Kwararru a fannin kiwon lafiya sun bayyana cewa an samu karin ‘yan Nijeriya da ke mutuwa sakamakon cututtuka irin su hawan jini da ciwon suga da cututtuka masu alaka da tamowa da kuma haduran akan tituna.
Sai dai an samu sabani kan abubuwan da suka haddasa yawan mace-macen da aka samu a bara, bayan da gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu ta fara daukar matakai kan tattalin arziki.
- Yadda Amfani Da Karen Mutum-mutumi Da Jiragen Ruwa Da Motoci Masu Sarrafa Kansu Ya Kara Fito Da Ci Gaban Fasahar Kasar Sin
- Yara Miliyan 1 Ke Mutuwa Duk Shekara A Farkon Watansu Na Haihuwa A Nijeriya – UNICEF
Sauye-sauyen tattalin arzikin da aka bayyana a matsayin wani abu mai matukar zafi, sun hada da cire tallafin man fetur da kuma faduwar darajar Naira, lamarin da ya yi sanadin tashin gwauron zabi na kayan abinci da sufuri da kuma harkokin kiwon lafiya.
Yayin da wasu daga cikin masanan ke dora alhakin yawan mace-macen da ake fama da su a kan tabarbarewar tattalin arzikin da ake fama da shi a kasar, wasu kuma na cewa ba shi da alaka da hakan.
Kwararrun, wadanda suka zanta da LEADERSHIP Sunday a jihohi 13 na tarayya, sun bayyana abubuwan, da suka hada da manyan asibitocin jami’an kiwon lafiya da na koyarwa da manyan asibitoci, kamar manyan daraktocin kiwon lafiya (CMDs), masu ba da shawara kan kiwon lafiya, masana abinci mai gina jiki, masu hada magunguna da masu kula da gawarwaki.
Binciken ya mayar da hankali kan gabadayan asibitocin koyarwa da na kiwon lafiya masu zaman kansu. Yawancin ma’aikatan da aka zaba suna aiki a wuraren da ke cikin manyan biranen jihohi da kananan garuruwa bisa dogaro da kayan aiki da kwarewa kan magance cututtuka daban-daban.
Daga cikin kwararrun akwai CMD na Asibitin Koyarwar Jami’ar Uyo (UUTH), Farfesa EmemAbasi Bassey; wani likita mai ba da shawara a Hukumar Kula da Asibitin Jihar Edo, Dakta Osagie Ebonwonyi; Babban Sakatare kuma babban daraktan kula da lafiya na asibitin tunawa da Sir Yahaya da ke Birnin Kebbi, Jihar Kebbi, Dr Abubakar Zaki; wata kwararriyar masaniyar abinci mai gina jiki mazauniyar Enugu, Misis Gladys Umeh, da wani likita, Dakta Jude Agbugba.
Sun ba da amsa game da tambayoyin da aka yi musu kan ko wasu ‘yan Nijeriya sun mutu tun bayan sauye-sauyen da gwamnatin yanzu ta bullo da su, wanda cututtuka suka yi sanadin mace-mace da kuma kula da gidajen gawarwakinsu.?
Yawancin jami’an sun ki bayyana adadin wadanda suka mutu a lokacin da ake yin wannan nazari.
Wasu sun ce irin wadannan alkaluma ba su dace a ambata su ga jama’a ba, yayin da wasu kuma suka nemi wakilanmu su rubuta wasiku na yau da kullum ga mahukuntan asibitocinsu ko kuma ma’aikatar lafiya.
Duk da haka, sun sun yi tarayya akan karuwar mace-macen da ‘yan Nijeriya ke yi a karkashin gwamnati mai ci.
A Jihar Akwa Ibom, bincike ya nuna an samu karuwar mace-mace a galibin manyan asibitoci da suka hada da UUTH, babban asibitin Anua, da wasu gidajen ajiyar gawa masu zaman kansu.
Ko da yake Farfesa Bassey ya lura cewa “babu wani asibiti a ko’ina a duniya da mutane ba sa mutuwa,” an gano cewa saboda kalubalen zamantakewa da tattalin arziki da ake fama da shi a Nijeriya, adadin wadanda suka mutu ya karu fiye da yadda aka saba a jihar.
Bassey ya ce kayayyakin aikin likitanci da suka hada da wuraren gadaje na dakunan gaggawa da sauran sassan, sun yi yawa. Ya koka da cewa galibin mace-macen na faruwa ne saboda yadda mutane ke kula da wasu cututtuka, ya kara da cewa saboda yanayin tattalin arziki wani lokaci ana kawo marasa lafiya asibiti a makare.
“Wasu daga cikinsu ana kawo su ba su da halin da za su biya kudin magani ko na gwaje-gwaje,” in ji shi. A cewarsa, rashin isassun kudade ya kawo cikas wajen gudanar da ayyuka masu inganci da fadada kayayyakin aikin likitanci da daukar kwararrun likitoci domin shawo kan kwararar marasa lafiya zuwa asibiti.
Yawancin wadanda suka mutu, in ji shi, majinyata da ke fama da matsalar ciwon koda, inda da yawa ba sa iya biyan kudin wankin mako-mako.
Ya bayyana cewa rashin wutar lantarki a matsayin babban kalubale da cibiyar da ke akan tsarin band ‘A’, sai dai akwai rashin isassun tsarin da gwamnatin tarayya da gwamnatocin Jihohi ke yi don tafiyar da asibitin.
A babban asibitin Anua, an ruwaito cewa, adadin wadanda suka mutu ya karu yayin da akasarin majinyatan da ke mutuwa a kullum saboda matsalar kudi; da yawa an ce suna amfani da ganyaye domin magani saboda rashin iya biyan kudin magani na yau da kullum a cibiyoyin kiwon lafiya.
“Muna daukar gawarwaki fiye da da, saboda wannan mawuyacin lokaci ya sa mutane suka kwashe aljihunsu har ta kai ga ba za su iya samun ingantacciyar maganin cutar da ke damunsu ba,” Tony Nsudo, wani ma’aikacin dakin ajiye gawa a wani wurin ajiye gawarwaki a Uyo, babban birnin jihar, ya shaida wa daya daga cikinsu. wakilanmu.
Afiong Emma, masani kan sinadarai da abinci mai gina jiki, ya zargi galibin mace-mace a kan rashin isasshen abinci mai kyau da aiki.
“A yanzu haka a yawancin gidaje, muna cika cikinmu da kowane irin abinci don mu koshi kawai ba tare da la’akari da wasu abinci suna dauke da guba a ciki ba,” ta bayyana.
Wata kwararre a fannin kiwon lafiya, kuma mai kula da abinci mai gina jiki, Misis Gladys Umeh, ta ce adadin wadanda suka mutu ya karu a ‘yan kwanakin nan sakamakon kuncin rayuwa da ake fama.
Baya ga mace-mace, Umeh ya bayyana cewa mutane da dama na fama da tabin hankali saboda wahala.
“Eh, mutane suna mutuwa tun lokacin da aka afka wadannan wahalhalu saboda ba sa cin abinci sosai dalilin rashin kudi. Don haka, lokacin da mutane ba samun abinci mai kyau, suna kamuwa da rashin lafiya a lokacin da ba su da kudin sayen magunguna,”in ji ta.
Umeh ya shawarci gwamnatoci da su kafa dokar ta-baci a fannin kiwon lafiya tare da samar da magunguna kyauta ga jama’a da kuma abincin da ‘yan kasa za su ci.
Wani ma’aikaci a dakin ajiye gawa na asibitin koyarwar gwamnatin tarayya da ke Owerri a Jihar Imo ya ce a kullum ana samun karuwar mace-mace a karkashin wannan gwamnati.
Wani likita, Dr. Jude Agbugba, ya ce ya sabawa ka’idojinsu na bayyana cututtukan da ke kashe mafi yawan ‘yan Nijeriya.
Ya, duk da haka, ya ce yawancin marasa lafiya suna mutuwa ne saboda cututtukan koda da bugawar zuciya.
A nasa gudunmuwar, Dr. Harold Onumo ya bayyana cewa halin da ake ciki na yawan mace-mace ya faru ne a gwamnatin yanzu kuma ana iya kwatanta shi a kan mummunan yanayin tattalin arziki da jama’a ke fuskanta.
Ya shawarci gwamnatin tarayya da ta nemo hanyar da za ta rage farashin man fetur, domin a cewarsa, “Duk kasashen da muke koyi da su suna da muhimman ababen more rayuwa, abubuwan kara kuzari da kuma tsare-tsare na jin dadin jama’arsu.
A Birnin Benin na Jihar Edo, ma’aikatan dake aiki a dakin ajiye gawa na Asibitin Kwararru na jihar sun ce galibin gawarwakin da ake kawowa mutanen na mutuwa ne sakamakon hadurra da cututtuka, kenan ba za a iya alakanta su da kuncin rayuwa kadai ba.
