Mai magana da yawun kungiyar yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, Sanata Dino Melaye ya bayyana cewa ‘yan APC ne ke kara ruruwa wutar rikicin sai an cire shugaban jam’iyyar PDP, Dakta Iyorchia Ayu kafin zaben 2023.
Melaye ya bayyana hakan ne lokacin da yake tattaunawa a dakin watsa shirye-shirye na LEADERSHIP da ke Abuja.
Ya kara da cewa ‘yan APC suna kokarin tarwatsa tsarin mulkin jam’iyyar PDP, shi ya sa suka dage a kan sai an saukar da Ayu daga mukaminsa.
Melaye ya koka kan yadda jam’iyyar PDP ta samu kanta a rikicin cikin gida, amma duk da haka yana da tabbacin cewa Atiku ne zai lashe zaben shugaban kasa na 2023.
Shi dai Ayu ya ki amincewa da bukatar Gwamna Jihar Ribas, Nyesom Wike na ya sauka daga shugabancin jam’iyyar a matsayin sharadi da zai mara wa Atiku baya a zaben 2023.
Ya ce, “Wadanda suka dage sai an cire Ayu daga shugabancin PDP, ‘ya’yan jam’iyyar APC ne da ke kokarin tarwatsa tsarin mulkin PDP domin APC ta amfana.
“Idan muka duba tsarin mulkin jam’iyyarmu, in har aka cire shugaban jam’iyyar, to dole a maye gurbinsa da wani da suke yankin daya. A yau idan har Ayu ya sauka, mataimakinsa daga yankin arewa ne zai gaje shi.
“Kuma suna adawa ne kan dan arewa bai kamata ya zama shugaban jam’iyyar ba, sannan dan takarar shugaban kasa ya kasance dan arewa, amma hakan ya taba faruwa a baya lokacin da dan arewa yake shugabancin jam’iyyar aka zabi Goodluck Jonathan, sa’ilin da aka rantsar da Jonathan sai aka cire shi nan take.
“Mu ba mu ce Ayu ya ci gaba da shugabancin jam’iyyar lokacin da aka zabi Atiku a matsayin shugaban kasa ba. Lokacin da Atiku ya samu nasara a zabe, to dole Ayu ya sauka daga shugabancin jam’iyyar.
“Lokacin da muka zabi Ayu a matsayin shugaban jam’iyyar, kowa ya san daga yankin Arewa ya fito, an dai zabe shi ne bisa cancanta da zai iya magance matsalolin jam’iyyar.
“Bisa haka, nake cewa babu wata matsala. Jam’iyyar PDP ta kasance tana da kyakkyawan tsari da muke tabbatar da cewa kowa ana ba shi hakkinsa,” in ji shi.
Mai magana da yawun kungiyar yakin neman zaben Atiku ya dage da cewa dan karamin rashin jituwa ne aka samu tsakanin bangarori guda biyu na jam’iyyar wanda ake samu a cikin harkokin dimokuradiyya.
A cewarsa, matsala da aka samu da Wike nan da ‘yan kwanaki komai zai daidaita, domin ita PDP jam’iyya ce mai hada kan ‘ya’yanta.