Yadda Muka Sa Taimakon Al’umma Gaba A Gidauniyarmu Ta Bintalya – Hajiya Binta

Hajiya Binta

Hajiya Binta

Hajiya Binta Hamidu Haruna, ita ce shugabar Gidauniyar Bintalya, wacce aka fi sani da ‘Bintalya First Foundation’. Mata ce da ta yi fice wajen tallafa wa al’umma, da kuma kokari da wajen ilmantar da jama’a, musamman a fannin fasahar ilimin kwamfuta, wadda ta kwashe shekaru da dama tana yi, da kuma ganin an shawo kan tabarbarewar Ilimi, musamman a Arewacin kasar nan.

A cikin wannan tattaunawar, Hajiya Binta ta bayyana wa wakilinmu cewa tana ganin yana da muhimmanci a taimaka wa wadanda ba su da shi, musamman a wannan lokaci da ake fama da matsin tattali arziki. Wannan ne ya sa ta sadaukar da lokaci da dukiyarta wajen samar da bashi ga al’umma marasa karfi. Inda ta ce ta ware miliyoyin nairori domin wannan. Akwai muhimman bayanai a wannan hira, kamar yadda wakilinmu ya rubuto mana:

 

A kwanakin baya masu karatunmu sun taba karantawa inda ki ke ba da horo na harkar ilimin kwamfuta ga ’yan kasuwa don su samu damar shiga tsarin kasuwanci na zamani, za mu so mu ji ina aka kwana a wancan tsarin?

Wannan tsarin alhamdulillahi, don yanzu haka kowannen su yana amfani da wannnan ilimin da ya koya a wajenmu yana tafiyar da kasuwancinsa cikin tsari na yanar gizo, kuma kasuwancin yana tafiya yadda ya kamata.

 

Bayan wancan rukunin, an yi wa wasu rukunai daga baya ne ko kuma akwai shirin yi wa wasu yanzu?

Eh, akwai shirin yin wannan a nan gaba, amma akwai wanda mu ke yi yanzu, wanda ya shafi ilimi na kowa-da-kowa, inda muka kira duk wanda yake da sha’awar ya kara ilimi na kamfuta, kamar su, ‘web designing and Graphic design’, inda muka yanke shawarar daukar mutum dubu daya su samu wannan horo.

Bayan wannan, kamar yadda kika yi magana cewa ana neman karin buda kwakwalwa ne, mutanenmu musamman na Arewa, za ki ga ilimin kamfuta nan kadan kawai suka sani, dan na sharan fage kawai, shin akwai wani shirin da ki ke yi na buda kwakwalwar ‘yan Arewan don ba su horo?

Shi ne wanda na ke yi yanzu, wanda yanzu haka ma an fara ba su horon na ‘web designing and Graphic design’. Kuma a yin hakan ne muka fahimci cewa akwai yaran da sun yi karatun amma sun manta da shi, saboda rashin samun ita na’urar a hannu, don idan akwai na’urar ba za su manta da karatun ba, kuma a yanzu yadda zamani yake tafiya da ilimin kamputa, dole ne gwamnati ta yi wani abu akan wannan al’amari wanda kamputa ya yi karancin a hannun matasa, domin yin hakan zai taimaki matasan su wajen tafiyar da kasuwanci.

 

Wadanne hanyoyi ake bi wajen ba da wannan horon?

Mu a bangarenmu yanzu haka mun buda ajin horo, inda mu ke horar da kowa, namiji, mace, tsoho da tsohuwa ilmin kamputa, wanda a yanzu haka muna da akalla mutum dari biyar wadanda muka fara masu horon. Tabbas za mu ci gaba da yin wannan abu har illa-masha’a, kuma wannan abu kyauta ne kamar yadda muka ba sa yinsa, wanda mu ke ba wa al’umma tun shekaru Ashirin baya kuma har yanzu ba mu fasa ba.

 

Misali, yanzu wani matashi ya karanta wannan tattaunawa tamu, kawai a jarida ya gani, amma bai san yadda zai samu shiga ba, ya zai yi?

Wannan abu ne mai sauk, za ka nemi ofisoshina da na ke da su, ka je wajen ofoshin ka yi wa kanka rajista, domin duk wanda za ka tambaya ina ne ofishin gudauniyar Bintalya da ke jihar Kaduna, za a gaya maka. Ka ga kenan kawai zuwa za ka yi ka dauki fom ka cike, a duba lokacin da akwai sarara a ba ka, a ce ka dawo ka yi karatunka.

