta kawo kuma ta haihu a wannan asibiti daga bisani aka sallame su suka koma gida. Ta ce yau kuma gashi ta kawo diyata ita ma a duba ta.
Dahiru Magaji shi ne mai kula da wannan asibiti ta Magama Jibia ya yi karin haske kan yadda makwabtansu mutanen Nijar ke zuwa asibiti domin neman magani da kuma amsar sinadarin dan kauce wa kamuwa datamowa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp