Ministan Yada Labarai Da Wayar Da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana cewa ana kokarin cusa kaunar kasa a zukatan al’umma ne a matsayin wata dabara ta yakar muggan laifuka irin su hare-haren ‘yan bindiga, satar mutane, da ta’addanci a Nijeriya.
Mai tallafa wa ministan kan harkokin yada labarai, Malam Rabi’u Ibrahim, ya ruwaito a cikin wata sanarwa ga manema labarai cewa Idris ya fadi hakan ne a ranar Juma’a a Abuja lokacin da ya karbi bakuncin Babban Hafsan Hafsoshin Tsaro (CDS), Janar Christopher Musa, wanda ya kai masa ziyarar aiki a ofishinsa.
- Ina Rokon Allah Ya Shirye Ni Kafin Lokacin Mutuwata -Murja Kunya
- Shirin Mati A Zazzau’ Zai Zama Fim Na Hausa Na Farko Da Za A Haska A Tashar Netflix
Ministan ya ce sahihiyar hanyar da za a yaki aikata muggan laifuffuka ita ce a saka so da kaunar kasa da sadaukarwa a zukatan jama’a tare da haduwa wuri daya a matsayin ‘yan kasa ɗaya al’umma ɗaya domin a dunkule a yaki muggan laifuffuka.
Ya ce: “Tilas ne a dawo da batutuwan nan na sadaukar da kai da kuma so da kaunar kasa, domin mu samu irin hadin kai da albarkar da dukkan mu mu ke nema. Mun ga yadda kyawawan ɗabi’un mu su ke ta sukurkucewa – tilas ne mu dawo da wadannan kyawawan dabi’u kuma mu sake dawowa cikin hayyacin mu a matsayin ‘yan Nijeriya.
“Ya kamata mu sake zama mu ga inda mu ka kauce daga alkibila da nufin yin gyaran da ya dace a yanzu.
“Na gode kwarai da wannan ziyara. Mu na ganin cewa irin hadin gwiwar da ku ke so shi ne duk mu cure a wuri guda domin mu yaki ta’addanci kuma mu sama wa ƙasar nan hadin kai, cigaba, da zaman lumana.
“Babu yadda za ku iya samun nasara a wannan yaki ba tare da babbar rawar da kafafen daya labarai na Nijeriya da su kan su ‘yan Nijeriyar za su taka ba.”
Idris ya ce aikata muggan laifuffuka ya jawo bata suna sosai ga Nijeriya, don haka aikin da ya rataya a wuyan wannan ma’aikatar shi ne ta kyautata tare da sauya tunanin da ake yi game da kasar.
Ministan, wanda ya jaddada cewa yada labarai na da muhimmanci ga yaki da ta’addanci, ya kuma ce hadin gwiwa tsakanin ma’aikatar tasa da hukumomin soja ya na da muhimmanci wajen samar da matsaya da za ta karfafa tsaron kasa kuma ta inganta martabar kasar a idon duniya.
Idris ya ce nan ba da jimawa ba ma’aikatar za ta kaddamar da gangamin yekuwar sauya fasalin ƙasa a matsayin wani kokari na musamman da za a sanya sabon shaukin kaunar kasa a zukatan al’umma.
“Wadansu daga cikin wadancan abubuwan da mu ke magana a kan su za su fara fitowa a bainar jama’a a farkon shekara mai zuwa lokacin da mu ke fatan Shugaban Kasa zai jagoranci gangamin yekuwar sauya fasalin kasa. Mu na so a sake tattaunawa kan wannan batu na ma’anar dan kasa”.
Haka kuma ministan ya bukaci hukumomin soja da su dawo da tsarin nan na saka ‘yan jarida a cikin gumurzun yaki domin su samo bayanan farko na yadda ake yaki wanda ta hakan ne za a samar da labarai masu inganci.
Tun da farko sai da Babban Hafsan Hafsoshin Tsaro din, wato Janar Musa, ya ce ziyarar da su ka kai wa ministan ta na daga cikin dabarun su na yaƙi wadanda ba na gumurzu ba ne domin su gina haɗin gwiwa tsakanin rundunonin soja da kafafen yada labarai saboda kalubalen da sojoji ke fuskanta a yakin ta fuskoki daban-daban sun shafi jama’a ne inda su sojojin da su ‘yan ta’addan kowa so ya ke ya ja ra’ayin ‘yan Nijeriya.
Ya ce: “Wannan ya na daga cikin hanyoyin da mu ke bi na gudanar da al’amurra domin mu gina hadin gwiwa tsakanin Rundunonin Soja da jama’ar kasa kuma babu inda ya fi cancanta mu fara da shi da ya fi inda labarai ke fitowa.”
Ya yi kira ga jama’a da su ba sojoji goyon baya a kan yaki da tada hankalin jama’a, ta’addanci, da hare-haren ‘yan bindiga
Ya nanata cewa wannan yaki al’amari ne da ke bukatar saka hannun dukkan ‘yan Nijeriya domin a murkushe manyan masu aikata laifuffukan da ke kawo barazana ga dorewar kasar nan.
Musa ya ce gudanar da harkar yaɗa labarai cikin tsari wani babban ginshiki ne wajen yaki da ta’addanci domin yawancin ‘yan ta’addar an yaudare su har su ka tashi tsaye su na yakar kasar haihuwar su.
Ya ce ta hanyar gudanar da yada labarai cikin tsari da kuma fadakarwa, rundunar soja ta samu nasarar jawo hankalin wasu daga cikin ‘yan ta’addar su ka aje makaman su, su ka mika wuya ga gwamnati.
Ya yi bayyana cewa ya zuwa yanzu kimanin ‘yan ta’adda 140,000 ne su ka mika wuya ga rundunar soja a bisa kankin kan su.
Janar Musa ya ce yanzu aikata muggan laifuffuka ya tashi daga batun shaukin akida zuwa son a samu kudi, inda ‘yan ta’adda ke samun karamar riba ta hanyar satar mutane da kai hare-hare da sauran muggan laifuffuka.
Shugabannin hukumomin yada labarai na gwamnati da su ka mara wa ministan baya wajen karbar maziyarcin sun haɗa da Darakta-Janar na Hukumar Talbijin ta Kasa (NTA), Malam Abdulhamid Dembos; da takwaran sa na Hukumar Rediyo ta Nijeriya (FRCN), Dakta Mohammed Bulama; da na Muryar Nijeriya (VON), Malam Jibrin Ndace; na Hukumar Wayar Da Kai ta Kasa (NOA), Mista Lanre Issa-Onilu; na Hukumar Kula Da Gidajen Rediyo Da Talbijin ta Kasa (NBC), Mista Charles Ebuebu, da kuma Babban Sakataren Cibiyar ‘Yan Jarida ta Nijeriya (NPC), Mista Dili Ezughah.