 

Duk wanda yake bibiyar shafukanki da kuma shafukan Gidauniyar Bintalya, zai ga ana bayar da tallafin kudade ga kungiyoyi da daidaikun jama’a. Mu fara da daidaikun jama’a, yaya tsarinku na ba daidaikun jama’a bashi yake?

To, Gidauniyar Bintaliya ce take bayar da wannan bashin, ba gwamnati ba, ba wani ba. Gidauniyar ‘Bintalya first foundation’ ce ke bayar da wannan tallafin da take ganin zai taimaki mutane matuka, taimakon nan na shafi al’umma wadanda suke da sha’awar yin sana’a, suke da sha’awar yin kasuwancin. Kuma su da yawa kafin fara wannan kasuwancin, mutane suna da bukatar wasu ‘yan kananan kudi ne wanda zai taimaka masu ba manyan kudi ba.

Saboda muna da wadanda kudade kalilan kawai suke nema su tada kansu, suna tada kansu kuma ba su bukatar wani abu kuma. Kuma daga nan wadansu za su zo su goyo a bayansu, wanda hakan ya sa muka fitar da tsare-tsarenmu na ba da bashi daga dubu ashirin, dubu hamsin har zuwa dubu dari, inda duk muna yin wannan ne don ba wa al’umma jari su je su juya kasuwancinsu su dawo da shi, wanda babu ruwa ko kalilan a cikinsa.

Idan suka juya kamar na wata uku, sai su dawo mana da shi a kasha-kashi duk wata, to ka ga duk wanda ya yi hakan idan ya dawo neman kari ai za mu bas hi, wanda ko duk ya ki dawowa da shi, dole za mu je mu karbo kudinmu a hannun shi mu dawo da shi, saboda muna da niyyar ba wa wani, ka ga don haka ai ba zau bar masa ba saboda ba kyauta bane, kawai mu mun ba shi ne ya taimaki kansa. Don haka muna fatan al’umma za su ba mu hadin kai wajen idan suka karba su dawo da shi, domin ci gaba da kawar da matsalolin da ke damun mutane.

Daga nan, sai muka zo muka fara ba da mai yawa kamar, Naira miliyan daya, wanda shi wannan yana da ruwa na kashi goma bisa dari. Shi ma wannan idan ka karba z aka rika dawowa da shi ne wata-wata zuwa wata shiga hark a gama biya.

Mun sanya ruwan ne saboda babu wanda zai dauki kudi mai yawa ya ba ka, ba tare da samun ko sisi ba. Har iya lau, ya zuwa yanzu, mun bayar da kudi akalla ya kai miliyan dari, kuma muna ci gaba da bayarwa.

Sannan kuma muna sa ran za mu ba da kamar Miliyan dari biyu a cikin jihar Kaduna da kewaye, daga kuma sai mu tafi sauran Jihohin Nijeriya su ma mu ba da rancen. Duk muna hakan ne don mu rika ta da al’umma wadanda ba su da karfi.

Wadanda ba su bukatar manyan kudi kamar dubu dari, akwai kuma kananan kudin da aka ware kamar dubu biyar zuwa dubu goma, hakan yasa muka shigo da kungiyoyi da unguwanni, da kungiyoyi masu zaman kansu wadanda aka sansu, masu taimako, mukan ba su wannan kudin domin su taya mu kaddamar da wannan taimako, domin su suka san irin al’ummar da ke bukatar irin wannan kudin, kuma za su koma masu sana’a na daidai wannan kudin, domin su yi kasuwancinsu.

 

Idan za ka ba mutum bashi dole sai ka sanya matakan tsaro wajen ganin wadannan kudin sun dawo, shin wadanne hanyoyi kuke bi?