Wani ma’aikaci a asibitin koyarwa na jami’ar Benin da ya nemi a sakaya sunansa ya ce asibitin ya samu karin gawarwaki daga jihar da sauran jihohin da ke makwabtaka da shi, inda ya kara da cewa batun karin samun gawawarwaki yana faruwa ne a nan ko kuma can.
A martanin da ya mayar, wani likita mai ba da shawara a hukumar kula da asibitocin Jihar Edo, Dakta Osagie Ebonwonyi, ya bayyana cewa a gaskiya babu wani sahihin batu da ya nuna cewa mutane na mutuwa musamman saboda yunwa da wasu nau’o’in kuncin rayuwa da matsalar tattalin arziki ta janyo.
Ya ce irin wadannan rahotanni ko bincike na bukatar “nutsuwa wajen gudanar da bincike, tun kafin a zo da rahoton cewa yawan gawarwakin da ake ajiyewa ana iya danganta su da kuncin rayuwa.
“Irin wannan aikin na da matukar wahala wajen tabbatar da cewa mutane na mutuwa ne saboda matsalar tattalin arziki; yaya za ku yi, Mene ne alakar? Abin da kuke bukatar tambaya shi ne shin mutane suna mutuwa ne sakamakon yunwa, ko kuna bukatar nuna akwai yunwa a kasar,” in ji shi.
A wasu asibitocin gwamnati biyu da wakilinmu ya ziyarta a Garin Ilorin na Jihar Kwara, samun bayanai kan adadin wadanda suka mutu ya yi wuya, amma ma’aikatan dakuna gawarwakin da suka nemi a sakaya sunansu sun ce an samu karuwar gawarwakin da ake kai wa dakin ajiyar gawa daga wajen asibiti a kwanakin baya.
Wani babban ma’aikacin daya daga cikin asibitocin ya tabbatar da ikirarin ma’aikatan ddkin ajiye gawarwaki.
Da alama ana samun karuwar gawarwakin da ake kawowa daga waje zuwa dakin ajiyarsu na asibitin gwamnati tun bayan cire tallafin man fetur. Wannan na iya kasancewa gaskiya saboda karin mace-mace daga cututtukan da ke da alaka da talauci da karancin kudi da ke da alaka da rashin isa ga ingantaccen ayyuka na kiwon lafiya, ”in ji shi.
“Babbar illar cire tallafin man fetur ga majinyatan asibitoci a Ilorin, babban birnin Jihar Kwara, shi ne raguwar adadin masu kamuwa da cutar a kullum. Ko da a duk inda aka kawo irin wadannan lokuta a cikin cibiyoyin kiwon lafiya, koyaushe ana gabatar da su a makare. Ba za a iya rabuwa da wannan ci gaban na mace-mace ba daga hauhawar farashin magunguna da sauran kayan masarufi a asibiti ba, ”in ji shi.
A Jihar Neja, an samu karuwar mace-mace da ake dangantawa da ciwon zuciya.
An kuma gano cewa wasu daga cikin majinyatan suna jinyar rashin lafiyar da ke da alaka da ciwon zuciya,suna farawa ne da hawan jini, sannan bayu zuwa cututtuka masu tsanani wanda ke haifar da bugun zuciya ko bugun jini.
Yayin da wasu kwararrun likitoci a asibitocin gwamnati suka gwammace a sakaya sunansu, sun bayyana cewa, an gano cewa an samu karuwar masu fama da ciwon zuciya a babban asibitin Minna.
A jihar Kaduna, galibin majinyatan sun fuskantar wahalar biyan kudaden asibiti.
A ziyarar da aka kai wasu asibitocin gwamnatin Kaduna ta Kudu ta nuna cewa wasu majinyata asibitoci na bin su bashi yayin da suke kokawa kan halin da suke ciki.
A babban asibitin Sabon Tasha, da yawa daga cikin majinyatan sun koka da “basu da kudin da za su biya mu kudaden da muke bin su.”
Wani ma’aikacin babban asibitin Kakuri, mai suna Emma, ya ce duk da cewa an samu karuwar mace-mace, hakan ba wai kawai ya ta’allaka ga wahalar da ake ciki bane.
Daga bayanin da aka samu daga Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri (UMTH) an samu raguwar adadin mace-mace a cikin shekaru biyu da suka gabata idan aka kwatanta da na bana.
Misali, yayin da aka samu rasuwar mutum 1,167 asibitin cikin 2022 da mutuwar 1,062 a cikin 2023, adadin da ya kasance 873 na mutuwar mutane a cikin 2024.
Ga wuraren ajiye gawarwaki kuwa, kasancewar Jihar Borno da ke da rinjayen Musulmi, galibin wadanda suka mutu ana binne su nan take a makabartar kamar yadda Addinin Musulunci ya tanada.
