Yadda Za A Rage Matsalar Rashin Aiki A Nijeriya Ta Hanyar Tura Matasa Kasashen Waje

Aiki

Daga Bello Hamza,

A daidai lokacin da ake fuskantar tsananin rashin aiki yi a fadin tarayyar Nijeriya, don kuwa an kiyasta cewa, akwai sama da ‘yan Nijeriya kusan miliyan 130 wadanda suke fama da rashin aikin yi ko suke fadi-tashin neman aikin yi ko suka rasa aikin yi. Wannan lamarin ya kara ta’azzara fatara, talauci da hauhuwar matsalar rashin tsaro.  Ahmed Adamu, PhD Malami a Jami’ar Nile dake Abuja Babbar Birnin Tarayyar Nijeriya ya bayar da mafita na yadda za a rage tare da kawo karshen matsalar rashin aiki a Nijeriya, ya yi wannan bayanin ne a mukalar da ya gabatar ranar 18 ga watan Nuwamba 2021 a wani taro da ya halarta, ya kuma aiko wa da Leadership Hausa kwafin mukalar, a cikinta ya tabo yadda rashin aikin yi a tsakanin al’umma ke barazana ga rayuwa da zamantakewar al’ummar da kuma yadda hakan ke ta’azara matsalar tsaro da ake fuskanta a sassan Nijeriya, ya ce, yakamata a samar da hanya mafi sauki da matasanmu za su fita zuwa kasashen waje a hukumance don yin cirani da baje basirar da Allah ya basu a kasashen duniya, wannan zai rage nauyin da ake fuskanta na neman aiki a cikin gida da kuma irin hatsarin da matasa ke fuskanta a kokarin sun a fita zuwa kasashe waje.

Ya kuma kara da cewa, “Duk kuwa da tulin basuka da gwamnati ke cigaba da rantowa tare da shirye-shirye daban-daban domin magance wannan babban kalubalen amma har yanzu dai lamarin na kara kazanta. Akwai bukatar neman wata dabarar domin cimma nasarar shawo kan lamarin.

Daya daga cikin hanyoyin da za a iya bi wajen shawo kan matsalar rashin aikin yi shi ne a gwamnati ta gabatar da wani shiri na musamman wanda Nijeriya za ta tura ‘yan kasarta miliyan 20 zuwa kasashen waje a cikin shekara 10.

Fita zuwa kasashen waje na kamari a yankin Afrika, wanda Nijeriya tana na gaba-gaba wajen samun adadin masu kaura daga kasar zuwa waje ta haramtattun hanyoyi, wadanda mafi yawan mutanen nan matasa ne. Matsin rayuwa da kunci ke tilasta ‘yan Nijeriya da daman gaske kaura zuwa waje domin neman rayuwa mai inganci da samun walwala”.

Daga na Dakta Ahmed Adamu, ya bayyana cewa, “A zahirance, kashi uku cikin goma na ‘yan Nijeriya na da burin barin Nijeriya zuwa kasar waje don neman rayuwa mai kyau. Wani matashi dan Nijeriya ya ce gara masa ya mutu a kokarinsa na kaura daga kasar nan a maimakon cigaba da zama a Nijeriya, kenan ya amince ya jefa rayuwarsa cikin hatsari wajen neman fita kasar waje ta gurbatacen hanya. A lokuta daban-daban, masu kaura ta barauniyar hanya suna fuskantar tulin barazana da firgici, cin zarafin su, take musu hakki da sauran wahalhalu. Amma duk da hakan sun gwammace su fuskanci wadannan matsalolin a maimakon zama cikin Nijeriya.

Nijeriya daya ce daga cikin kasashe masu neman kananan aikin yi da kuma gurbin kananan ayyukan, amma samun sabon aiki ya karanta ga masu nema. Wahala kawai ake sha ba tare kuma da samun aikin yi din ba, matsalar da ta mamaye ko’ina a fadin kasar nan.

Har ta kai yanayin da ana samun wani gurbin aikin yi guda daya a kalla mutum dari za su cika bukatar nema. Babu wani dama da zai iya cike gurbin rashin aikin da ake fama da shi a Nijeriya. Ana kuma kara samun marasa aikin yi. To me za mu yi kan hakan?”

Ya kuma ce, “Akwai bukatar Gwamnatin Nijeriya ta tsara wani halastaccen tsarin da zai bada damar fita waje don rage matsalar rashin aikin yi. Hakan zai bai wa ‘yan kasar nan da suka cancanta damar yin rijista da shirin hijira zuwa waje. Kuma hazikai, fasihan kwararrun a fannin kimiyya da likitocin da suka dace za su iya samun guraben aikin yi a wasu kasashen da suke bukatar masu irin kwarewarsu.

Gwamnati ta shiga yarjejeniyar fahimtar juna da gwamnatocin kasashen da suka ci gaba da suke bukatar ma’aikata. Wadannan kasashen za su kafa wata damar zabar ma’aikata daga Nijeriya da suke da muradin fita don neman aikin yi.

