Connect with us

LABARAI

‘Yan Bindiga Sun Harbe Basarake A Jihar Nasarawa

Published

on

A daren jiya Juma’a ne wasu ‘yan bindiga suka kai hari garin Odu inda suka tayar da hankulan mutane suka kuma harbe Dagacin Odu, Mista Amos Ewa Obere (ASP Rtd) har lahira. Odu kauye ne a karkashin garin Udege a karamar hukumar Nasarawa ta jihar Nasarawa.

An garzaya da Dagacin da suka harba zuwa babban asibitin Udege domin bashi taimakon gaggawa, amma sai rai ya yi halinshi a asibitin.

Kafin rasuwarsa, marigayi Obere wanda tsohon jami’in dan sanda ne mai mukamin mataimakin sufeta shine Dagacin garin Odu da kauyukan da ke kewayenshi.

Shaidun gani da ido sun shaidawa majiyarmu cewa ‘yan bindigan suna yawa, sun shiga garin suna harbe harbe wanda hakan ya firgita al’umma, sannan suka tafi suka aikata mummunan abinda ya kawo su, na kisan Dagacin.
Advertisement

labarai