Idan mutum ya rubuta ya karbi kudi, muna da wata tawaga da mu ke tura su suje wajen sana’ar ta ka, su tabbatar cewa abin da k ace z aka yi shi kake yi. Idan kuma ba ka taba yin sana’a ba ne, za mu tambaye ka wani sana’a za ka yi, domin a kowa ma ka irin sana’ar da kake sha’awa a sanya ka hanya. Don haka, idan wata daya ya yi ba mu ka saka kudi ba, za mu aika ma ka da sako cewa ko ka manta da kudinmu ne. Daga nan idan mun ji ka shiru kuma, za mu kara aika ma ka da sako na biyu, amma ba za mu maimaita na uku da kai ba. A mataki na uku sai dai mu aika ma ka da tawagarmu ta karban kudi.

 

To amma ba ku ganin cewa akwai wadanda za a iya ba bashi su gudu da kudin?

Duk inda ka ke sai an nemo ka, domin ba mu yarda ma mu ba ka bashi ba tun farko ba tare da Garanto wanda zai tsaya maka ba, ka ga idan mutum ya gudu ai za a kama garantonsa.

 

Sai batun kungiyoyi da kika tabo, misali yanzu idan wasu kungiyoyi suka karanta wannan tattaunawar, suna son zuwa su karbi wannan bashi, shin za su taho ne kawai su karba ko kuma akwai wasu hanyoyi da ake bi kafin haka?

Za su taho ofishinmu ne su yi rajista da mu, domin mu san ko su wane ne, daga nan sai mu yi bincike akansu mu ga cewa shin da gaske su ke suna son karbar bashi ne don taimakon mutanensu, ko akasin haka. Idan muka yi bincika muka ga cewa haka ne, to za mu ba ta, idan kuwa ba mu gamsu b, to za mu kira ta mu ce mun ji kaza, kaza da kaza, ya abin yake. Abin sai ka cancanta za mu ba ka.

Bugu da kari, rajistar ba wai kawai akan wannan bashin ba ne, saboda Gidauniyar Bintaliya tana rabon abinci, tufafi da kayan karatu. Ka ga irin wadanda abubuwa sai ka yi ragista da ita sannnan za ka samu, don ko a lokacin Babbar sallah ma mun yi rabon abinci, kuma kungiyoyin muka kira muka ba su kayan, domin su suka san masu bukata daga cikin mutanensu, don haka muka kira su domin su taya mu raba wa al’umma, wadanda ba su da karfi su yi hidimar Sallah. To ka ga idan ka yi rajista da Gidauniyar Bintalya kana da damar samun irin wadannan abubuwa idan suka zo kanka.

 

Mu koma baya kadan, kin yi maganar cewa yara da yawa sun yi karatun Kamfuta amma duk sun mata saboda rashin mallakar na’urar, shin wane abu ki ke yi wajen magance hakan?

A halin yanzu, wannan sabon ilimin na ‘web designing da Graphic design’ da muke da niyyar koyarwa ya yi karanci a Arewancin Nijeriya, saboda yanzu a ma’aikatu dole sai ka iya za a dauke aiki. Kuma duk wanda ya yi fice a horon da mu ke bayarwa, mu na ba shi kyautar na’urar.

 

Ba ku neman taimako daga wasu kungiyoyi ku gwamnati?

Eh gaskiya mun nema, mun rubuta wasiku zuwa ga nasatoci, ministoci da gwamnatocin Jihohi, muna gaya masu irin halin da ake ciki, amma babu wanda ya ce wani abu.

 

A karshe, wadanne shawarwari ki ke da shi ga al’umma, musamman a wannan mawuyancin halin da ake ciki?

Shawata ita ce, ina fatan ‘yan uwa na da al’umma su rika ba wa junansu hadin kai, don lokaci ya yi da yakamata idonsu ya bude, kasance suna gane masu sonsu, da makiyansu, ya kasance wanda yake son ya taimakesu su mara masa baya, sub a shi hadin kai, domin dukka duk taimakon kai ne. Idan aka cire bakin ciki, hassada da kiyayya aka ajiye su a gefe aka hada kai, duk za a kawar da matsaloli, kuma sai an yi hakuri al’amura suke tafiya daidai.

 

Kira ga ’yan siyasa da gwamnati fa?

Muna fatan gwamnati za ta sanya ido akan matsalolin da al’umma su ke ciki, kuma ta kasance tana da kunnen-ji, don sauraron al’umma da kuma jin matsalolin da suke ciki domin kawo agaji gare su. A karshe kuma ina fatan kasar mu ta zauna lafiya, duk wadannan fitintunu, Allah ya yi mana maganinsu.

 

Exit mobile version