Kowace za ta gamsu ne da matakan da ta gindaya ga masu neman aiki da ita da suka hada da kwarewa koyon magana da yaren kasar da zai bai wa kowani dan Nijeriya da ke son aiki da kasar damar cike ka’idojin da suke akwai don fara aiki da zarar ya isa kasar wajen.

Ta wannan hanyar ‘yan Nijeriya da suka cancanta samun damar cike bukatar manyan kasashe uku da suke son aiki da ita. Za su nuna hazakarsu tare da kwarewa wajen amfani da harsuna daban-daban. Za su samu zarafin samun horon share fage na tsawon shekara daya ga duk dan Nijeriya da ya fita kasar wajen domin yin aiki.

Horon zai wakana ne ta hanyar gamsar da kasar da mutum ke so. Misali mutane suna son zuwa kasar Japan akwai bukatar su nemi sani da gogewa kan ababen da ake bukata ga ma’aikatan Japan. Sannan da bukatar su koyi amfani da yaren Japanese don iya mu’amala da mutanen can da musu aiki yadda suke so”.

Haka kuma ya bayyana cewa, “Ta karkashin shirin Gwamnatin Nijeriya za ta tura jeren bayanan tarihin wadanda suka dace da cike matakan da aka gindaya na yin aiki da kasar Japan. Sai dai hakkin mai daukan aiki ne zabar wanda yake so ya yi aiki da su daga cikin wadanda suka nuna sha’awar aiki da shi.

Sannan Gwamnatin kasar nan ta tattauna hanyoyin da wadanda suka ci gajiyar tafiya za su samu saukin fara rayuwa a can kasashen wajen da dauke musu nauyin jigila wato kudin jirgi.

Shirin zai zama wani dandamali ne na hada alaka tsakanin mai neman aiki da mai daukan aiki, ta yadda mai neman dauki aiki zai bibiyi masu son aiki yadda ya dace. Sannan zai taimaka wajen cimma yarjejeniya tsakanin mai neman aiki da mai daukan aiki ta wajen ganin an cika ka’idojin da suke akwai.

Hakan kuma zai bada damar tsari mai kyau ga fita kasashen waje, zai kuma rage ganganci da rayuwa ga matasan Nijeriya ke yi wajen fita kasar waje neman rayuwa mai inganci. Kenan za a samar da tsari halastaccen da zai bada dama ga mai neman dammar”.

Ya kuma ce, “A lokacin da na wallafa batun wannan tsarin a shafina na yanar gizo, ‘yan Nijeriya da daman gaske ciki har da kwararru daban-daban sun nuna sha’awar su ga wannan sabon tsarin. Hakan ya nuna akwai ‘yan kasar nan da yawa da suke son irin wannan shirin.

Fitar da albarkatun kasa ba ya takaita ne kawai ga albarkatun da suke cikin kasa ba har ma da dan adam. Fitar da jama’a zuwa kasar waje zai kyautata wa Nijeriya tattalin arzikinta da samar mata da riba.

A karshen wannan shekaran, adadin kayan da Nijeriya ke shigowa da su zai iya kawai tiriliyan 7, yayin da mai da ake fitar da shi ya takaita a kan tiriliyan 1. Don haka tura ‘yan Nijeriya kasashen waje domin yin aiki zai kyautata yawan abun da zai ke shigowa Nijeriya a matsayin riba. Kuma tabbas za a yi alfari da hakan.

Daga karshe, Dakta Ahmed Adamu, ya kara hasken cewa, “Sannan wannan tsarin zai kuma taimaka wajen shawo kan rigimar darajar naira da kudaden ksashen waje wacce dala ta zarce naira don haka za a samu damar daga darajar naira, kuma za a samu damar ayyukan yi sosai”.

A shekarar 2019, ‘yan Nijeriya da suke aiki a kasashen waje sun aiko wa Nijeriya dala Biliyan 26. Irin wannan kudin da ke shigowa shine mafi yawa baya ga kudin da kasar ke samu daga fita da danyen Mai.

Kara samar riba daga kasashen waje zai rage talauci da fatara. Wadanda suke aiki a kasashen wajen za su ke turo wa ahlinsu kudade zuwa gida, wanda zai rage radadin talauci a cikin al’umma. Sannan irin wannan damar zai kuma rage kaifin buga-bugar neman aiki ta ko halin kaka a fadin kasar.

Tunin wasu kasashe irinsu Philippines, Pakistan, Ethiopia, da Bangladesh suka rungumi wannan shirin. Ba kawai Nijeriya za ta tsaya da wannan shirin bane, akwai bukatar a gabatar da wasu tsare-tsare daban-daban domin rage kaifin matsalar rashin aikin yi.”

Ya kuma ce, tsarin zai taimaka wa gwamnati wajen samun kudaden shiga domin gwamnati za take samun dan abun shiga daga kowani dala da ya shigo. Gwamnatin za ta iya amfani da jrin wannan kudin wajen gudanar da ayyukan raga kasa da samar da wasu sabbin damar na aikin yi.

Exit mobile version