Daga Khalid Idris Doya,
Ministar kula da harkokin mata a Nijeriya, Madam Pauline Tallen ta kamu da cutar murar mashako, wato cutar Korona.
Tallen ta bayyana wannan batun ne a wani jawabin da ta fitar a jiya Lahadi. Ta na mai shaida cewar ta amshi shawarar jami’an lafiya ne bayan da ta gana da wasu mutane da aka gano sun kamu da cutar Korona da har ta fara nunawa a jikinsu.
Jawabin nata na cewa, “Biyo bayan mu’amala da wasu daidaikun mutane da na yi wadanda suka kamu da korona; jami’an lafiya sun shawarce ni da na yi gwaji kana na illace kaina na ‘yan wasu kwanaki.
“Ina sanar da jama’a cewa bayan da aka yi min gwaji ni da iyalaina, sakamakon gwajina ya fito ya nuna cewa tabbas na kamu da cutar Korona, yayin da su kuma sauran iyalaina nasu sakamakon ya nuna cewa ba su kamu da cutar ba.
“A yanzu haka na shiga kulle domin jinyar cutar nan ta Korona tare da amsar magunguna. Don Allah ina rokon addu’o’inku, kuma ina rokonku da ku kasance masu yarda da ce Korona gaskiya ce, ku kula da matakan kariya daga kamuwa da wannan annobar.
“Ina rokonku da ku kula da kawukanku da na iyalanku tare da kasarmu,” a cewar Ministan.
Ministar ta yi fatan alkairi da addu’ar Allah kawo karshen wannan cutar ta Korona mai hanzarin yaduwa a tsakanin jama’a, inda ta hori ‘yan Nijeriya da su kasance masu bin matakan kariyan kai daga kamuwa da wannan cutar ta Korona.