ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, September 11, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Asusun NADF Ya Tallafa Wa Manoman Albasa 2,000 A Wasu Jihohin Kasar Nan

by Leadership Hausa
9 months ago

Asusun tallafa wa ci gaban noma na kasa (NADF), ya kaddamar da aikin raba wa manoman Albasa kayan aikin gaggawa.

Kimanin manoman Albasar 2,000 da ke Jihohin Arewacin kasar nan ne, suka amfana da kayan. Asusun ya tallafa musu ne da nufin rage musu radadin ambaliyar ruwan sama da ta lalata gonakinsu a shekarar 2024.

  • Rahoton KPMG Ya Shaida Karfin Gwiwar Kamfanonin Kasa Da Kasa Game Da Bunkasar Tattalin Arzikin Sin A 2026
  • Sheikh Al-Sudais Ya Gargadi Masu Ibadah Kan Kiyaye Darajar Masallatan Harami

Har ila yau, ta gudanar da wannan tallafin ne, bisa hadaka da Ma’aikatar Aikin Noma da Samar da Wadataccen Abinci ta Tarayya. kazalika, an bayar da daukin ne a Jihohin Borno, Yobe, Sakkwato da kuma Kebbi, inda wannan talllafin ya zo daidai da matsayin bangare na kokarin karfafa aiwatar da ajandar ‘Renew Hopes’ ta Shugaba Bola Ahmed Tinubu, na tallafa wa manoma.

ADVERTISEMENT

Jaridar BusinessDay ta ruwaito cewa, an tallafa kowane manomin an Albasa da buhunhuna hudu na takin zamani, mai nauyin kilo 50, samfurin 15-15 NPK da kuma Irin Albasa da magungunan feshi da na kashe kwari.

Daukacin gwamnonin da ke wadannan jihohin hudu da manoman na Albasa suka amfana da tallafin, sun gode wa asusun na NADF. Sun kuma yi alkawarin ci gaba da yin hadaka da gwamnatin tarayya da sauran masu ruwa da tsaki, musamman a bangaren yin noman Albasa, domin samun riba da kara habaka tattalin aziki da samar da ayyukan yi da kuma rage talauci.

LABARAI MASU NASABA

Kha’amuna Khadi Ta Karɓi Jagorancin Gudanarwa Ta Bankin Noma

Dalilin Da Ya Sa Aka Horar Da Manoman Tumatir 100 A Garin Zariya

Kazalika, an kaddamar da rabon kayan ne a harabar kamfanin sarrafa takin zamani da ke babban birnin Maiduguri, wanda mallakin Gwamnatin Jihar Borno ne. Babban Sakatare kuma jami’in a Asusun na NADF, Mohammed Ibrahim ya bayyana cewa; wannan tallafin gwamnatin tarayya ce ta samar da shi, bisa nufin rage wa manoman na Albasar a wadannan jihohin asarar da suka yi, sakamakon ambaliyar ruwan sama a kakar noma ta bara da kuma nufin kara bunkasa fannin aikin noma a kasar nan.

Ibrahim, wanda wani jami’i ya wakilce shi a wajen taron rabar da kayan, Shettima Gambo Lawan, ya sanar da cewa; asarar da manoman Albasar suka yi, wani babban kalubale ne da zai iya haifar da koma baya ga fannin na nomanta a kasar da kuma shafar ribar da ya kamata su samu daga fannin, inda ya yi nuni da cewa; wannan tallafi ya zo a kan lokaci.

Ya kara da cewa, wannan tallafi shi ne wanda aka fara gudanarwa a zangon farko, karkashin shirin na asusun NADF, musamman ga manoman da suka yi asara sakamakon iftila’in ambaliyar ruwan sama da kuma na kalubalen sauyin yanayi.

“Manoman Albasa sama da 2,000 ne suka amfana kai tsaye da wannan tallafi, musamman duba da cewa; fannin na noman Albasar a fadin kasar nan, ya kasance yana inganta rayuwar manoman da suka rungumi fannin,” in ji Sakataren.

Ya ci gaba da cewa, sai dai abin takaici; manoman Albasar da dama sun tabka asara biyo bayan samun ambaliyar ruwan saman, musamman a Jihohin Sakkwato, Kebbi, Yobe da kuma Borno. A cewarsa, wannan asarar da suka yi, ta shafi kudaden shigarsu da kuma haifar da karancin Albasar a kasuwanin kasar nan. “Saboda hakan ne, asusun na NADF, ya yi wannan hadaka da gwamonin wadannan jihohi da kuma sauran masu ruwa da tsaki a fannin aikin noma, domin bayar da wannan dauki na gaggawa ga manoman na Albasa da ke fadin wadannan jihohi da nufin kara karfafa wa manoman gwiwa,” a cewarsa.

“Wannan dauki da aka gudanar a yau, an yi shi ne karkashin shirin aiwatar da ajandar ‘Renew Hopes’, na Shugaba Bola Ahmed Tinubu, domin tallafa wa manoma”, a cewar Ibrahim.

Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum ne ya kaddamar da rabar da kayan. Babagana, wanda kwamishinan ma’aikatar aikin gona da kula da albarkatun kasa na jihar, Bawu Musawu Alhaji ne, ya wakilce shi a wajen taron tare da yaba wa gwamnatin tarayya kan samar da wannan tallafi.

Ya sanar da cewa, manoman Albasa a jihar 450 ne, suka amfana da wannan tallafi, inda kuma sauran manoma 1,550, da aka zabo a sauran jihohin, suka amfana da wannan tallafi a yayin ambaliyar ruwan sama da ta afku a gonakinsu, a 2024. “A madadin Gwamnatin Jihar Borno da kuma takwarorina, na Yobe, Sakkwato da kuma Kebbi, muna mika godiyarmu ga asusun NADF, kan nuna tausayawarsa na bayar da wannan tallafi,” a cewar Zulum.

“Wannan shirin, ya a nuna a zahiri irin shugabanci na gari da sauraron koken manoma da kuma yin dubi, kan irin gudunmawar da fannin aikin noma ke bayarwa a kasar nan,” in ji gwamnan.

Leadership Hausa
Website |  + postsBio
  • Leadership Hausa
    Wane Ne Dan Shagamu: Su Wane Ne Suka Kashe Shi A Kano?
  • Leadership Hausa
    An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu
  • Leadership Hausa
    Karuwar Farin Jinin Gwamna Umaru Bago A Siyasar Jihar Neja
  • Leadership Hausa
    Kyakkyawan Tsarin Laken Asiri Zai Dakile Shirin Magudin Zabe A Nijeriya —Mohammed

MASU ALAKA

Abin Da Ya Sa Gidauniyar NADF Da Bankin Manoma Suka Yi Haḍaka
Noma Da Kiwo

Kha’amuna Khadi Ta Karɓi Jagorancin Gudanarwa Ta Bankin Noma

August 1, 2026
Dalilin Da Ya Sa Aka Horar Da Manoman Tumatir 100 A Garin Zariya
Noma Da Kiwo

Dalilin Da Ya Sa Aka Horar Da Manoman Tumatir 100 A Garin Zariya

July 18, 2026
Labarin Farfesoshi Tagwaye Da Suka Yi Karatun Digiri Tare Suna Aiki Tare A Wuri Ɗaya
Noma Da Kiwo

Sharhi A Kan Dabarun Zamani Na Yin Auren Ƴaƴan Itatuwa

July 11, 2026
Next Post
An Yi Matukar Inganta Harkokin Sadarwa A Kasar Sin Cikin Shekaru Biyar Da Suka Wuce

An Yi Matukar Inganta Harkokin Sadarwa A Kasar Sin Cikin Shekaru Biyar Da Suka Wuce

LABARAI MASU NASABA

ASUU Ta Yi Barazanar Shiga Yajin Aiki Na Ƙasa Gaba Ɗaya

September 11, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwarzon Gwamnan Shekarar 2026 Kwamared Nasir Idris

September 11, 2026

Dalilin Da Ya Sa Ba Zan Janye Wa Atiku Ba A Zaɓen 2027 – Peter Obi

September 11, 2026
Farashin Siminti Zai Ragu Idan Farashin Kayan Aiki Ya Sauka – BUA

Gwarzon Shekarar 2026 Abdulsamad Rabiu

September 11, 2026
Cutar Kwalara Na Ci Gaba Da Yi Wa ‘Yan Nijeriya Kisan Mummuƙe

Buƙatar Ɗaukar Matakan Daƙile Yaɗuwar Cutar Mashaƙo A Nijeriya

September 11, 2026
Ding Xuexiang Ya Halarci Taron Kolin CIFTIS Tare Da Ganawa Da Manyan Jami’an Kasashen Waje

Ding Xuexiang Ya Halarci Taron Kolin CIFTIS Tare Da Ganawa Da Manyan Jami’an Kasashen Waje

September 10, 2026
Sin Ce Ta Zo Ta Farko A Rahoton Yanayin Tsaron Jama’a Na Duniya

Sin Ce Ta Zo Ta Farko A Rahoton Yanayin Tsaron Jama’a Na Duniya

September 10, 2026
Sin Ta Ciri Tuta Game Da Rawar Gani Da Take Takawa A Fannin Warware Kalubalen Tsaro A Gabas Ta Tsakiya

Sin Ta Ciri Tuta Game Da Rawar Gani Da Take Takawa A Fannin Warware Kalubalen Tsaro A Gabas Ta Tsakiya

September 10, 2026
Gwamnatin Tarayya Ta Gwangwaje Tawagar Kwallon Kwando Ta Mata Da Dala 100,000 Kowace

Gwamnatin Tarayya Ta Gwangwaje Tawagar Kwallon Kwando Ta Mata Da Dala 100,000 Kowace

September 10, 2026
Sin Da Amurka Na Gudanar Da Tattaunawa Dangane Da Yiwuwar Rage Harajin Ramuwar Gayya Wanda Darajarsa Ka Iya Kaiwa Dala Biliyan 30

Sin Da Amurka Na Gudanar Da Tattaunawa Dangane Da Yiwuwar Rage Harajin Ramuwar Gayya Wanda Darajarsa Ka Iya Kaiwa Dala Biliyan 30

September 10, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.