Yadda Ya Kamata A Yi Shagulgulan Sallah – Husaini Adamu Yakun

Tabbas akwai kalubale a garemu mu iyaye da kuma hukuma, bukukuwa da shagulgulan Sallah ya zama al’ada a garemu ne tun iyaye da Kakanni har ma akan kebe wasu wurare da iyaye da yara sukan taru domnin gudanar da shagulgulan Sallah. To amma yanzun lamarin akwai kalubale domin ba hakan ake yi ba, yanzun tarbiyan yara ta gurbata, a baya a kan je a yi a kuma tashi lafiya cikin nishadi da farin ciki ba fad aba tashin hankali. Ba batun sara-suka, babu shaye-shaye. Wadannan shawarwari ne da suka fito daga bakin, Alhaji Husaini Adamu Yakun, shugaban masu sayar da Kaji da kwai na Jihar Kaduna, a matsayin sakon sag a al’ummar Musulmi a bisa taya murnar da yake mana da bukin Sallar Layya da ke gabanmu nan da ‘yan kwanaki.

Alhaji Husaini Yakun ya ci gaba da cewa,  A yanzun ya zama dole ga mu iyaye da mu janyo hankalin yaranmu, in har ya zamana za a je inda tarbiyan yara za ta gurbata, to kamata yay i kowa ya shiryawa yaransa bukukuwan Sallah a gida daga nan in akwai bukata su wuce da iyayen na su su tafi gidan ‘yan’uwa da abokanan arziki a yi zumunci a dawo gida. Amma a halin yanzun duk irin wadannan wuraren da akan ware domin yin shagulgulan akwai kalubale sosai a kansu wanda ya kamata a sa ido a kansu, mu kuma hana yaranmu zuwa irin wadannan wuraren, domin idan yaro ya je zai ga na sama da shi sun dauki kayan shaye-shaye, a nan yaro abin sha’awa ne zai bas hi ba tare da ya san illar abin ba, daga nan sai ya kwatanta idan ba a yi sa’a bas hi ma daganan ya dore kenan.

To ya kamata kuma hukuma ta sanya ido sosai a irin wadannan wuraren duk yaron da aka gani yana shaye-shaye a kama shi a hukunta shi. In kuma har kana son sai yaran naka sun je irin wannan wajen, to ka debe su da kanka ka kais u su yi abin da za su yi a gabanka sai ka dawo da su gida. Wasu zai b aka sha’awa ka ga sun debi yaran na su a mota sun je wuraren shakatawan sun yi nishadi sun dawo gida, amma ba a saki yaran hakanan kawai sakaka ba.

Ina kuma kara janyo hankulanmu musamman a kan yaranmu mata, domin a irin wadannan lokutan ne z aka ga yaran ‘yan mata sukan fita su je su gudanar da abin da bai dace ba, a aikata fasadi da sunan bukukuwan Sallah Allah Ya kiyaye. Akwai kalubale sosai a kanmu mu iyaye maza da mata musamman a kan tarbiyan ‘ya’yanmu mata, ya kamata mu kara zage damtse mu mayar da hankali sosai a kan tarbiyan ‘ya’yanmu mata musamman. Mu tabbatar mun hada karfi da karfe a tsakaninmu iyaye maza da mata mu gam un baiwa ‘yayanmu tarbiyar da ya kamata.

Sau da yawa malaman makaranta sukan yi kokarin baiwa yaranmu tarbiya tagari, amma sai ka ga in an dawo gida kuma iyaye suna warwarewa. Iyaye kar fa mu manta, Addininmu ya hana baligi namiji da mace su caba ado su kuma kebe a can gefe guda a cikin dare ne ko rana, ko a wani daki domin Allah ne kadai Ya san abin da zai iya faruwa a wannan lokacin. Don haka, dole ne mu iyaye mu tsananta matakai na tsaro ciki da waje a wajen tarbiyan yaranmu. Abubuwa da yawa suna faruwa ne tare da sakacinmu mu iyaye, domin sai wasu iyayen su ga diyarsu da wayar 20,000 ko ma 30,000, suna kallo ba tare da sun tambayi ma bahasi ba, way a baki, a kan me, me kike yi da ita? Da makamantan hakan. Wanda ko da aure wanda ya ba ta yake nemanta kamata yay i ya bari in sun yi auren sai ya saya mata a mazaunin matarsa.

Exit mobile version