A dakin ajiye gawa na asibitin Kwararru na Jihar Filato (PSSH), ba a yarda a ajiye gawarwaki a cikin dakin fiye da makonni biyu.
Wani ma’aikacin ajiye gawa na jami’an tsaro na PSSH da ya nemi a sakaya sunansa, saboda ba’a shi izinin yin magana ba, ya bayyana cewa galibin gawarwakin an same su ne sanadin hatsarin mota.
Asibitin koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa ya ki bayyana adadin gawarwakin da aka ajiye a dakin ajiyar gawa a cikin watanni 12 da suka gabata.
Kakakin asibitin ya ce yana bukatar amincewa daga CMD, Farfesa Yusuf Bara, kafin ya fitar da irin wadannan bayanai.
A jihar Abia, wani kwararre a fannin lafiya a wata cibiyar lafiya mai zaman kanta da ke titin Bende, a Umuahia babban birnin jihar, Jude Eke, ya bayyana damuwarsa kan halin da tattalin arzikin kasar ke ciki.
Ya tabbatar da cewa halin da tattalin arzikin kasar ke fama da shi na iya haifar da mummunar illa ga lafiyar jama’a, musamman wadanda ke da dimbin nauyin a harkar kudi.
Wani likita mai suna George Okere, ya ce gwamnati za ta iya shawo kan lamarin ta hanyar aiwatar da manufofi da tsare-tsare masu gamsar da mutane.
Sakatare na dindindin kuma babban daraktan lafiya na asibitin tunawa da Sir Yahaya da ke Birnin Kebbi, jihar Kebbi, Dakta Abubakar Zaki, ya tabbatar da cewa majinyata na mutuwa sakamakon hadurra da masu ciwon suga da kuma ciwon ciki.
Wani rukunin marasa lafiya da suke mutuwa, sau da yawa mata ne masu juna biyu da yara masu fama da zazzabin cizon sauro da Taifod.
Ba zan iya fadin ainihin adadin wadanda suka mutu tun farkon wahalar a yanzu ba saboda yawan adadin,” in ji shi.
A Cibiyar Kiwon Lafiya ta Kebbi, Kalgo, jami’in da ke kula da rajistar haihuwa da mutuwa, Malam Umar Abubakar, ya ce a wasu lokuta adadin mace-macen da ake samu a asibitin yana karuwa kuma yana raguwa, ya kara da cewa adadin yawan mace-macen da ake samu a asibitin ya kan yi yawa a lokacin damina da lokacin zafi, zazzabin cizon sauro da sankarau.
A bangaren Dakta Babatunde Kerim, wani masanin abinci mai gina jiki, cewa ya yi yawan mace-macen ba za a iya danganta shi da wahalhalun da ake ciki a yanzu ba, sai dai yanayin sakacin da mutane ke yi game da umarnin likitoci idan ba su da lafiya.
Ba a samu karuwar gawarwakin da aka ajiye a dakin ajiye gawa na asibitin Jihar Osun dake Asubiaro, Osogbo ba sakamakon karin farashin man fetur da gwamnatin tarayya ta yi.
Ko da yake mahukuntan asibitin sun hana LEADERSHIP Sunday samun damar gano gawarwakin da aka ajiye a dakin ajiyar gawa na asibitin jihar, Asubiaro, Osogbo kafin da kuma bayan karin farashin mai, wani ma’aikacin dakin ajiyar gawarwaki ya ce babu wani karin gawarwakin da aka shigar a ciki.
Sai dai wani ma’aikacin lafiya Dakta Wale Adisa da ya amsa tambayoyin wakilinmu inda ya ce an samu karin adadin mutanen da ke mutuwa sakamakon cutar hawan jini.
Ya yi nuni da cewa karin farashin man fetur ya yi tasiri a kowane fanni na kokarin dan’Adam, kuma hakan na iya yin illa ga lafiyar al’ummar kasa da kuma haifar da illa ga lafiya.
Ziyarar da aka kai sashen ajiye gawarwaki asibitin Kwararru na Abdullahi Wase da ke Kano (asibitin koyarwa na jihar) domin tantance adadin wadanda suka mutu a asibitin bai yi nasara ba, domin an mika wa wakilin sashen Serbicom Unit, inda jami’an suka ki bayyana komai.
Lokacin da aka tuntubi mataimakin babban daraktan kula da lafiya na asibitin, ya bukaci wata wasika daga hukumar ma’aikatar lafiya, da ke nuni da yanayin bayanan da ake nema.