Daga Bala Kukkuru
An shawarci Gwamnatin Tarayyar Nijeriya da ta kara damara a wajan gyara tarbiyyar matasa da yara kananu masu tasowa a duk fadin kasar.
Imam Suleman Ibrahim, Babban Limamin Masallacin Juma’a na tsibirin rukunin gidajen unguwar Wantauzan Anfo Biktoriya Ailan kuma shugaban kungiyar Izalatul Bidi’a Wa Ikamatus Sunna ta kasa reshan Jihar Legas ne ya bukaci hakan a lokacin da ya ke gudanar da hudubarsa ta sallar Juma’a a makon jiya.
Ya ce, kafin zuwan annobar Korona a na koya wa dalibai karatu kwana biyar a cikin mako daya, Asabar da Lahadi ne kawai yara ba su zuwa makaranta, amma yanzu bayan cutar ta wuce, an dawo a na koya wa yara karatu kwana uku a cikin mako daya.
A cewarsa, “to ka ga tun daga nan an fara samun matsaloli a wannan bangare. Abinda a ke koya wa yara karatu kwana biyar a mako, an dawo kwana uku a cikin mako. Yaushe yara za su fahimci abubuwan da a ke koya mu su?”