Wannan hadin ba ya sa bilicin, yana fitar da ainahin fatar mutum, sannan yana cire Narkarwa yana gyara fata sosai.
Wannan hadin ba shi da wata illa saboda na asalin abubuwa ne, sannan kuma ba shi da wata wahala sosai ba shi da illa a jikin fata, na asali ne na gida.
Za su gyara miki jiki sannan kuma su da wo miki da martabar fatarki.
- Kamfanonin Kasa Da Kasa Na Fatan Yin Amfani Da Damammaki Na Shirin Raya Kasa Na Shekaru Biyar–Biyar Karo Na 15 Na Sin
- Ƴan Bindigar Daji: Jihohin Arewa 7 Sun Kaddamar Da Rundunar Fatattakar Su
Abubuwan da ake bukata:
Suga kofi daya da rabi, Zuma babban cokali biyu, Bota babban cokali daya, Body wash.
Yadda ake hadawa:
Da farko za ki sa mu roba mai kyau haka sai ki zuba suga a ciki sannan ki ka wo zumarki mai kyau ki zuba, sai ki zuba bota sai ki ka wo body wash ko wanne iri kike da shi za ki iya amfani da shi sai ki zuba.
Sannan ki yi ta kwaba shi kina damawa kina gauraya shi kamar kina buga shi za ki yi ta yi har sai ya yi laushi sugan ya narke za ki ga kalarsa ta koma yalo.
Shikenan kin gama hadawa. Za ki rika wanka da shi, idan kika fara amfani da shi kafin sati daya fatarki ta canja ta yi kyau.













