Yadda Wasu ‘Yan Bindiga Suka Kashe AVM Mohammed Maisaka

Maisaka

A cikin daren ranar Talatar da ta gabata ne, wasu gungun mahara suka yi drar mikiya a gidan Air Bice-Marshal Mohammed Maisaka mai ritaya da ke Makarfi Road, Rigasa cikin garin Kaduna.

Majiyarmu da ta ziyarci gidan marigayin, da misalign karfe 1.00 nr a ranar Talata, ta shaida mana cewa, mutane da dama sun shuga damuwa tare nuna alhinin wannan babban rashi da aka yi.

“Makasan dai ba su karya kofar gidan ba, kamar yadda ake yada jita-jita. Sun shiga inda yara ke kwana inda suka fara tsorata wani babban sojan sama.”

Bayan ‘yan bindigar sun tabbatar da cewa, hankalin Maisaka ya tashi matuka, wanda kuma bai dade da dawo wa daga kasar waje ba don neman magani ba, sakamakon ciwon da yake  fama da shi na shanyerwar jiki, tun kusan shekara uku, wanda kuma ya fara samun sauki, kuma yana daki a lokacin da ‘yan bindigar suka fada cikin gida, da suka gano shi, nan take suka harbe shi, tare da wani mutum daya, dukkansu kuma sun mutu. Ganin yadda aka kashe, wannan soja dama ‘yar uwarsa na gidan sai ta fito da ce da makasan tana rokonsu da ita ma su kasha ta, amma sai suka ce mat aba wajenta suka zo ba, don haka ta bar gurinsu, ba za su kasha ta ba.

 

Exit mobile version