Iyaye mata mata barkanmu da wannan lokaci. Kasancewar a yanzu muna fuskantar barazana daga bullar annobar sarkewar numfashi, da yawan mazaje na killace a gida.Yana da kyau mata su san hanyoyin da za su bi don su mori wannan lokaci da mazajensu.
A farko, yana da kyau mu koyi hakuri, mu kara hakuri a kan wanda muke dashi a baya. Sannan mu kara azama akan abubuwan da mukeyi na kyautatawa. Mu guji duk wani abu da zai jawo mana sabani da maigida a wannan lokaci, domin in kin bata masa ina zai je ya samu natsuwa? Sannan mu zama masu tattalin abin da muka tanada, kama daga abinci har zuwa kayyayakin amfani.
Yaranmu mu kula da tsabtarsu, karatunsu, har Allah ya kawo mana karshen al’amarin. Iyaye mata mu guji mayar da hankali a kan wayar maigida, musamman a lokacin da yake amsa waya ko yake rike da ita a hannunsa. Mu tuna akwai abokan kasuwanci, abokan hulda da sauransu. Mu kyautata musu zato a wannan lokaci domin ba kowanne amsa kira ba ne zai zama na ‘yanmata ko bazawarar maigida.
Mun sa ni a wannan lokaci magidanta na zaune a gida a takure saboda ba zirga-zirga, to iyaye mata mu yi kokarin sama musu yanayin farin ciki a wannan lokaci, ta yadda za su ji a zuciyarsu ashe ba abin da ya fi zama da iyali dadi.