‘Yan bindiga Sun Kai Hari Gidan Yarin Oyo, Sun Saki Fursuna 1,000

Daga Sulaiman Ibrahim,

Rahotanni sun ce kimanin fursunoni dubu sun tsere daga gidan yarin Abolongo da ke cikin garin Oyo bayan da wasu ‘yan bindiga suka kai hari gidan gyaran halin tare da sake dukkan fursunonin.

Wata majiya ta shaida wa LEADERSHIP cewa ‘yan bindigar sun isa gidan fursunonin da yawansu da misalin karfe 10:00 na daren Juma’a suka fara harbi ba kakkautawa, sannan suka saki fursunonin da suka tsere zuwa wurare daban-daban.

Ya kara da cewa, sojoji biyu da Jami’an tsaro na Amotekun guda biyu sun mutu a artabun bindigar da suka yi da maharan, wanda daga baya suka tayar da bam don karya katangar gidan yarin don samun shiga.

Sai dai majiyar ta kara da cewa an tsaurara matakan tsaro a Oyo da kewaye a safiyar ranar Asabar, lamarin da ya kai ga sake cafke wasu daga cikin fursunonin da suka gudu.

Har zuwa lokacin wannan rahoton, rundunar ‘yan sandan jihar Oyo ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance ba don tabbatar da ainihin adadin wadanda suka tsere daga gidan yarin.

Exit mobile version