• English
  • Business News
Tuesday, October 14, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yadda Za Ki Hada Biredin Shawarma A Gida

by Bilkisu Tijjani
2 years ago
Shawarma

Assalamu alaikum masu karatu, barkammu da sake haduwa da ku a wannan makon a cikin shirin namu na Girki Adon Mata.
To yau kuma za mu yi bayani kan yadda uwargida za ta yi Burodin Shawarma
Ga dai abubuwa da uwargida za ki tanada:
Fulawa, yis (yeast), gishiri, bota (butter) ko man zaitun:

Yadda za ki kwaba Biredin:
Za ki samu roba karama ki zuba yis din a ciki ki zuba ruwa, sai ki bar shi ya jiku ya kuma narke a cikin ruwan. Sai ki sami wata babbar roba ki zuba fulawarki da gishiri da bota ko man zaitun ki juya ki kawo wannan ruwa yis din da kika jika ki zuba a kai, ki kawo ruwa ki zuba a kan fulawar ki kwaba sosai har sai kin ga ta hade jikinta, sannan sai kin ga ta daina kama hannunki, idan kin ga tana makalewa a hannunki sai ki kara fulawa ki sami wata robar ki shafe ta da mai ki saka sauran fulawar a ciki.

Amfanin shafa man shi ne don kada ta lillike a jikin robar. Daga nan ki rufe robar ki ajiye a rana ta yi kamar awa biyu domin ta kumburo ta tashi.

Idan kin bude kin ga ya rubanya yadda yake wato ya kumburo sai ki saka hannu ki naushe shi domin ya kwanta, ki kara juyawa, sai ki gutsira yadda kike so ki zuba fulawa a kan allon yanka wato (chopping board) ki murza iya fadin da kike so. Ki barbade shi da fulawa ki ajiye shi a gefe ki ci gaba da murza ragowar.

Idan kin gama sai ki sami kasko ki dora shi a kan wuta idan ya yi zafi sosai sai ki dauko wannan fulawar da kika tada ta ki saka a cikin kaskon, idan kin ga ta fara kumburowa kamar roba balo sai ki juya daya barin ma ta yi haka, haka za ki rin ga yi har ki gama gasawa gaba daya. A ci dadi lafiya.

LABARAI MASU NASABA

Yadda Ake Gurasa Ta Semovita

Yadda Ake Lemon Tsamiya (Tamarin Juice)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Yadda Ake Gurasa Ta Semovita
Girke-Girke

Yadda Ake Gurasa Ta Semovita

October 12, 2025
Yadda Ake Lemon Tsamiya (Tamarin Juice)
Girke-Girke

Yadda Ake Lemon Tsamiya (Tamarin Juice)

October 4, 2025
Yadda Ake Hada Sushi
Girke-Girke

Yadda Ake Hada Sushi

September 27, 2025
Next Post
NIS

NIS Ta Kara Kaimin Sintiri A Arewa Maso Gabas Domin Dakile Karancin Kayan Abinci

LABARAI MASU NASABA

Amnesty International Ta Soki Tinubu Kan Yi Wa Masu Laifin Take Haƙƙin Ɗan Adam Afuwa

Amnesty International Ta Soki Tinubu Kan Yi Wa Masu Laifin Take Haƙƙin Ɗan Adam Afuwa

October 14, 2025
‘Yan Bindiga Sun Sace Ɗan Jarida A Kan Hanyarsa Ta Zuwa Ɗaukar Horo A Kwara

‘Yan Bindiga Sun Sace Ɗan Jarida A Kan Hanyarsa Ta Zuwa Ɗaukar Horo A Kwara

October 14, 2025
Zaman Gidan Yari Ya Nuna Min Mutanen Da Ya Kamata Na Yi Hulɗar Siyasa Da Su — Faruk Lawan

Zaman Gidan Yari Ya Nuna Min Mutanen Da Ya Kamata Na Yi Hulɗar Siyasa Da Su — Faruk Lawan

October 14, 2025
Majalisa Na Shirin Sauya Lokacin Zaɓen 2027 Zuwa Nuwamba 2026

Majalisa Na Shirin Sauya Lokacin Zaɓen 2027 Zuwa Nuwamba 2026

October 13, 2025
Yajin Aiki: Malaman Jami’a Sun Ce Barazanar ‘Ba Aiki, Ba Biya’ Ba Zata Tsorata Su Ba

Yajin Aiki: Malaman Jami’a Sun Ce Barazanar ‘Ba Aiki, Ba Biya’ Ba Zata Tsorata Su Ba

October 13, 2025
Nazarin CGTN: Jama’ar Duniya Sun Jinjinawa Rawar Da Mata Ke Takawa A Harkokin Ci Gaba

Nazarin CGTN: Jama’ar Duniya Sun Jinjinawa Rawar Da Mata Ke Takawa A Harkokin Ci Gaba

October 13, 2025
Matakan Da Sin Ta Dauka Na Mai Da Martani Ga Bincike Mai Lamba “301” Da Amurka Ta Gudanar Sun Zama Wajibi Don Kare Hakkinta

Matakan Da Sin Ta Dauka Na Mai Da Martani Ga Bincike Mai Lamba “301” Da Amurka Ta Gudanar Sun Zama Wajibi Don Kare Hakkinta

October 13, 2025
NPFL Ta Ci Tarar Kano Pillars ₦9.5m, Ta Rage Mata Maki 3 Da Ƙwallaye 3

NPFL Ta Ci Tarar Kano Pillars ₦9.5m, Ta Rage Mata Maki 3 Da Ƙwallaye 3

October 13, 2025
Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar Da Gangamin Wayar Da Kai Kan Laifuka A Intanet

Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar Da Gangamin Wayar Da Kai Kan Laifuka A Intanet

October 13, 2025
Ana Gudanar Da Taron Masu Mukamin Magajin Gari Na Kasa Da Kasa A Birnin Dunhuang Na Sin

Ana Gudanar Da Taron Masu Mukamin Magajin Gari Na Kasa Da Kasa A Birnin Dunhuang Na Sin

October 13, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.