Likitoci masu neman ƙwarewa a Abuja sun fara yajin aiki saboda rashin biyan albashi, kuɗaɗen alawus, da sauran haƙƙoƙinsu.
A taron manema labarai da ƙungiyar likitocin ta gudanar a ranar Laraba, shugaban ƙungiyar, Dokta George Ebong, ya bayyana cewa yajin aikin na gargaɗi ne kuma zai ɗauki kwanaki uku.
- Ma’aikatar Harkokin Wajen Sin: Babu Wanda Zai Ci Nasara A Yakin Cinikayya Ko Yakin Harajin Kwastam
- Jagoranci Nagari: Kungiyar Lauyoyi Ta Karrama Gwamnan Zamfara Da Lambar Yabo
Yajin aikin ya shafi ayyukan asibitocin gwamnati a babban birnin tarayya, inda aka samu cikas a ayyukan jinya.
Dokta Ebong ya bayyana cewa sun ɗauki wannan matakin ne bayan wa’adin makonni uku da suka bai wa gwamnati don warware matsalolin bai haifar da sakamako ba.
Ƙungiyar likitocin ta koka kan halin ko-in-kula da asibitocin Abuja ke ciki, inda suka nemi Ministan Abuja, Nyesome Wike, da ya shiga cikin lamarin don magance matsalar kafin yajin aikin ya tsawaita.
A ranar Talata ne shugabannin ƙungiyar suka cimma matsayar shiga yajin aiki bayan wani muhimmin taro da suka gudanar.