Yajin aiki wata hanya ce da ma’aikata ke bi domin ganin an biya su hakkokinsu na aiki. Yajin aiki a Nijeriya na neman kasa samun tasiri wajen gwamnati.
Yanzu haka malaman jami’a sun kwashe watanni suna daka yajin amma, har yanzu kwalliya ta kasa biyan kudin sabulu.
- Buhari Ya Mika Sakon Ta’aziyyar Rasuwar Tsohon Sufeton ‘Yansanda Tafa Balogun
- Jihar Nasarawa Ta Fadakar Da Al’ummarta A Kan Cutar Hanta
A karshen watan da ya gabata ne shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya bayar wa’adin mako biyu ga masu ruwa da tsaki kan harkar ilimi da su tabbatar da warware wannan matsala cikin mako biyu, amma sai ga shi har zuwa wannan lokaci, ba a cika wannan umarni na shugaban kasa ba, al’amarin da ya sa ASUU ta ba da sabon umarni na ci gaba da yajin aikin, al’amarin da zai kara jefa daliban da ke zaune a gida, halin damuwa.
Sai dai duk da ci gaba da wannan yajin aikin yanzu haka, ana ci gaba da tattauna wa da gwamnati kan wannan lamari, sai dai abin tambayar shi ne, yaushe za a cim ma matsaya, wannan shi ne abin da ‘yan Nijeriya suka matsu su ji, domin kuwa, an dade ana tafka ruwa kasa tana shanye wa.
Don haka ne ma malaman jami’ar suka ja daga a wannan karon, da niyyar sai sun ga abin da ya ture wa buzu nadi.
Shi dai yajin aiki wata hanya ce da ma’aikata ke bi, wajen ta kaurace wa zuwa gurin da suke yin aiki, da niyyar sai biya musu bukatunsu kafin su koma.
Wani lokaci hakarsu na cim ma ruwa, wani lokacin kuma haka nan za su gaji su koma bakin aikin ba tare da samun biyan bukatar ba.
Zuwa yanzu yajin aikin da kungiyar malaman jami’oi ta kasa ta shiga koda yake ba shi ba ne na farko, na wanann shekarar dai an fara shi ne ranar 14 ga watan Fabarairu na shekara ta 2022, wanda kungiyar ta bukaci a biya mata bukatunta da suka yi yarjejeniya da gwamnatin tarayya, amma ba a samu cika mata su ba.
Yau kwana 172 ke nan, watau fiye da wata biyar ke nan daliban jam’o’i suke zaune a gida ba tare.
Ranar Lahadi 31 ga watan Yuni 2022 ta makon da ya wuce ne wa’adinta na mako hudu ya cika, ba tare da samun cimma buri ba,hakan shi ya sa, ASUU ta sake ba da wani wa’adin na wasu karin mako hudu.
Idan dai ba a manta ba, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba Ministan ilimi Adamu Adamu mako biyu da ya kawo karshen yajin aikin.
Sai dai bisa ga dukkan alamu ba a samu cim ma wata matsaya ba, shi ya sa suka kara bada wani wa’adin mako hudu wanda ya fara daga 1 ga watan Agusta 2022.
Kungiyar ASUU ba ita kadai ba ce a gwagwarmayar da take yi ta ganin an koma bakin aiki ba bayan biya mata bukatunta, domin kuwa kungiyar kwadago ta kasa NLC na daga cikin masu mara ma ta baya, inda ta shiga kwarya-kwaryar zanga- zanga ta kasa baki daya ta kwana biyu, domin nuna goyon bayan a biya mata hakkinta a ranar 26 da 27 ga watan Yuli 2022.
Wasu kungiyoyi da dama su ma ba a bar su a baya ba, domin kuwa sun goya ma ita kungiyar baya ta ganin an biya mata hakkinta.
Ba kungiyar ASUU kadai ta shiga yajin aiki ba domin kuwa kungiyar manyan ma’aikata jami’o’i ta kasa SSANU suna mara musu baya.
Abin bai tsaya a nan ba, saboda kungiyar Likitoci masu koyon aiki “Resident Doctors Association” wadda ita ma ba wannan ba ne karo na farko da fara shiga irin yajin aiki ba domin wa’adi ne ta bayar.Ita ma ta bada wa’adin mako biyu ma gwamnatin tarayya ta biya mata bukatunta ko kuma ta tsunduma cikin yajin aiki, kamar ASUU ta saba shiga irin wannan yajin aikin, ta tafi ta bar marasa lafiya wasu kwance a asbiti ba tare da cikakkiyar kulawa ba, wasu suna mutuwa, wasu su kara tagaiyara ba masu kulawa da lafiyarsu,ba tare da samun an biya mata dukkan bukatun nata ba.