A birane da dama a Nijeriya, farashin Man Fetur duk lita daya, ana sayarwa, a tsakanin Naira 1,400 zuwa Naira 1,500.
Hakan ya sanya ‘yan kasar da dama, musamman talakawa kokawa, kan wannan karin farashin na Man.
Kazalika, hakan ya kuma nuna yadda ita ma, hukumar kula da harkokin sarrafawa da tacewa da kuma sufurin man fetur ta kasa NMDPRA, ta yi ikirarin cewa, ba ta lafi, kan wannnan karin, na farashin Man.
Hukumar a cikin sanarwar da ta fitar a ranar 19 na watan Satumbar 2026, ta ce, ba ita ce, ke da alhakkin daidata farashin Mai, a kasar ba.
Ta kafa hujja da sashe na 205 daya a cikin baka, na dokar masana’antar sarrafa Man.
Wannan dokar dai, ita ce, ta bayar da damar kayyade farashin Mai a kasar.
Wannan batun haka yake a Zahiri kuma mun yi Imani, da hakan.
A gefe daya, matatar Man dangote, ta kara farashin Man daga Naira 85 zuwa Naira 1,265 tare da kuma kara farashin, zuwa Naira 1,350 kan kowacce lita daya.
Ta ce, ta yi hakan ne, saboda tashin farashin danyen Mai a kasar duniya wanda ya kai dala 100 kan kowacce Ganga daya.
A cikin ‘yan kwanuka, dillalan Man suka kara farashinsa, wanda a cikin mako daya, gidajen Mai, musamman a Legas da Abuja, suka kara farashinsa, zuwa Naira 1,450, kan kowacce lita daya.
Hukumar NMDPRA ta yi ikirarin nuna damuwarta kan karin da ya jefa alumma cikin karin wata matsalar, musamman ga masu yin tafiye-tafiye da kuma shafar harkar kasuwanci, a daukacin fadin kasar.
Bugu da kari, hukumar ta dogara kan sashe na dokar masana’antu ta 205 biyu a cikin baka da kuma sashe na 205, hudu a cikin baka wato PIA, da suka haramtawa gwamnati shiga tsakani, kan daidaita farashin Mai.
Ta kuma yi ikirarin cewa, ita, ba wania abu da za ta yi, kan lamarin.
Hukumar dai, ta dogara ne, kan matatar Mai daya a kasar, inda ta dogara, kachkam, kan shigo da Man daga ketare.
Haka zalika, sashe na 216 na dokar hukumar, bai bata wani iko, na daidaita farashin Mai a kasar ba.
Masu kayyade farashin, babu abinda suka sani, illa batun kara farashin Man.
A gafe daya, ‘yan kasa masu amfani da Man, suna ci gaba da jin jiki, inda ake ci gaba da takike su, saboda karin farashin Man kuma babu wani alamun sauki da za su iya samu.
A duk lokacin da aka samu karin farashin Mai a kasar, hakan na shafar fannin sufuri tare da kuma samun karuwar farashin kayan abinci, musamman duba da cewa, sai an kashe kudi ne, ake yin safarar kayan amfanin gona da aka noma, zuwa kasuwannin kasar.
Suma masu kanannan sana’oi, musamman wadanda suka dogara da yin amfani da injinan Janareta, duba da irin matsalar da ake ci gaba da fuskanta, daga babban layin kasamr da wutar lantarki na kasa, inda karin farashin, na ci gaba da shafar sana’arsu,
A bangaren ‘yan Nijeriya, abinda suka fi bukata daga gun mahukuntan kasar shi ne, a samar Man a cikin farashi mai sauki, ba wai hujojin da hukumar, ta fake a kansu, a cikin sanawar da ta fitar, kan lamarin ba.
A nan, wannan Jaridar ta bukaci a maido da tsarin daidaita farashin Man ko kuma a sake mai do tallafin, da aka cire.
Bugu da kari, muka kira ga mahukuntan hukumar da su yi amfani da nauyin da aka dora masu, ba wai fakewa kan dokar ta PIA ba, a duk lokacin da aka samu karin farashin, a kasar.
Ita kanta majalisar kasar, akwai rawar da za ta taka kan karbar bayanai akai-akai daga hukumar ta NMDPRA.
Kazalika, ya zama wajibi, kwamitin kula da harkokin Mai da albarkatunsa ya gayyaci mahukunta hukumar ta NMDPRA, domin yin bayani dalla-dalla, musamman kan yadda hukumar ta koma tamkar, ta koma ta zango daya, duba da yadda farashin Man, a kasar ke tafiya kamar na gasa.
Abin takaiaci ne, kan gazawar mahukuntan hukumar, kan gaza bayar da cikakken ba’asi ko bayan ikan samun karin farashin, wanda hakan ya nuna a Zahiri, su mahukunta ne ba su cancanci, a kira su mahukunta ba.
A karshe, za mu iya cewa, sai idan hukumat a zahirance, ta nunawa ‘yan Nijeriya cewa, tana da karfin iko, kana za su iya cewa, suna da yakini, akanta, ba wai kawai sai idan an samu karin farashin ba, ta rika ftra da sanarar da saba yi, kan karin ba.














