ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, September 12, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yadda Za A Tsaftace Hammata

by Leadership Hausa
9 months ago

Idan an gyara jiki kada a manta cewa akwai inda ya fi muhimmanci da a kula da shi. Musamman ma bayan an aske gashin gurin, akwai hanyoyi da za a bi don hana wajen yin baki.

Ababe da dama ne suke kawo hammata ta yi baki koda an aske gashin gurin. Yawan zufa da amfani da man cire gashin hammata da yawan kiba da kuma amfani da turare masu karfi a hammata.

  • Asusun NADF Ya Tallafa Wa Manoman Albasa 2,000 A Wasu Jihohin Kasar Nan
  • Da Sahalewar Nijeriya Bayan Samun Bayanan Sirri Amurka Ta Kai Hari — Tuggar

Amfani da man kwakwa:

ADVERTISEMENT

Babban abin da ake amfani da shi a wajen hada man zamani shi ne man kwa-kwa domin yana dauke ne da sinadarin kara haske kuma yana da bitamin E.

A shafa man kwa-kwa a hammata a kullum a yi minti goma kafin a yi wanka. Bayan an yi haka, sai a wanke da sabulu mara karfi (wanda sinadaran da aka hada shi ba mai zafi ba ne) da ruwan dumi.

LABARAI MASU NASABA

Yadda Ake Kula Da Labba Domin Su Kasance Masu Laushi

Yadda Ake Kare Hannu Daga Bushewa

 

Amgani da gurji da lemon tsami:

Kamar yadda aka sani cewa ruwan lemon tsami na dada hasken fata, haka kuma gurji shi ma na dauke da sinadarin kara wa fata haske da kuma sanya ta laushi da sulbi. A hada ruwan lemon tsami da markadadden gurji a wuri daya sannan a shafa a hammata. A bari ya jima na tsawon mintuna goma sannan a wanke da ruwan dumi.

 

Garin kurkur da kwai:

Kurkum ma na dada wa fata haske, za a iya kwaba garin kurkur da ruwan kwai sannan a shafa a hammata bayan mintuna goma zuwa sha biyar sai a wanke da ruwan dumi. A kullum kafin a yi wanka.

 

Aski: A daina barin hammata da gashi, a yi kokarin aske shi a lokacin da ya fito. Domin idan da akwai gashi a hammata, zai hana gumi bushewa zai fara tara shi ya yi ta ba da wani irin wari. Sai a ga koda an fesa turare, sai a ji kamshin turaren daban, warin hammata kuma daban.

Yin amfani da wadannan ababen wajen gyaran hammata zai rage warin jiki da kuma hana fesowar kuraje da fitowar bakar kala a karkashin hammata da kuma rage gumin hammata.

Leadership Hausa
Website |  + postsBio
  • Leadership Hausa
    Gwarzuwar Ma’aikaciyar Gwamnati Ta Shekarar 2026 Mrs Zubaida Umar
  • Leadership Hausa
    Gwarzon Ɗan Siyasa Na Shekarar 2026 Sanata Abdul’Aziz Abubakar Yari
  • Leadership Hausa
    Gwamnan Shekara na 2026 Gwamna Caleb Manasseh Mutfwang
  • Leadership Hausa
    Wane Ne Dan Shagamu: Su Wane Ne Suka Kashe Shi A Kano?

MASU ALAKA

Yadda Ake Kula Da Labba Domin Su Kasance Masu Laushi
Ado Da Kwalliya

Yadda Ake Kula Da Labba Domin Su Kasance Masu Laushi

September 5, 2026
Yadda Ake Kare Hannu Daga Bushewa
Ado Da Kwalliya

Yadda Ake Kare Hannu Daga Bushewa

August 29, 2026
Ado Da Kwalliya

Yadda Ake Kula Da Farce

August 23, 2026
Next Post
Hadaddun Lemukan ‘JUICE’

Hadaddun Lemukan ‘JUICE’

LABARAI MASU NASABA

Yaƙin Amurka Da Iran Ya Janyo Asarar Fitar Da Ganga Biliyan 2.8 Na Mai

Yaƙin Amurka Da Iran Ya Janyo Asarar Fitar Da Ganga Biliyan 2.8 Na Mai

September 12, 2026
Zan Dawo Da Tallafin Mai Ne Don Rage Farashin Fetur Da Na Sufuri – Atiku

Zan Dawo Da Tallafin Mai Ne Don Rage Farashin Fetur Da Na Sufuri – Atiku

September 12, 2026
An Gargaɗi Mazauna Kusa Da Kogin Kaduna Kan Sako Ruwa Daga Shiroro

An Gargaɗi Mazauna Kusa Da Kogin Kaduna Kan Sako Ruwa Daga Shiroro

September 12, 2026
Shekaru 22 Bayan Rushewar Nigeria Airways, Gwamnati Ta Biya Ma’aikata 2,700 Biliyan 18

Shekaru 22 Bayan Rushewar Nigeria Airways, Gwamnati Ta Biya Ma’aikata 2,700 Biliyan 18

September 12, 2026
Kalaman Christopher Musa Game Da El-Rufa’i Na Ci Gaba Da Tayar Da Ƙura

Kalaman Christopher Musa Game Da El-Rufa’i Na Ci Gaba Da Tayar Da Ƙura

September 12, 2026
Dangote Ya Ƙara Farashin Fetur, Kwana 2 Kafin Shiga Kasuwar Hannun jari

Sanata Yari Ya Gudanar Da Taron Masu Ruwa Da Tsaki A Zamfara

September 12, 2026
Gwamna Dauda Lawal Ya Raba Motocin Aiki Ga Manyan Makarantu A Zamfara

Gwamna Dauda Lawal Ya Raba Motocin Aiki Ga Manyan Makarantu A Zamfara

September 12, 2026
Dangote Ya Ƙara Farashin Fetur, Kwana 2 Kafin Shiga Kasuwar Hannun jari

Dangote Ya Ƙara Farashin Fetur, Kwana 2 Kafin Shiga Kasuwar Hannun jari

September 12, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Jam’iyyar APC Ce Za Ta Lashe Zaɓen Shugaban Ƙasa Da Gwamnoni A Nijeriya -Dikko Raɗɗa

September 12, 2026
NNPCL Ya Rage Farashin Man Fetur Zuwa ₦860 Kan Kowacce Lita – IPMAN

Mene Ne Ra’ayinku Kan Dawo Da Tallafin Man Fetur Ko Barin Sa?

September 12, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.