‘Yan Bindiga Sun Kaiwa Sojojin Nijar Hari

Ma’aikatar Cikin Gidan Jamhuriyar Nijar ta bayyana cewa; wata bataliyar jami‘an tsaron kasar ta yi artabu da ‘yan ta’adda dauke da muggan makamai a kusa da gundumar Dogon Kiriya a ranar Lahadin da ta gabata.

Sanarwar da Ma’aikatar ta fitar ta ce, an fatattaki ‘yan ta’addan bayan zazzafar fafatawar da aka yi da su, sai dai jami’an sojin kasar biyu sun kwanta dama, amma babu alkaluman wadanda suka mutu ko suma jikkata daga bangaren ‘yan ta’addan. A karo na biyu kenan da ake kai farmaki a yankin Dogon Doutchi duk da cewa, an dauki tsawon lokaci ba tare da jin duriyar ‘yan ta’adda a wannan yanki ba.

A cikin watan Fabrairun da ya gabata, an kashe jandarmomi biyu da farar hula guda a harin da ‘yan bindiga suka kai a kauyen Bagaji da ke wannan yanki. Yankin na Dogon Doutchi na kusa da tarayyar Nijeriya, amma dai akwai tazarar daruruwan kilomitoci tsakaninsa da yankin Diffa, in da mayakan Boko Haram suka sha kai hare-hare.

Tuni shugaban kasar ta Nijar, Muhammadou Issoufou ya bukaci taimako daga kasashen yammacin duniya da suka hada da Majalisar Dinkin Duniya domin magance matsalar ta’addanci a kasar.

Exit mobile version