ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Monday, December 22, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

‘Yan Bindiga: Gwamna Dauda Ya Kai Ziyarar Jaje A Zurmi Da Birnin Magaji

by Leadership Hausa
2 years ago
gwamna

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal a Juma’ar nan ya ziyarci al’ummomin Ƙananan Hukumomin Zurmi da Birnin Magaji bisa harin ta’addancin da ‘yan bindiga suka kai, inda Gwamnan ya jaddada aniyarsa ta kawo ƙarshen matsalar tsaron da jihar ke fama da shi.

In dai ba a manta ba, a makon da ya gabata ne ‘yan bindiga suka kai hare-hare a Nassarawar Zurmi da ke Ƙaramar Hukumar Zurmi da Nasarawar Godel da ke Ƙaramar Hukumar Birnin Magaji a cikin jihar ta Zamfara.

A sanarwa da Kakakin Gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya sanya wa hannu a Gusau, ya bayyana cewa ziyarar ta kasance ta jaje ce da ta’aziyya ga al’ummar da wannan bala’i ya shafa na asarar rayuka, tare da nuna cewa gwamnati na tare da su.

ADVERTISEMENT

Ya ce, Gwamnan ya nuna wa jama’ar cewa yana tare da su, ya kuma tabbatar da jajircewar gwamnatinsa wajen lalubo sahihiyar hanyar kawo ƙarshen wannan bala’i da ya addabi jihar.

  • Yadda Mayar Da Gonaki Fulotai Ke Tsananta Karancin Abinci

 

LABARAI MASU NASABA

Ko Kin San… Maganin Sanyi Na Mata (Infection)?

Ko Kin San… Yadda Za Ki Gyara Kanki Da Kanki?

Sanarwar ta Malam Idris ta kuma bayyana cewa, a yayin da Gwamna Dauda ya kai ziyarar gani da ido ga ofishin ‘yan sanda na Zurmi, wanda ‘yan ta’addan suka ƙona, ya nuna masu a shirye yake wajen samar masu da duk kayan aikin da suke nema don wannan namijin aiki.

Gwamna Lawal ya ce, “Ina miƙa saƙon ta’aziyya ta game da jami’ai biyu da suka rasa rayukansu a harin da ‘yan bindiga suka kai wa Nasarawar Zurmi. Ina sane da irin tashin hankalin da ke tattare da irin wannan bala’i ga duk wanda ta rutsa da shi, ina tabbatar maku, tare da iyalan waɗannan gwaraza, cewa ina tare da duk al’ummar wannan yanki a cikin addu’o’i na.

“Na yi matuƙar jinjina ga ƙoƙarin jajirtattun jami’an tsaronmu masu yaƙi da ta’addanci. Jajircewar ku na ganin kun kare al’ummar mu daga ‘yan ta’adda, wannan abin yabawa ne.

“Gwamnati na za ta ci gaba da bayar da duk wani taimako da dakarun muke buƙata. Tare za mu kawo ƙarshen waɗannan matsaloli, kuma mu ƙara ƙarfi.”

A lokacin da Gwamna Lawal ya shiga garin Zurmi, ya kai gaisuwar ban-girma ga Sarkin Zurmi, Alhaji Bello Sulaiman.

Da yake jawabi ga jama’ar Nasarawar Godal da ke Ƙaramar Hukumar Birnin Magaji kuwa, Gwamna Lawal ya tabbatar masu da cewa ya riga ya aiko da kayan tallafi tun lokacin da abin ya faru.

“Na zo yau ne domin in nuna tausayawa ta da ta’aziyya ga iyalan waɗanda wannan abu ya shafa, tare da tabbatar da cewa gwamnati na ba za ta numfasa ba, har sai ta kawo ƙarshen wannan rashin tsaro.

“Ina fata wannan ziyara tawa za ta miƙa wani saƙon kyakkywar fata ga al’ummar Nasarawar, tare da tabbatar masu da cewa muna tare da su a wannan mawiyacin hali.

A lokacin da ya ke dawowa zuwa Gusau, Gwamna Lawal ya yada zango a Kasuwar Daji da ke Ƙaramar Hukumar Ƙauran Namoda don jajanta wa Alhaji Hamisu Kasuwar Daji, wanda waɗannan ‘yan ta’adda suka kai wa gidansa hari.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Ko Kin San… Yadda Za Ki Gyara Kanki Da Kanki?
Adon Gari

Ko Kin San… Maganin Sanyi Na Mata (Infection)?

October 19, 2025
Ko Kin San… Yadda Za Ki Gyara Kanki Da Kanki?
Adon Gari

Ko Kin San… Yadda Za Ki Gyara Kanki Da Kanki?

October 12, 2025
tusar gaba
Adon Gari

Ko Kin San… Dalilin Da Ke Sa Mata Ke Ganin Farin Ruwa Kafin Ko Bayan Al’adarsu?

August 31, 2025
Next Post
Nazari Kan Noman Citta A Zamanance

Nazari Kan Noman Citta A Zamanance

LABARAI MASU NASABA

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja

December 21, 2025
Raphinha Da Yamal Sun Ci Ƙwallaye Yayin Da Barcelona Ta Doke Villarreal

Raphinha Da Yamal Sun Ci Ƙwallaye Yayin Da Barcelona Ta Doke Villarreal

December 21, 2025
Davido Zai Raƙashe A Bikin Buɗe Gasar AFCON 2025 A Morocco

Davido Zai Raƙashe A Bikin Buɗe Gasar AFCON 2025 A Morocco

December 21, 2025
Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

December 21, 2025
An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

December 21, 2025
Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

December 21, 2025
Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

December 21, 2025
Tinubu

Dambarwar Naɗa Muƙamai Da Soke Su A Gwamnatin Tinubu

December 21, 2025
Zaben Fidda Gwani A APC: Sanatocin Jigawa Sun Rasa Tikitin Komawa Majalisa

APC Za Ta Gudanar Da Babban Taronta Na Kasa A Watan Maris

December 21, 2025
Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

December 21, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.